Tuesday 29 October 2019

Babban Dalilin da Yasa Kullum Kannywood Take Ci baya akan Sauran Takwarorin ta - Yakubu Mohammed

Tura Wannan Zuwa Ga
Shahararren mawaki kuma dan fina-finan Hausa, Yakubu Mohammed ya saki sabuwar wakar turanci mai suna Superstar wadda ya yi ta da salon Hip-hop.
Jarumi Yakubu Mohammed
Mawakin ya bayyana wa BBC cewa ba wannan ne karon farko da ya saki wakar Turancin Ingilishi mai irin wannan salon ba, dama can ya yi wasu da harshen Turanci.
Wakar Superstar waka ce mai kalaman karfafa gwiwa, sabanin yadda aka san wakoki masu salon hip-hop da zantukan soyayya.
"Waka ce da take magana a kan kara kwarin gwiwa, idan mutum yana so ya yi abu lallai zai iya yi," in ji Yakubu.
Ya ce lokaci ya yi da mawakan Hausa za su fara waka da harshen da ya fi bazuwa da karbuwa a duniya.
Yakubu ya ce "Ya kamata wakokinmu da fasaharmu ba wai su tsaya kawai a kasar Hausa ba, ya zamanto cewa za ka iya yin na Hausa za ka iya yin na turanci."
Ya ce ya fara wakokin Hausa ne saboda ya lura cewa an bar mawakan Hausa a baya, sabanin takwarorinsu na kudu.
"Yawanci idan abubuwa suka faru a arewa, duniya ba ta sani, ba ta jin mu saboda da hausa muke fitowa mu fada, amma abu daya idan ya faru a kudu sai ka ji duniya ta dauka ana cewa a zo a taimaka," a cewarsa.

Jarumi, Ali Nuhu, Sani Danja da Yakubu Mohammed a wajen shirin Kawayen Amarya
Yakubu ya nun takaicinsa kan yadda mawakan kudancin Najeriya ke samun damarmaki fiye da mawakan Hausa na zamani.
"Mawakanmu na Hausa babu wanda za ki ji an gayyace shi ko America ko wata kasar. Akwai wani bikin mawaka da ake yi duk shekara a Dubai, babu mutumin arewa kwaya daya da aka dauka. Amma 'yan kudu da suke dan sirka yarabancin da turanci ana kiransu."



Yakubu Mohammed da wata 'yar wasa a lokacin daukar fim din MaimunaHakkin mallakar hotoYAKUBU MOHAMMED
Image captionYakubu Mohammed da wata 'yar wasa a lokacin daukar fim din Maimuna

'An baro Kannywood a baya'
Yakubu Mohammed ya dade a harkar fina-finan Hausa inda ya ke shirya fina-finai da bayar da umarni musamman ma a kamfaninsu na 2 effects Empire wanda suka kafa shi da dan wasa kuma babban abokinsa Sani Danja.
Sannan Yakubu ya kware wajen rawa da waka, asali ma a fagen waka ya fi yin suna a Kannywood.
A zamanin da, ya yi wakoki da dama da suka samu karbuwa wajen ma'abota wasannin Hausa irin su 'Jarumai' da 'Zubar gado' da 'Gara' da 'Muna tafa-tafa' da 'Jarida' da dai sauransu.
Da wuya ka wuce yara kanana ko matasa ba ka ji suna rera daya daga cikin wadannan wakokin ba.
Daga baya, Yakubu ya fara fitowa a fina-finan Hausa kuma nan da nan ya samu karbuwa har masu shirya fina-finan kuduancin Najeriya ma suka fara sa shi a fina-finansu.



Yakubu da Sani Danja abokan juna ne tun suna matasaHakkin mallakar hotoYAKUBU MOHAMMED
Image captionYakubu da Sani Danja abokan juna ne tun suna matasa

Sai dai Yakubu ya ce a matsayinsa na wanda ya dade a masana'antar, ya fahimci cewa an baro ta a baya ta fannin ci gaba.
"An riga an wuce wani waje bamu farga ba har akai mana nisa," a cewar Yakubu Mohammed.
"Duk duniya yanzu an daina buga fina-finai a faifan CD, sai dai a kalla ta intanet wato ta manhajar Youtube ko ta wasu mahajojin.
"Amma Kannywood ba ta gane haka da wuri ba. Yanzu haka akwai fina-finai sama da dari biyar da aka yi amma an kasa fitar da su saboda asara za a yi," in ji Yakubu.
"Kasuwanci dai dama shi ne jigo a kowace sana'a, duk yadda ka so abu ba za ka so yau ka yi gobe ma ka yi amma ka yi asara ba."
Ya ce amma an fara gano mafita musamman saboda kirkirar manhajar Northflix wacce ke bai wa masu sha'awar kallon fina-finai kallo ta intanet.
''Yan wasan Kannywood ba sa iya boye sirrinsu'



Yakubu Mohammed a fim din 4th RepublicHakkin mallakar hotoYAKUBU MOHAMMED
Image captionYakubu Mohammed yana fitowa a fina-finan turanci da na Hausa

Yakubu Mohammed ya ce yana takaicin yadda 'yan uwansa 'yan wasan Hausa ke bankada sirrikansu a shafukan sada zumunta.
Ya ce "ba komai ba ne za ka fito shafukan sada zumunta kana bayyanawa. Mu tuna muna da mabiya, muna da masoya muna da iyaye amma sai mu fito muna bayyana abubuwan da ba su dace ba."
Ya ce irin wadannan abubuwa na bata masana'antar.
"Dama dai rayuwar duniya zo mu zauna ne zo mu saba, sai ana hakuri. Idan wani abokin aikinka ya yi maka ba dai-dai ba ka kira shi a waya ku daidaita amma fitowa shafukan sada zumunta bai dace ba.
"Irin wadannan abubuwan na kara bata mana masana'antarmu," in ji Yakubu Mohammed.
An samu karuwar 'yan wasan da ke cacar baki a shafukan sada zumunta musamman ma Instagram.
Ko a makon da ya wuce, dan wasa Isa A Isa sun samu rashin fahimta tsakaninsa da Sadiya Haruna inda har ya kai ga 'yan sanda sun kama ta.

MAKALOLI MASU ALAKA:

SHIN SHIGOWAR JARUMA MARYAM YAHAYA KANNYWOOD CE SILAR KWARAROWAR KANANAN JARUMAI A KANNYWOOD?

Karanta Tarihin Kafuwar Masana'antar Kannywood

Jaruma Fati Washa ta Tayar da Kura a Shafukan Sada Zumunta Bayan Fitar Wasu Zafafan Hotunan Ta
Kuma a kwanaki ma manyan 'yan wasa Adam A Zango da Ali Nuhu sun samu rashin jituwa inda har Zango ya zagi Ali Nuhu a shafinsa na Instagram.
Hakan ya bai wa mutane da dama mamaki ganin cewa taurarin biyu manyan abokan juna ne.
Fada ya yi kamari inda har Ali Nuhu ya maka Adam zango a kotu kafin daga baya suka shirya a tsakaninsu kuma Ali Nuhu ya janye karar.
Yakubu ya ce duk da cewa kowa da irin tarbiyyarsa amma "duk abin da mutum ya ke yi marar kyau ya boye."
Ya ce yana fatan ganin an sauya wannan hali a Kannywood.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



Source: BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user