Saturday 7 December 2019

KARANTA DALILAN KARIN AUREN MACE SAMA DA DAYA

Tura Wannan Zuwa
Addinin Musulunci addini ne mai adalci kuma yazo da dukkan maslaha da hukunce-hukuncen abunda ya shafi addini da rayuwa kuma bai kasance addinin da ake gabatar dashi daka ba face ya kasance addini ne wanda ALLAH (SWT) ya saukar zuwa ga Annabi (ﷺ) kuma yayi umurni dashi kuma ake koyi daga gare shi Annabi (ﷺ).

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya


Marubuciya: Faridah Bintu Salis

Hakika Addinin Musulunci ya tabbatar da cewa ya halatta ga musulmi ya auri mace daga daya har zuwa hudu, kuma duk wanda ya auri sama da hudu to ya wajaba agare shi ya rabu da sauran, hudu kawai zai bari a tare dashi, dalilin auren mata hudu kuwa shine fadin ALLAH (SWT) cewa:

فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا

“.... Ku auri abunda ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abunda hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba.” [Suratul-Nisa'i: 03]

Babban abun dake daure kai shine yadda Mata da dama suka kekashe kasa da sama akan lallai mazajensu bazasu kasance da wasu mata ba koma bayan su, kafin a samu Macen da take ikirarin nuna kauna da amincewa wajen kawo mata abokiyar zama sai an kirga mata da dama kafin a samu hakan duk da kasancewar ana samu din.

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya

Wannan mummunar kiyayyar takin amincewa mazaje karin aure ya jefa al'ummah cikin halin ha'ula'i mai tarin yawa koda yake daman duk sanda aka bijirewa umurnin ALLAH (SWT) Toh ba za'a taba ganin da kyau ba, amma duk sanda akayi hakuri da jarrabawar ALLAH kuma aka amshe shi hannu biyu aka roke shi cin nasara da jarrabawa da ikonsa sai aga an samu maslaha tare da Nasara acikin dukkan al'amura.

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya

Kuma wannan kiyayya ce da ta game mafi yawan mata daga ma'abociyar addini da ma'abociyar ilimi dama jahilar da mafi yawan gama garin mata suna nuna tsantsar kiyayya ga kalmar nan ta KISHIYA !!!

Na sani cewa akwai munanan labarai dama na gani da ido dangane da abubuwan da suke faruwa a tsakanin mata adalilin kalmar nan ta KISHIYA, sai dai amma wannan bai kamata ace an butulcewa umurnin ALLAH (SWT) ba, domin daman dukkan rayuwar ɗan adam jarrabawa ce don haka ALLAH (SWT) ya jarraba bayinsa akan wannan mataki na karin aure daga biyu ko uku har zuwa hudu.

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya

Ina kara tunatarwa da jan hankalin 'Yan uwa mata da su kara sanin cewa duk wani abu da ALLAH (SWT) yayi umurni dashi kuma aka samu Annabi (ﷺ) Ya aikata shi, ko yace a aikata shi to hakika za'a samu hikimomi masu yawa acikinsa kamar yadda shima auren mace sama da daya yake da nashi hikimomi da dama.

Kadan daga ciki kuwa:

1. Hikima ce daga ALLAH (SWT) kasancewar akwai Mata wadanda ALLAH yake halittar su bakarara (Mace wacce bata haihuwa) saboda haka yayin da mutum ya auri mace wacce bata haihuwa maimakon ya sake ta sai akayi masa rangwamen kara aure idan yana da hali, wannan zai sa ya zamto ya taimakawa ita matar wacce bata haihuwar da ciyarwa da tufatarwa maimakon ace ya rabu da ita.

Amma sai ka samu mace bata haihuwa kuma tayi kane-kane akan cewar kada mijinta yayi karin aure, shin wannan Adalci ne, ya kamata 'Yar-uwa idan kin kasance a wannan matakin Toh kiyi tunani ki kuma sauya ra'ayin ki zuwa ga abu mafi dacewa da kyakykyawar tunani.

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya

2. Yana daga cikin Hikimar karin aure sanin kowa ne ALLAH (SWT) ya sanyawa mata Jinin haila da na biki, wanda a lokacin da suke cikin wannan hali bai halatta su tara da mazajen su ba, sabanin namiji wanda shi ALLAH bai halicce shi da wannan al'adar ba, saboda haka aka halatta masa auren mace sama da daya, domin idan daya daga cikin Matan nasa ta shiga cikin wannan hali zai iya karkatawa zuwa ga dayar ba tare da ya fada cikin wani hali ba wanda zai haifar masa da fushin ALLAH (SWT).

'Yar-uwa ya kamata kiyi karatun ta nutsu shin zaki so mijinki ya kasance cikin fushin ALLAH ??? Bayan ALLAH (SWT) ya halatta masa yadda zai kiyaye kansa da fadawa cikin fushinsa. Ko da yake akwai matan da suke ganin da ayi musu KISHIYA gara mazajensu su kasance acikin fushin ALLAH, har ma suke yiwa kansu ikirari da cewa: “DA KISHIYAR GIDA GARA KISHIYAR WAJE” Wa iyazubillah.

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya

3. Yana daga cikin Hikimar auren mace sama da daya kasancewar Mata sun fi maza yawa ako ina cikin fadin duniyar nan, ALLAH (SWT) ya halatta auren sama da daya domin a taimakawa sauran mata kada su fada ga halaka, saboda idan kowa ya auri mace daya kuma ya hakura da ita yaki karawa to hakika sauran mata kuwa suna iya shiga daya daga cikin halaye guda biyu:

HALI NA FARKO: ko dai su hakura su zauna hakan babu aure har mutuwa, wanda yana da wahala yin hakan domin sai wacce ALLAH (SWT) ya tsare ya kuma kiyayeta, domin yadda namiji yake da Sha'awa ita ma mace tana da ita, kuma tana so ta biya bukatar ta kamar yadda namiji yake so yaga ya biya bukatar sa.

Dalilan Karin Aure Sama da Ɗaya

HALI NA BIYU: Ko kuma su fada karuwanci domin neman biyan bukata wanda yin hakan musiba ce babba gare su da kuma musulmi baki daya.

Saboda haka mafita daga wannan shine a taimaka musu a aure su biyu-biyu, uku-uku ko hudu-hudu ga wanda yake da ikon hakan.

Saboda haka 'Yar-uwa mai kokarin hana mijinta karin aure shin zaki so Yaranki mata ko kannenki mata su kasance cikin halin ha'ula'i saboda wasu matan sun hana mazajensu su aure su ??? Nasan dai ba zaki so haka ba, toh ke meyasa kike kokarin hana mijinki auren wata mace bayan kuma ALLAH yayi umurni da hakan ???

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ILLOLIN ZAMA DA MATAR AURE GUDA DAYA

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Kowanne Miji ya Kula dasu Idan Zai Yi Magana da Matar Sa

SHIN KO KASAN ZAURAWA SUN KASU KASHI UKU?

'Yan-uwa mata ya kamata ku rage zafin kishi, ku zauna da 'Yan-uwanku mata lafiya a gidajen mazajenku ku bar hayaniya, ku yarda da tsarin ALLAH domin shine ya halattawa namiji ya auri mace hudu idan yana da halin hakan.

Wannan kadan kenan daga cikin Hikimomin auren mace sama da daya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user