Saturday 10 August 2019

KARANTA WARAKAR ZUKATA CIKIN BAYANIN AZUMIN ARFAH

Tura Wannan Zuwa
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Salati da aminci su tabbata bisa Annabin Rahma, tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan managartan bayi. 

Hawan Arfah


Yau ne da safe (05/12/1440) naga wani rubutu yana ta yawo a Internet, wai wani mutum yace wai yaji wani Malami a Radio yana cewa wai Haramun ne yin azumin Arfar wannan shekarar tunda yazo aranar Asabar, don haka wai bana (wannan shekarar) babu azumin ranar Arfah. Wai har yaje wajen wani limami ya Qara tabbatar masa da hakan.

Daliban zauren fiqhu har sun fara jefo min tambayoyi akan bayanin da rubutun ya kunsa, sai naga cewa zai fi kyau in ajiye uzurina in tsaya in warware mas'alar gwargwadon iko ba tare da tsawaitawa ko zurfafawa ba.

To yayin da na duba sosai sai naga alamar marubucin kodai bai yi bincike ba kafin yayi rubutun, ko kuma bai fahimci nassosin hadisai wadanda sukayi magana akan mas'alolin guda biyu ba.

Abu na farko da zamu yi la'akari dashi shine hadisin falalar Azumin ranar Arfah din wanda Imamu Ahmad da Nisa'iy suka ruwaito kuma suka ingantashi ta hanyar Sayyiduna Abu Qataadah (Allah ya yarda dashi). Yace  Manzon Allah (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :

"AZUMIN RANAR ARFAH YANA KANKARE (ZUNUBIN) SHEKARU BIYU; WACCE TA GABATA DA WACCE ZATA ZO. SHI KUMA AZUMIN ASHURA YANA YANA KANKARE (ZUNUBIN) SHEKARAR DA TA GABATA".

Imam Doktor Muhammad Bakru Isma'eel yace "An so (wato mustahabbi ne) yin azumin ranaku takwas din da suka gabaci ranar Arfah din saboda hadisin Sayyiduna Hunaidah bn Khalid (radhiyallahu anhu) wanda ya karbo daga matarsa, ita kuma daga wata daga cikin matayen Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tace : "Manzon Allah (saww) ya kasance yana azumtar kwanaki tara na Dhul Hijjah, da ranar Ashura, da kuma kwanaki uku a kowanne wata..."

(Imamu Ahmad ne da Abu Dawud suka ruwaitoshi).

Don Qarin haske aduba littafinsa mai suna ALFIQHUL WADHIHU (Juz'i na farko, shafi na 561).

To 'yan uwa kun ga ashe kenan idan har yana azumtar wadannan kwanaki tara din ajere to har asabar din ta shigo ciki. Koda yake dama akwai hadisin da yayi umurnin hada Jumu'ah da asabar din ga masu azumin nafilah.

To idan muka koma kan hadisin da yayi umurni da yin azumin Ashura da Arfah, babu togo acikinsa. Wato ba'a ce idan ranakun sun zo a asabar ko Jumu'ah ko lahadi kada a azumcesu ba. To kunga wannan ma hujjah ce dake warware maganar wancan mutumin.

Kuma awajen Malaman Ilmul Usool, ana fara gabatar da hadisin dake tabbatarwa ne akkan wanda ke korewa. Ita ma wannan Qa'idar tana Qara kore maganar wancan mutumin.

Sai kuma mu koma kan hadisin da shi wancan mai rubutu ya dogara dashi yake neman rikita wasu daga cikin al'ummar musulmai : Zamu kawo nassin hadisin ne kafin mu kawo maganganun da Malamai sukayi akansa kamar haka :

Daga Samma'u 'Yar Busrin (Allah ya yarda da ita da babanta) cewa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "KADA KU AZUMCI RANAR ASABAR SAI DAI CIKIN ABINDA AKA FARLANTA MUKU. KODA ACHE DAYANKU BAI SAMU KOMAI (DA ZAI CI)  BA, SAI 'BAWON INABI KO SANDAN ITACE, TO YA TAUNASHI".

