Saturday 2 November 2019

Karanta Amfanin Sada Zumunta Guda 20

Tura Wannan Zuwa Ga
1-Allah ta'ala yayi Umarni da sada zumunta. Suratul bakara 36, Suratul Isra'i 26, Suratul Rum 38,   Suratul bakara 210,  Suratul Nisa'i 2 .

Amfanin Sada Zumunta

Marubuci: Ahmad Musa

2- Sada zumunta yana kara tsawon rai, Bukari 5986,  Muslum 2557.

3- Sada zumunta yana kara arziki,  Bukari 5986

4- Sada zumunta yana cikin abubuwan da akayi Umarni dashi, tun farkon musulunci, bayan tauhidi, Bukari 7

5- Sada zumunta dalili ne na shiga Aljannah,  Bukari 5983

6- Sada zumunta yana cikin abubuwan da Allah yake so. Sahihut-targib 2/667.

7- Sada zumunta yana tseratarwa daga azaba, Abu Dauda 4902

8- Sada zumunta wasiyyar da Annabi (SAW)  yayi wa Al'ummarsa. Sahihut-targib 2/669

9- Sada zumunta siffar muminai ce.

10  Sada zumunta yana sawa a karbi aikin mutum. Sahihut-targib 2/674

11- Sada zumunta yana cikin siffofin masu hankali.

12- Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira, ya dinka sada zumunta,. Bukari da Muslum.

13- Sada zumunta yana kare mutum daga la'antar Allah. Tafsir Ibn kasir Suratul Ra'adi,25.

14- Yin Sadaka ga yan uwan zumunta, yana jawo lada biyu, na Sadaka dana zumunta. Sahihu, Sunanil Tirmiziy. 1/202 .

15,  Sada zumunta yana kara soyayya tsananin dangi da yan'uwa .

16- Sada zumunta yana kara hadin kai tsananin yan'uwa.

17- Wanda baya sada zumunta bazai shiga Aljannah ba.

18- Allah taala ya yiwa mahaifa alkawari zai sadar da wanda ya sadar da ita, zai yankewa wanda ya yanketa.

19- Mai sada zumunta shine wanda ko ba'a zo masa ba, shi zai je.

20,  Baya cikin sada zumunta sai wanda yazo maka kawai zaka je masa.


MAKALOLI MASU ALAKA:

ME KUKA SANI GAME DA LITTAFIN KU AL-QUR'ANI MAI GIRMA?

Shin dagaske Ne duk 'Yam Matan Jami'a Lalatattu Ne?

SHIN KO KASAN ZA KA IYA SABAWA ALLAH AMMA DA SHARUDA GUDA BIYAR?

Allah Ya bamu ikon sauke wannan nauyi na sadar da Zumunta Amin!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user