Tuesday 29 October 2019

BINCIKE: Nijeriya Tana Fuskantar Makircin Manyan Kasashen Duniya

Tura Wannan Zuwa
Bayan dogon sharhi akan al'amuran dake faruwa na ta'addanci a wasu yankunan Nijeriya, na nazarci wasu makircin da manyan kasashen duniya suke kokarin shiryawa kasar, bisa kallon yadda Gwamnatin jam'iyyar APC karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta dauki hanyar yin wasu mahimman aiyukan da manyan kasashen duniya ba sa so, nazari na ya nuna min cewar matuqar Gwamnati Najeriya bata maida hankali ba, zata cigaba da fuskantar makilci kala daban-daban daga manyan kasashen duniya.

Nijeriya Tana Fuskantar Makircin Manyan Kasashen Duniya

Najeriya kasa ce da Allah ya Azirta ta da ma'adanai da albarkatun kasa nau'in kala daban-daban, Allah ya fifita darajar kasar sama da kowace kasa a Nahiyar Afrika, kusan kowace babbar kasa a duniya tana da alaqar kasuwanci da Najeriya, kuma kowace kasa tana amfanuwa da Kasuwanci da take a Najeriya, amma abin takaici Najeriya bata amfanuwa ko ribantuwa da kasashen da suke kasuwanci dasu ta kowace fuska.

Kafin zuwan mulkin demokadiyya a Najeriya karo na biyu a shekarar 1999, Shugaban Mulkin Soja a lokacin Gen. Sani Abacha, bai sake fuska a manyan kasashen duniya ba, yaki amincewa su kulla huddar Kasuwanci da manyan kasashen duniya saboda tsoran sharrin su, bayan zuwan demokadiyya Najeriya ne, jam'iyyar PDP ta samu goyon bayan wasu manyan kashen duniya bisa yarjejeniyar kulla alaqar kasuwanci idan sun kafa gwamnati, akan  yarjejeniyar ne jam'iyyar PDP ta kafa gwamnati karkashin Shugaba Olusegun Obasanjo, a tsawon mulkin jam'iyyar PDP na shekaru 16, jam'iyyar tayi amfani da karfin mulki ta wajen gurgunta Najeriya, ta hanya Saida wasu mahimman ma'adanai, Kadarori da Masana'antun gwamnatin Najeriya a wasu kasashe da manyan yan kasuwa dake ciki da wajen kasar.

Duk wani Dan Najeriya Shaida ne akan abin da jam'iyyar PDP tayi na gurgunta Najeriya karkashin hadin guiwar ta da Manyan Kasashen duniya, musamman ma yadda jam'iyyar PDP ta mallakar da dukiyoyin kasar a wasu manyan yan Siyasa da yan Kasuwa, da yadda jam'iyyar ta bada kafar satar dukiyar kasar a wasu manyan kasashe Duniya, amma cikin hikima irin na ALLAH, ya nufa jam'iyyar PDP tayi 6atan lissafi a zaben shekarar 2015, a lokacin ne Talakawan Najeriya suka gano munanan Manufofin jam'iyyar PDP na Gurgurta Najeriya, hakan ne yasa jam'iyyun adawar kasar sukayi hadakar jam'iyyun Siyasa, aka kafa APC-Maja domin tunkarar PDP a zaben 2015, APC tayi nasarar lashe zaben Shugaban kasa da yan majilisu dattawa da Wakilai da gwamnoni mafiya rinjaye akan jam'iyyar PDP mai mulki a lokacin.

Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa mulki a shekarar 2015, shugaban ya maida hankalin sa wajen kallon Najeriya ta dogara da kanta musamman ma a bangaren Tattalin arziki, ya kuma inganta Harkar Noma, ya kuma maida hankali bangaren samar da makamashin wutar lantarki, sa'anan ya farfardo da wasu Masana'antun gwamnati, da yunkurin dawo da wasu kaddarorin gwamnati da jam'iyyar PDP ta mallakar a wasu kasashe da wasu manyan yan siyasa da yan kasuwa na ciki da wajen kasar.