Malaman da suka ruwaitoshi sun ha'da da : Imamu Ahmad, Tirmidhiy, Abu Dawud, Nisa'iy, Hakim, Daramiy, Ibnu Maajah, Baihaqiy da Bagawiy.

Ga kuma abinda Malamai masanan ilimin hadisi suka ce akansa :

Al Hafiz Imam Ahmad bn Hajr Al Asqalaniy yace :

Mazajen hadisin amintattu ne. Sai dai shi hadisin 'Mudh'darib' ne (wato akwai tufka da warwara acikin wani sashen isnadinsa).

Domin ance daga riwayar Abdullahi 'dan Busru ne da ya karbo daga 'Yar uwarsa Samma'u, kuma ance a'a ya karbo ne daga mahaifinsa Busru. Kuma an ce a'a daga 'yar uwarsa Samma'u ya karbo, Ita kuma daga Nana A'ishah (Allah ya yarda dasu).

 "Imamu Malik yayi inkarin hadisin (wato bai yarda da ingancinsa ba).

Kuma Hafiz Ibnu Hajr din ya Qara da cewa "Imam Abu Dawud ma ya ruwaito daga Malik bn Anas (rah) yace "Wannan hadisin Qarya ne".

Kuma shi kansa Imam Abu Dawud din yace "Wannan hadisin an shafeshi. Wato ba'a aiki dashi.

Don Qarin bayani aduba Bulugul Maram na Asqalani din, bugun darul fikri shafi na 121 hadisi na 711.

Muhammad bn Isma'eel As-San'aniy acikin shahararren littafinsa mai suna "SUBULUS SALAM" (Sharhin Bulugul Maram) acikin juzu'i na biyu shafi na 665 bayan ya kawo hadisin, kuma ya kawo dukkan maganganun da malamai sukayi akan hadisin sai yace "Abu Dawud ya karbo daga Imamu Malik cewa wannan hadisin "QARYA NE". amma abinda Abu Dawud din ya fa'da cewa wannan hadisin shafaffe ne, to watakil yana nufin ga hadisin da ya shafe hukuncin wannan din, fa'darsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam)  :

Daga Ummu Salamah (Allah ya yarda da ita) matar Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tace "Ya kasance mafi yawan abinda yake azumta daga ranaiku, ranar asabar ce da ranar lahadi.  Kuma ya kasance yana cewa "SU BIYUN SUN KASANCE RANAKUN EEDI NE GA MUSHRIKAI, KUMA NI  INA SO IN SA'BA MUSU NE".

Isnadin hadisin mai Qarfi ne, Imamu Ahmad ya kawoshi acikin Musnadu juzu'i na 10 shafi na 27,812 . Hakanan Ibnu Hibban ya ruwaitoshi acikin Sahihu nasa, juzu'i na 8 shafi na 3646 da kuma na 3616.

Ibnu Khuzaimah shima ya fitar da hadisin acikon Sahihu nasa akan lambar hadisi na 2167, Tabaraniy  ya ruwaito shima acikin Mu'ujamu juzu'i na 23 shafi na 616. Hakim ya ruwaitoshi acikin Mustadraku Juz'i na 1 shafi na 436.

Ibnu Qayyimil Jauziyyah acikin Zadul Ma'ad juzu'i na biyu shafi na 67 yace an karbo hadisin ne daga Kareeb maulan Abdullahi bn Abbas yace "Ibnu Abbas ya aikeni dashi da wasu mutane daga Sahabban Annabi (saww)  cewa in tambayi Ummu Salamah (ra) cewa SHIN WADANNE KWANAKI NE ANNABI (SAWW) YAFI AZUMTARSU?. SAI TACE ASABAR DA LAHADI.

