Saturday 14 March 2020

Shin Ko Kasan Yadda Bala'i Yake Tafiya A Cikin Rayuwar Ka?

Tura Wannan Zuwa
Bala'i ya tashi zai yi tafiya, sai ya nemi aboki. Ciwo ya ce zan bi ka, Bala'i ya ce ban yarda da kai ba, domin kai da an sha magani sai ka ɓace, kuma wanda duk ka shafe shi, zai samu lada.

BALA'I YA TASHI ZAI YI TAFIYA..

Marubuci: Dr. Mansur Sokoto

Gobara tazo ta ce za ta bi shi, sai ya ce, ban aminta da ke ba, domin ke idan kin gama aiki sai a sake share wuri aci gaba da rayuwa.

Bashi ya iso yana yi wa kansa kirari: "Ni ke hana mutum barci, in hana shi zuwa masallaci, in sakar masa ciwo marar dalili, in sa shi ƙarya da saɓa alkawari, in jefa shi gidan kaso, in ya mutu in gaji gidansa da iyalinsa, sannan ba zan barshi ba sai na tsaya da shi wurin hisabi a gaban Allah."

Nan take Bala'i ya ce zo mu tafi tare, tabbas kai ne abokin tafiyata.

Babu abokin tafiya in ba kai ba.

Allah ya raba mu da musibar bashi, Amin!!!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user