Wednesday 18 September 2019

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI MUTUM DA YAYI ZINA A JAMI'A AKWAI DARASI MAI AMFANI A CIKIN LABARIN

Tura Wannan Zuwa
'Yan uwa na Maza da Mata akwai wata ƙissa da zan bamu, mai matuƙar amfani acikin wannan zamanin namu, ma'abocin ƙissar, wanda abin yafaru dashi, shine yake bayar da Labarin yadda al'amarin ya kansace dashi.


Labarin Wani Mutum da Yayi Zina

Labarin yana cikin wata Mujallah (Magazine News paper) ta ƙasashen Larabawa, kuma cikin harshen Larabcine, amma zanyi ƙoƙari wajen fassarawa gwargwadon yadda na fahimta, saboda nima din ba gwani bane a harshen Larabci.

Gata kamar haka:

Mutumin yana cewa:

A lokacin da ina saurayina nasami Admission a Jami'a, bayan nafara karatunne sai na haɗu da wata Budurwa (Girl-friend) acikin Jami'ar tamu muka ƙulla soyayya da ita tamkar ma'aurata, hardai tasami juna biyu, (yai mata ciki kenan).

Da iyayenta suka gane sai suka tambayeta wanda yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.

Sai yayanta ya taho nema na a fusace yana nufin ɗaukar mataki a kaina, yana zuwa saiya tambayeni kaine kayima ƙanwata ciki ko ???

Sai na amsa masa da cewa:

Wace ce, ni banma taɓa ganinta ba a Rayuwata, ban santa ba.

Sakamakon rashin hujjar da zasu kamani da ita dole suka ƙyaleni.

Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida saina tarar da Mahaifiyata a dur ƙushe  tana kuka.

Saina dur ƙusa na ɗaga ta sai tasake yanke jiki tafaɗi ƙasa har sau uku.

Sai na tambayeta a karo na ƙarshe.

"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru mama)?

Sai tace:

Kanwarkace gata can wani yayi mata ciki!

Yace sai naji kamar an sokeni da mashi, hankalina yatashi na tasa ƙeyarta muka tafi wurin wanda tace yai mata cikin.

Da mukaje sai yafaɗa min maganar data tayarmin da hankali.

Bawata magana bace face wadda na fadama yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.

(Ban santa ba, ban ma taɓa ganinta ba)!

Bayan zamani yaƙara yin nisa sai nayi nufin yin aure nafara neman aure nasamu matar da nake so kuma akasa lokaci akayi biki, ranar farko dana tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa ba.

Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina yatashi.

Sai ta faɗamin wata magana mai shiga rai.

"Don Allah karufa min asiri, ka suturta al'amarina kaima Allah sai ya suturta al'amarinka."

Yace sai nace a cikin zuciyata:

Ya Rabby yakfy, yakfy.

(Ma'ana Ya Mahalliccina ya isa haka ya isa haka).
.
Ya cigaba da cewa:

Bayan mun kwashe shekaru da mata ta sai muka haifi 'ya mace kyakkyawa gata da haske kamar wata.

A lokacin da tacika shekaru 6 a duniya sai gata wata rana tashigo gida tana kuka.

Me yafaru ?

Ai me gadi ne yayi mata fyaɗe!

MAKALOLI MASU ALAKA:

TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BA

KARANTA LABARI MAI SOSA ZUCIYAR DUK WANI MAI IMANI

KARANTA KAYATACCEN LABARIN WANI AKU DA MATAR UBANGIDANSA

KARANTA YADDA RAYUWAR AURE TA LALACE A WANNAN ZAMANIN DA MUKE CIKI

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Aljazaa'u min jinsil amal!

Wallahi duk tsiyar da kake sheƙewa idan Allah ta'ala yaga dama sai ya haɗa maka zafi kan zafi irin wannan!

Yanzu kunga shi ya lalata 'yar mutane guda daya tak shi kuma an lalata masa guda uku!

Yaa Allah ka ƙara karemu daga zina, masuyi kuma Allah ka shirya su Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








Source: TAFARKIN TSIRA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user