Jam'iyyar PDP bisa goyon bayan wasu manyan kasashen duniya da manyan attajirai dake ciki da wajen kasar sunyi yunkurin Shirya makilci kala daban-daban ta yadda zasuyi karfa a tsakanin Talakawa da Buhari, na farko an zarge su da shirya Makilcin kashe Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta hanyar saka masa Guba, shugaban yayi Doguwar jinya amma bai mutu ba, hakan ne yasa suka chanza salon Siye yan majalisar Tarayya domin su masa tarnaqin da dazai hana shi gudanar da duk wasu mahimman aiyukan.

A shekarar farko na hawan Buhari mulki, an zarge su da kafa wasu Kungiyoyin ta'addanci a kudancin kasar, a yankin Niger Dalta, inda sukayi amfani da wasu yan ta'adda masu fasa Bututun Mai da ruguza Wasu manyan Kadarorin gwamnati dake yankin da manufar nakasa tattalin arzikin Kasar, saide Gwamnati Shugaba Muhammadu Buhari ta farka da wuri, inda ta dauki matakin tura sojojin da suka fatattaki yan ta'addan domin a zauna lafiya a yankin.

An kuma zarge su da farfado da Kungiyar ta'addanci nan ta Biafra a kudancin kasar, anan ma Gwamnati ta maida hankali wajen murkushe Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, sunfi bada karfi wajen kawo Ta'addancin da za'a zubar da jinin Talakawa, burin su suyi karfa tsakanin Talakawa da Buhari, ta yadda a zaben 2019 baza'a zabe shiba, amma Gwamnatin Buhari tayi aiki tuquru wajen murkushe ta'addanci daga kowace sashi na kasar, har yakai gwamnatin jam'iyyar APC tayi nasara a zaben 2019.

Manyan kasashen duniya, da manyan-manyan yan siyasa da yan kasuwa dake ciki da wajen Najeriya musamman ma wanda suka mallakar da dukiyoyin Najeriya akansu, basu so ba jam'iyyar APC tayi nasara a zaben 2019, nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu ya fusata manyan kasashen duniya da ake zargin zasu fara farfado da wasu Kungiyoyin ta'addanci da zasu sake kiwotan hankalin Talakawan Najeriya yadda zasu tsani jam'iyyar APC a zaben 2023, dan a zabi jam'iyyar PDP da zata iya dawo musu da damar da suke da ita na mallakar da ma'adanai, masana'antu da kaddarorin Gwamnatin Najeriya.

Jam'iyyar PDP ta zama tamkar karar farautar wasu manyan kasashen duniya ne, suna amfani da jam'iyyar wajen Satar dukiyar al'ummar kasar, idan kuka lura duk Matsalolin da yake faruwa na tabarbarewar tsaro, musamman ma a jihar Zamfara, Matsalar Garkuwa da Mutane da yawaitar Makamai a wasu sassa an fara zargin wasu manyan kasashe da shirya wannan makilcin ta yadda zasu kiwoci hankalin Talakawan kasar su tsani gwamnati jam'iyyar APC karkashin shugaba Muhammadu Buhari.

Aiyukan da shugaba Muhammadu Buhari yake a Najeriya, amma manyan kasashen duniya basa so Najeriya ta mallake su akwai:

1. Basa Son Makamashin Wutar Lantarki ya zauna a Najeriya

2. Basa Son Najeriya ta iya Noma abincin da take ci a Shekara.

3. Basa So Najeriya ta Mallaki Matatan Man Fetir a cikin gida.

4. Basa Son Najeriya ta Farfado da Masana'antun Gwamnati da PDP Suka Lalata.

5. Basa Son Najeriya ta dawo da Kaddarorin ta da wasu Azzalumai suka mallakar akan su.

6. Basa Son Najeriya ta Kwaco Rijiyoyin Man dake hannun Wasu yan Kasuwa dake ciki da wajen kasar.

7. Basa Son Najeriya ta farfafo da Kamfanin Kirkire-kirkire na Ajakuta.

8. Basa Son Najeriya ta Bunkasa Bangaren Sufuri ta hanyar farfado da Kamfanin Jirgin Sama na (Nigeria Airways) Janyo ruwa daga yammaci zuwa Arewacin kasar, da Shimfida Hanyoyi jirgin Kasa a kowace sashin kasar.

