Saturday 14 March 2020

Karanta Kayatacciyar Hikayar Maciji da Tsuntsaye

Tura Wannan Zuwa Ga
Wannan hikayar shahararra ce acikin littafin hikayoyi na 'Kalila wa Dhimma', musamman yadda aka rinka amfani da ita wajen koyar da yara masu jiran sarauta hikimomin kuɓuta daga zaluncin duk wani azzalumi.

Cikin Hikima ake Warware Matsaloli...

Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo

Hikayar tace:-

A saman wata babbar bishiyar Kuka, anyi wasu tsuntsaye guda biyu waɗanda ke rayuwa acikin sheƙarsu dake saman wannan bishiya.

Sai dai kuma akwai wata damuwa tattare da waɗannan tsuntsaye.

Damuwar itace, duk sanda suka ƙyanƙyashe ƙwayayensu sai wani maciji ya zo ya shanyesu, shikuwa a ƙasan bishiyar yake rayuwa cikin wani kogo.

Kullum haka, kullum haka.

Rannan sai sukayi shawarar suje su sanar da Mallam Dila domin ya basu shawarar hanyar kuɓuta daga wannan ƙunchi da suke ciki.

Bayan sun same shi suke shaida masa irin zaluncin da maciji keyi musu gashi sun rasa yadda zasuyi.

Dila yayi ajiyar zuciya, sannan yace "kada ku damu, komai ƙarfin azzalumi, ƙasƙantaccen abu yana iya cin galaba akansa cikin hikima"

Yaci gaba da cewa "saboda haka, shawara ɗaya dazan baku shine, ku shiga cikin gari kuyi duba ga gidan dayafi kowanne arziki da kuma dakaru, sannan ku lura da abu mafi daraja wanda akayi sakaci dashi, sai ku ɗauko shi kurinka tafiya a hankali a hankali, da kunzo bakin kogon maciji sai ku wurgar dashi kuyi naku wuri".

Tsuntsaye sukayi godiya sannan suka tashi firrr! zuwa cikin gari domin aiwatar da shawarar mallam Dila.

Ai kuwa suna ta zagaya gari, sai suka hango 'yar sarkin garin tana wanka a cikin wani ƙaramin tafki, ga abin wuyanta yana ta walwali ta ajiyeshi a gefe saman kayan sanyawarta, sai kuma dakaru suna ta shige da fice.

Kwatsam sai gani akayi tsuntsuwa ɗaya tayi ƙasa-ƙasa tare da wuftar wannan abin wuya da bakinta, sannan ta tashi sama a hankali tana mai karkaɗa fuka-fukanta.

Koda faruwar haka sai hankalin 'yar sarki da dakaru yakai gareta. 'Yar sarki ta daka musu tsawa da cewar subi bayanta su karɓo mata abin wuyanta.

Ai kuwa a haka tsuntsuwar nan ta rinka janyo dakaru, ta sauka acan, da zarar sun runtumo gareta sai ta tashi, ta sake sauka a wani wurin, a haka har tazo bakin kogo sannan ta wurgar dashi.

A wannan lokaci maciji nata sharar bacci abinsa, yaci abinci yayi hani'an, jira yakeyi dare yayi yahau sama don ƙara farauto kwan tsuntsaye kamar yadda ya saba.

Karar wurgar da abin wuya kuwa sai ya tashe shi.

Koda ya hango abu mai walwali sai yayi sha'awar zuwa don ganin ko menene.

Yana daf da fitowa dakaru suka iso wurin suna ta haki, ɗaya daga cikinsu ya mika hannu zai ɗauki abin wuya amma sai ya jiyo motsi, dubawarsa keda wuya sai yaga maciji na fitowa gareshi.

Nan take kuwa waɗannan dakaru suka rufar masa da duka da sanduna har sai da suka halaka shi, sannan suka ɗauki abin wuyan gimbiya suka tafi abinsu.

Tun daga wannan rana tsuntsaye suka samu kwanciyar hankali, domin babu mai hanasu sakewa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: