Monday 2 December 2019

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN JIHAR BAUCHI KASHI NA UKU

Tura Wannan Zuwa
Kashi na uku

Daga nan sai Yakubu yasa aka gina ramin ganuwa kusa da Inkel da ya ke da zama, akayi gini a wurin tare da sanya masa ƙofofi huɗu, sannan ya taso daga Inkel ya zauna acikinsa tare da jama'ar sa.

Tarihin Jihar Bauchi

MarubuciSADIQ TUKUR GWARZO

Wannan gari yanzu haka shi ake kira da suna BAUCHI.

Mutane kuwa sai suka rinƙa zuwa gareshi rukuni rukuni suna yi masa mubayi'ar girma har sai da suka yawaita, ya zama suna fita wajen gari suna yin gidaje. Yaƙi kuma ya rinƙa fita da hare hare zuwa yankunan kafirai.

Yakubu ya aiki Muhammadu Kusu, da Dawaki Hammada da Yari su tafi yaƙi zuwa zaranda da Felu da Geji da Bulu, suka karkashe su tare da kamo ƴaƴansu bayi. Sannan Suka komo wurin Yakubu cikin aminci da tarin ganima.

Bayan wannan, sai ya aiki Sarkin Yara Ibrahim ya tafi dutsen Boli da yaƙi. Da ya isa waɗansu sukayi sulhu dashi, waɗansu kuma suka ƙi don haka ya yaƙe su. Sannan ya wuce har zuwa Lago da Gabari yayi yaƙi dasu. Daga ƙarshe ya koma wurin Yakubu da ganima mai yawa.

Haka kuma saɓani ya auku tsakanin Mallam Yakubu na Bauchi da Sarkin Gwambe Buba Yero,inda har sai da aka gwabza yaƙi a tsakani.

Yakubu ya ƙetara kogi ya cimma Gwambawa da yaƙi, akayi kashe kashe, daga bisani akayi sulhu. Gwambawa sukayi alƙawari ba zasu ƙara tada fitina irin wannan ba.

Bayann wannan kuma sai Yakubu ya sake shiryawa ya tafi yaƙi zuwa Bununu, da Lere da Pursum da Bukuru sannan ya koma gida. Babu jimawa kuma ya sake tashi yaƙi zuwa Yamyam Ramu da Yamyam Jini. Daga nan sai ya shige Montal da Yargam da wasu wuraren mazauna duwatsu da suke biye da Yargam har zuwa Unkwai da Ɗan chandam.

Daga nan sai Yakubu ya ɗauki haramar yaƙi zuwa Lafiya da Awai da sauran wuraren gishiri. Bayan dawowar sa gida Bauchi ne mutane suka ƙaru wurinsa jama'a jama'a, da suka haɗar da Hausawa da Fulani, da Barebari dama sauran ƙabilu. Hakan yasa Yakubu ya ƙara girman Bauchi daga ƙofa huɗu zuwa ƙofa tara.

MAKALOLI MASU ALAKA:





Bayan wannan sai Yakubu ya ɗaura haramar yaƙi sannam ya tafi zuwa Das, ya zauna cikinta yana yaƙi da mutanem ta yaƙi mai tsanani har tsawon shekaru biyu, ya zama yana bin mutanen Das cikin duwatsu yana kisa.. ana kan haka ne kuma fitinar Kulumbu ta motsa tsakanin sa da Sarkin Musulmi na lokacin Muhammadu Bello.

Zamu Ci gaba Insha Allah.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user