Monday 23 December 2019

HUKUNCIN DA KANNYWOOD TA DAUKA AKAN HOTUNAN TSIRAICIN RAHAMA SADAU - AFAKALLAH

Tura Wannan Zuwa Ga
Rahama Sadau ɗaya ce daga cikin jaruman da su ka yi shura a masana’antar kannywood, kuma wadda a ke ganin ci gabanta ta tsallaka har kudancin kasar nan.


Jaruma Rahama Sadau, Afakallahu

Saidai Jarumar na shan ƙorafe-ƙorafe daga wajen al’ummar Hausawa da ma abokan aikin ta waɗanda su ke ganin halayyarta na ɗabi’u da kuma shigar sitira da ta ke yi ya ci karo da addini da kuma tarbiyar Bahaushe.

Rahma Sadau ta fara samun wannan korafe ƙorafen ne tun a shekarun baya da ta yi wani bidiyon waka tare da fitatcen mawakin zamani na Arewacin kasar nan mai suna Classic wanda har ya janyo malaman addini da masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood su ka yi ta sukar abun.

A ranar 11 ga watan Disamba shekarar 2019 jarumar ta gayyaci yan uwa da abokan sana'ar ta wajen wani taron taya ta murnar sabon gidan abincin da zata bude mai suna SADAUZ HOME a garin kaduna.

Cikin mutanen da ta gayyata akwai mawakin Arewa Classiq aciki, ta kuma saki wasu hutuna da bidiyo tana rawa mawakin yana mata waka a wajen taron, wannan abun ya jawo cecekuce a kafafen sada zumunta har ya kai ga ma'abota kallon fina-finan Hausa suna yin raddi ga masana’antar akan wannan hotuna da bidiyon da ta saki.

Wannan dalilin ya sa shuwagabannin gudanarwa ta Kannywood su ka dakatar da Jarumar.

Hakan ya ja hankalin al’ummar Hausa da kafafen sada zumunta su ka yi ta tofa albarkacin bakinsu.

Wanna ba shakka ya kawowa Jaruma Rahma ci gaba a sana’arta ta fim domin kuwa a dalilin hakan ta samu ganawa da manyan mawakanna duniya irin su Akon a kasar turai.

To ko Rahma Sadau ci gaban mai hakan rijiya ta samu?

Wannan ita ce muhawarar da ke yawo a bakunan mutane.

Hakan ya sa mun tintiɓi jagororin masana’antar domin jin inda a ka haihu a ragaya.

A tambayar da wakilin mu ya yiwa Alhaji Jamilu Ahmad Yakasai Shugaban ƙungiyar masu shirya fina-finai na Arewa Reshen Jihar Kano, ko su na sane da ƙorafe ƙorafen da mutane ke yi a kan Jarumar?

Ya amsa da cewa: “Ba za mu tafi da duk wani baragurbi ba idan har ya na amsa sunan shi dan fim ne. Wasu korafe korafen mu na ji, wasu kuma ba ma sani domin sai ka na bibiyar mutum ka ke sanin abunda ya fada a soshiyal midiya.

Mu a tsarin mu na shugabanci duk wani da ya yarda cewa shi dan mu ne kuma ya yi wani abu da ya taba doka ta addini da al’adarmu to za mu yi iya yinmu domin daukar matakin ladabtar da shi.” In ji Yakasai

Ya kara da cewa a shekarun baya ta yi abunda bai dace da ka’idojin masana’antar ba wanda har jagorancin masana’antar ya dakatar da ita, amma saboda nadama da ta yi ya sa shugabancin hukumar tace finafinai da dabi`a ta Jihar Kano ta yafe mata. “Ni ban san a kan wane tsari a ka yafe mata ba a baya kuma wane irin yarjejeniya su ka yi.” A cewar Yakasai

Mun ji ta bakin Shugaban Hukumar tace Finafinai da Dabi`a ta Jihar Kano Alh. Isma’il Muhammad Na’Abba wanda a ka fi sani da Afakallah wanda shi ne ya yafe mata wancan laifin a baya, ko me zai iya cewa a kan dabi’un Rahma Sadau? “To mu dai hurumin hukumar mu shi ne tace hotuna da sautin fim ko waka mu tabbatar ba su ci karo da dokokin mu ba, duk abinda Rahma za ta yi da rayuwarta idan har ba a fim ko waka ta yi ba to ba mu da hurumi.

Sai dai a matsayinta ta Bahaushiya kuma musulma, ya kamata ta ji tsoron Allah, ta sani cewa sabawa Allah domin neman ci gaba ganganci ne ba karami ba. Kuma duk wadanda ta ke kwaikwaya ba za su karbe ta ba a matsayin ta su.” In ji Afakallah

Wakilin mu ya kara jin ta bakin Alhassan Kwalle daya da ga cikin masu fada a ji a masana’antar kannywood. Inda ya ke cewa
"Duk wani abun da rahama sadau zatayi a waje indai ba a acikin fim tayi ba toh ba ruwan mu, kuma kanta tayimawa tunda ta san ita mace ce kuma duk dadewar da za ta yi nan gaba za ta so ta yi aure ta kuma haihu, baya ga haka zata so ta barwa yaran ta abun da za su yi alfahari da shi.

 To ina ganin duk abinda ta yi kanta ta yiwa ba masana'antar Kannywood ba, tunda ta na da iyaye kuma ta na da ‘yan uwa su ne za su rika yi mata fada ba mu ba.

Amma idan ta yi abun da bai dace ba acikin fim toh wannan mu ya shafa kuma za mu dauki duk wani matakin da ya dace, zamu hukunta Marubucin da Furodusan shirin da a ka yi wannan laifin a ciki. Saboda haka idan wani ma ba ita ba ya je waje yayi abin da bai dace ba kan shi ya yiwa da yan uwansa, su zai barwa abun fade. Inji Alhassan Kwalle

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Cikakken Tarihin Rahama Sadau

Shin dagaske ne Rahama Sadau tayi Film din Batsa na Blue Films?

Kalli Zazzafar Sabuwar Wakar da ta Girgiza Kannywood dama Duniya baki daya...Latest Song Full HD Video

Daga karshe yayi kira ga duk wani jarumi ko jarumar da ke Masana'antar Kannywood da su sani cewa fa akwai Allah a duk abin da za su yi kuma akwai mutuwa dole duk abin da mutun ya aikata sai ya tsaya gaban Allah don kare kansa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





Source: Northflix
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user