Saturday 24 August 2019

KARANTA ILLOLIN YIN SHAFE-SHAFEN BLEACHING GA LAFIYAR JIKIN MU

Tura Wannan Zuwa
Shafe-shafe yana da illoli masu tarin yawa musamman ga ’ya mace.

Kafin fara yin Bleaching da kuma bayan anyi


1. Na farko yana canjawa mace launin fatarta.

Fatar da ba a yiwa shafe-shafe, ita take bada kariya daga cututtuka da sauran kwayoyin da suke yiwa fata barazana.

Fata ta asali tana ba mace garkuwa daga zafin rana.

Bayan mace tayi bilicin zata kasance cikin yawan laulayi, bazata iya yawo a rana ba domin zataji kamar ana kwara mata ruwan zafi, saboda tarasa fatarta ta asali datake bata garkuwa daga zafin rana.

2. Abu na biyu shi ne, mai bilicin bazata sami kariya daga cutar daji ba wato (Cancer), wadda cuta ce mai ban tsoro da wuyar sha’ani, ba kasafai aka fiya samun maganinta ba.

Cuta ce wadda take kama sassan jikin mutum, yawanci akan yanke gabobi ko wuraren data kama.

Duk wannan yasamo asali ne a sakamakon bilicin.

3. Mai bilicin za ta rasa kuzari, Idan kafin ta fara bilicin tana iya yin aiki na tsawon sa’a uku bata gaji ba, to yanzu ba lallai bane ta iya na sa’o’i biyu, hakan ya haifar mata da nakasu, maimakon a nemo kiba sai aka iske rama.

4. Ba a nan kadai illar shafe-shafe ta tsaya ba, akwai illoli masu tarin yawa da kuma tsoratarwa.

Misali bilicin na jawo gyambon ciki abin da aka fi sani da olsa (ulcer) wanda mafi yawanci akan dauketa a matsayin rashin cin abinci ke kawota.

Daga ciki akwai kassara dukkan wasu sassan jikinki masu amfani walau wadanda ake gani a zahirance da kuma wadanda ba mu iya gani, kamar irinsu:

1. Hanta.

2. Qoda.

3. Hunhu da sauransu.

DUBA WADANNAN:

KARANTA YADDA AKE DAUKAR RAYUKAN SALIHAN BAYIN ALLAH (MUMINAI)

KARANTA MAGANIN BASIR KO WANE IRINE DA YARDAR ALLAH

KARANTA FALALAR WANKAN GAWA DA YADDA AKE YINSA

Wadannan duk suna tagayyara ne sakamakon illar bilicin.

Da fatan za'a kiyaye.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: TAFARKIN TSIRA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user