Friday 18 January 2019

KARANTA KAJI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA TAKWAS

Tura Wannan Zuwa
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.



Darasi Na 8

ZAGAGEN AIKATAU

Zagagen aikatau na nufin kalmomin da kan gabaci kalmar da ke nuna aiki a cikin jumla. To dukkan zagagen aikatau na lokaci mai ci (wanda ake cikin yi) na 1 da na 2, da na lokacin da aka saba, ana rubuta su ne a haɗe, ba a raba su.

Lokaci mai ci 1:

ina, muna, kana, kina, kuna, yana, tana suna da ana. Misali:

suna zaune ba su na zaune ba
tana daka ba ta na daka ba

Lokaci mai ci 2:

nake, muke, kake, kike, kuke, yake, take suke da ake. Misali:

darasi muke ba darasi mu ke ba
Ali yana so ba Ali ya na so ba

Lokacin Sabawa

nakan, mukan, kakan, kikan, kukan, yakan, takan sukan da akan. Misali:

mukan ci ƙosai ba mu kan ci ƙosai ba
yakan zo nan ba ya kan zo nan ba.

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad .

KARANTA KAJI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA BAKWAI

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user