Wednesday 12 June 2019

KARANTA YAUSHE AKE YIN AZUMIN WATAN RAMADAN

Tura Wannan Zuwa Ga
Yin Azumin watan Ramadan yana wajaba da ɗayan abubuwa guda biyu:


YAUSHE AKE YIN AZUMIN WATAN RAMADAN1. Ganin watan Ramadan


قَالَ الله تَعَالَى: "فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ." (البقرة: 185)


“Duk wanda ya tabbatar da tsayuwar watan to ya azumce shi.” (Al Bakara: 185).


Idan mutum ya ga watan Ramadan shi kadai, kuma shi mutumin adali ne, wanda aka aminta da adalarsa, to, za a yi aiki da maganarsa ta ganin wata a wajen mafi yawancin ma’abota ilimi.”


عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ الله عَنْهُ قَالَ: تَرَاى النَّاس الْهِلاَل فَرَأَيْتَهُ، فَأَخْبَرْتُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَصَامَ وَأَمَرَ النَّاس بِصِيَامه." (رواه أبو داود).


Don fadin Abdullahi ibn Umar (R.A) ya ce: “Mutane sun ga wata, kuma ni ma na gan shi, don haka, sai na je na ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari, sai (Annabi) ya yi Azumi, kuma ya umarci mutane su ma su azumta.” (Abu Dawud ne ya rawaito).


YAUSHE AKE YIN AZUMIN WATAN RAMADAN2. Cikar Watan Sha’aban Kwana Talatin

Idan sama ta yi duhu gajimare ya rufe ta a ranar ashirin da tara ba a ga wata ba har aka wayi gari ranar talatin ga wata, to, wajibi ne a ranar talatin kowa ya dauki Azumi.


لِحَدِيثِ ابْنِ عُمَر رَضِيَ اللهُ أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "الشَّهْرُ تِسْعَ وَعِشْرُونَ لَيْلَةً، فَلاَ تَصُومُوا حَتَّى تَرَوْهُ، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا الْعِدَّةَ ثَلاَثِينَ." (رواه البخارى).


Saboda hadisin Abdullahi dan Umar (R.A) inda ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce:


“Wata dare ashirin da tara ne (don haka) kar ku yi Azumi har sai kun ga wata, idan kuwa sama ta yi girgije, to, sai ku lissafa kwana talatin.” (Bukhari ne ya rawaito).KARANTA HUKUNCIN KIN YIN AZUMIN RAMADAN
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user