Ibnu Qayyimil Jauziyyah yace akwai abin dubawa  ikin ingancin wannan hadisin. Yana nufin cewa akwai mutum guda wanda ba'a san ingancinsa ba, acikin mazajen hadisin. To amma Shaikh Arfan Abdulqadir acikin tahqiqin da yayi wa Zadul Ma'ad din yace Imamuz Zahabiy duk ya inganta Mazajen da Ibnul Qayyim din yake tantama akansu din, acikin littafinsa AL KASSHAF. Sauran mazajen isnadin kuma duk amintattu ne bisa sharadin Imamul Bukhariy.

Ibnu Qayyimil Jauziyyah yace "Mutane (wato Malamai) sunyi sa'bani game da wadannan hadisan biyu. Imamu Malik yace "Qarya ne". (yana nufin hadisin da ya aka hana azumtar asabar din) Tirmidhiy yace "Hadisi ne mai kyawu". Amma Abu Dawud yace an shafe hadisin ma. Nisa'iy yace "Hadisi ne Mudh'darib" (wato akwai rashin tabbas acikin isnadinsa).

Da yawa daga cikin malamai kuma sun ce babu sa'bani atsakanin hadisan biyu, domin acikin wancan hadisin ana nufin kada mutum ya kebanci asabar din ka'dai ako yaushe domin yin azumi. Kuma hadisin da ta nuna yawaita azumtarsa da Annabi (saww) ke yi, ana nufin tare da ranar lahadi ne.

Don haka a takaice dai duk azumin nafilah na musamman kamar Ashurah ko Tasu'ah ko na Arfah, ko na kwana uku din nan da akeyi a kowanne wata, ko azumin ramuko zaka iya yinsa koda yazo aranar asabar din ba'a  hana ba. Ba'a haramta ba. Abinda aka karhanta shine kebantar asabar din ka'dai da wasu ibadu (shima ba haramci bane. Karhanci ne kamar yadda yazo a litattafan Fiqhu).

Muhammad bn Isma'il As-San'aniy yace "Wancan hanin azumtar asabar din, Annabi (saww) ya yishi ne a farkon musulunci lokacin da Annabi (saww) yake son yin muwafaqah (wato daidaito) da Ahlul Kitabi. Sannan daga karshe umurninsa ya zamanto sa'ba musu ne kamar yadda hadisi na biyu ya bayyana Qarara.

Wasu Malaman kuma suka ce "Hanin ya shafi kebance asabar din ne kadai da ibadah sai dai idan an ha'da da wasu ranakun kafin ta, ko bayanta.

Imamut Tirmidhiy ya fitar da wani hadisi daga Nana A'ishah (ra) tana cewa "Manzon Allah (saww) ya kasance acikkn wata yakan azumci asabar, lahadi da litinin. Acikin wani watan kuma sai ya azumci Talata, Laraba, da Alhamis. Kuma hadisin da ake magana akansa dai yana nuni ne bisa mustahabbancin azumtar ranakun asabar da lahadi domin sa'ba wa Yahudawa da Nasara, kuma zahirinsa yana nuna halascin azumtar kowanne (asabar da lahadi din) ararrabe, ko a dunkule.

Anan ne muke Qara jan hankalin jama'a cewa kuyi azuminku ranar Arfah domin babu nassin da yace "HARAMUN NE". Kuma koda hadisin da yazo akan maganarsa, bai inganta ba awajen Malaman hadisi. Kuma koda awajen malaman da suka bashi matsayin "Hasanun" din, sun ce hukuncin kebantar asabar da azumi, Karhanci ne ba haramci ba.

Kuma hadisin da yazo da maganar halascin ya fishi inganci. Kuma lallai kada ku bar wannan garabasar ta wuceku. Gafarar zunuban shekaru biyu fa!!. Shin ka san zaka kai ba'di ne? Watakil wannan ce arfarka ta karshe aduniya. Don haka kada ka biye wa masu kawo ru'du acikin addini.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA HUDUBA MAI RATSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI TA ANNABI MUHAMMAD (SAW)

KARANTA FALALAR KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZULHAJJI

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN IMAM MALIK BN ANAS

An gabatar da wannan karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1) aranar 06/08/2019 daidai da 05/12/1440.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
Source: ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1)
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user