Harsashen manyan kasashen duniya, ya tabbatar musu da cewa Idan Najeriya ta mallaki wa'yannan abubuwan dana lissafo, kasar zata iya dogaro da kanta, kasar zatayi karfin tattalin arziki a duniya ta yadda bazata nemi agaji daga kowace kasa ba a fadin duniya, kuma Najeriya zata iya sarrafa komai a cikin gida, zata iya iya hada duk wani kayan kimiyya da fasaha na zamani a cikin gida Najeriya.

Gwamnatin jam'iyyar APC karkashin shugaba Muhammadu Buhari, tana iyaka bakin kokarin ta wajen kallon Najeriya ta mallaki abubuwan dana lissafo, Yanzu haka Buhari yayi nisa a bangaren samar da makamashin wutar lantarki a Najeriya, yanzu haka Najeriya ta samu karfin wutar lantarki da yakai MW10000, a mulkin PDP na shekara 16 ta samo Karfin lantarki a 2000MW ta barshi a 3000MW duk da cewa ta kashe bilyoyin Daloli, Amma a  shekara 4 APC ta kara 7000MW a dan karamin kudin data kashe.

Ribar Wutar Lantarki, Idan makamashin Wutar Lantarki ya zauna a Najeriya, kasar zata ribanta da abubuwa 3 zuwa 4, na farko Kamfanunuwan gwamnati zasu fara aiki, manyan yan kasuwa daga ciki da wajen kasar zazu Shigo su kafa manyan masana'antu, na Biyu zai bunkasa tattalin arziki domin masana'antu zasuna Biyan Haraji Mai tsoka ta yadda Najeriya zatake samu kudin shiga a asusun gwamnati, Kamfanoni da Masana'antu zasu dauki matasa aiki, zai kawo karshen zaman kashe wando a milyoyin Matasa, kuma zai samar da tsaro a kasar kasancewar idan matasa suna da aikin yi za'ayi karancin yan ta'adda.

Wannan daya daga cikin ribar abu daya da Shugaba Muhammadu Buhari yake kokarin Najeriya ta mallaka kenan, wannan kyawawan Manufofi ta jam'iyyar APC karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta tada hankalin manyan kasashen duniya, kuma ya zama tamkar barazanace ga ribar da suke samu a Najeriya karkashin alaqar kasuwanci dake tsakanin su da kasar.

Tinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauko wannan kyakkyawan hanyar, abu daya zaiyi domin tsira daga makilcin manyan kasashen duniya, ya zama Shugaba Buhari ya kara bunkasa harkar tsaro ta yadda za'a yaki ta'addanci a dukkan sassan kasar musamman ma bangaren jihar Zamfara, shugaban ya sake tsawatawa Hukumar Fasakauri na (Custom) saboda makamai suna shigowa daga 6arauniyar Hanyoyi, domin daga cikin makilcin manyan kasashen duniya ana zargin cewar sun shirya shigo da makamai cikin Najeriya da daukar nauyin farfado da wasu kananan ta'addanci ta yadda ta'addanci zai girma ya iya Sanadiyyar zub da jinin al'ummah, a tunanin su hakan zai fusata Talakawan kasar, ta yadda a zaben 2023 Talakawan Najeriya zasu kauracewa zaben jam'iyyar APC, saide su zabi jam'iyyar PDP wadda manyan kasashen duniya suke amfani da ita wajen sace dukiyoyin al'ummar kasar.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Illolin da Kabilar IGBO ta yiwa Sauran Kabilun Nigeria Wanda Hakan Zai Iya Haifar da Matsala anan Gaba

KARANTA TARIHIN YADDA TURAWA SUKA AZABTAR DA AL'UMMAR YANKIN AREWACIN NIGERIA

Karanta Jerin Abinci Hausawa Kafin Zuwan Shinkafa 'Yar Kasashen Waje

Daga Karshe dai, na gano jam'iyyar PDP bata yan Najeriya bace, jam'iyyar wasu manyan kasashe ne da suke amfani da ita wajen satar dukiyar al'ummar kasar nan, Allah ya watsar da mummunar aniyar su akan Talakawan Najeriya. Ameen Ya Allah

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user