Friday 23 August 2019

KARANTA KADAN DAGA CIKIN FALALAR RANAR JUMA'A

Tura Wannan Zuwa Ga
Juma‘a ita ce mafi girma a cikin ranaku da ALLAH Madaukakin Sarki ya halitta, ta yadda ya bawa yahudawa zabi sai suka zabi asabar, sa‘annan Ya bawa nasara zabi sai suka zabi lahadi, mu kuma al‘ummar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam sai ALLAH ya azurta mu da wannan rana ta juma‘a.

Falalar Ranar Juma'a


A cikin tane ALLAH Madaukakin Sarki ya halicci babanmu Annabi ADAM (AS) kuma a cikin wannan
rana aka sauko da shi daga AL-JANNAH, kuma a cikin irin wannan rana ALLAH Madaukakin Sarki zai
tashi alƙiyama.

Hadisi ya tabbata a cikin muslim cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace idan ranar juma‘a ta zo duk halittun ALLAH
Madaukakin Sarki hankalinsu a tashe yake (sabo da tsoran kada ALLAH ya tashi ƙiyama a wannan
ranar).

Sai mutum da al-janni
kawai hankalin su yake a kwance.

Haka kuma yana daga falalar ta juma‘a Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi Wasallam yace akwai wata sa‘a wanda duk ya risketa yana
mai addu‘a to ALLAH zai karbi addu‘arsa.

Muslim ne yarawaito.

Falalar Ranar Juma'a


Ana son kamewa da yawaita zikiri da salatin Annabi da iyalan gidansa (a.s).

Ana son yawaita karatun al-qur'ani da
addu'o'i ko sauraransu ta hanyar
radio.

Yana daga cikin sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana
karanta suratul KAHFI kowacce juma‘a.

Da dai sauran falalar ta masu dinbin yawa.

Ya dan uwa ka kasance mai koyi
ga abubuwan shugabanmu
Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.

Ya ku musulmi! mu yi gasa a kan wannan alheri mai girma, wanda Allah ya sanya shi cikin ranar Juma’a ga wanda ya sunnanta da sunnan Annabi a cikin wannan,
mu tsaftacce jukkunan mu, mu
sanya mafi kyawun tufafin mu, mu yi asuwaki, mu sanya turare, mu yi sammako don mu tafi sallar Juma’a, mu lazimci ladubban
Annabi (S.A.W), da tsari na Muhammadiyya.

DUBA WADANNAN:

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

KARANTA YADDA AKE YIN SALLAH

KARANTA MANYAN SUNNONIN SALLAH GUDA GOMA SHA HUDU 14

Mu kasance daga masu rigaye zuwa alherai, masu rabauta da mafiya daukakar darajoji, (Wannan falala ce ta Allah da yake ba da ita ga wanda yaso, kuma Allah shi ne ma’abocin falala
mai girma).

Allah  yasa mu da ce Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user