Monday 30 March 2020

Karanta Bambancin Jiya da Yau a Zamanance

Tura Wannan Zuwa Ga
Haƙiƙa munzo wani zamani wanda kusan dukkan abinda ke cikinta gwamma na jiya da yau ta kowanne fuska.

ZAMANIN GWAMMA JIYA DA YAU...

Marubuci:- Kamaluddeen Kmc

Da zaka sami wani babban mutum da shekarun sa sunkai 40 Ko 50 ko 60, idan ka kunna masa wani tsohon waka (old school musics) da zakaga yashiga tinanin rayuwar jiya.

Wani zai ce maka Allah sarki harka tinamin da rayuwar ƙuruciya lokacin duniya tana zaune lafiya.

Dayawan mutane sunason old school musics (Tsofaffin Waƙoƙin da) saboda yana tinamusu rayuwar jiya lokacin fitinar rayuwar duniya bai shafesu ba.

Lokacin suna cikin ƙuruciya babu damuwar duniya akansu.

Alal haƙiƙa alokacin bawai babu damuwar duniyar bane kwatata, kawai dai damuwar bai kai na yau yawa ba, shiyasa idan suka tina rayuwar jiya sai su ɗanji daɗi aransu.

Dayawan mutane lokacin da suke ƙananun yara suna sha'awan suyi maza maza su girma su sayi mota su  gina gida suyi aure su kuma tara dukiya.

Amma dazaran sun girma sun mallaki waɗannan abubuwa zaka samu damuwowi sunyi yawa, matsaloli sun yawaita.

Shiyasa idan suka tina rayuwar jiya saboda lokacin babu irin matsalolin rayuwa dasuke ciki saikaga sunji daɗi harma kuma suna sha'awan jiya maimakon yau.

Dayawa zakaga mutane suna yawan jin tsofin kiɗa saboda surika Tina rayuwar jiya wanda hakan yana samusu nutsuwa da nishaɗi a zukatan su.

Dayawan mutane idan kabasu zaɓi tsakanin rayuwar jiya da yau wanne yafi musu dadi?

Wallahi kashi 90 na mutane zasuce maka gwamma jiya da yau ta kowanne fuska.

A zamanin jiya, idan ka farka da sassafe zakayi tajin kukan tsuntsaye iri-iri a gidanku ko a maƙwabta, yawaitar tsuntsaye alamace ta albarka a waje, amma yanzu duk babu su, kafin kaga tsuntsu a gidanku saika daɗe.

A zamanin jiya , kusan kowani gida zakaga akwai bishiyan lemo, gwanda , gwaiba da sauran su, lokacin babu zafin Rana irin na zamanin yau.

Kusan kowanne gida zaka sami inuwar bishiya , mutane kan huta susha nishaɗi amma yanzu yawancin gidaje babu.

A zamanin jiya ne kaza keyin ƙwayaye  20 kuma ta ƙyanƙyashe ƙwayaye 18 ko kuma duk ashirin ɗin duka.

A zamanin jiya ne ilimi keda albarka, kaga ɗan primary ya iya turanci sosai, ya kuma iya rubutu da karatu.

Idan kana makarantar kwana ana baku abincin karin kumallo ƙwai da kifi, biredi da shayi.

Littafin karatu yana cikawa akwai su a ma'ajiya saidai abaka sabon littafin rubutu amma banda yanzu.

Lokacin ne jira ake kagama karatu gwamnati ko kamfani ta baka aiki, har roƙonka akeyi amma banda yanzu, yanzu kam da kuɗinka ma daƙyar zaka samu wani aikin komai yazama alfarma wa kasani wa yasanka.

A zamanin jiya ne anabi gida-gida ana neman wanda suka gama primary a turasu ƙasar waje suje suƙaro karatu alokacin ma iyaye basu so suma yaran baso suke ba. Amma yanzu fa? Kafin ka samu a ɗauki nauyin karatun ka saika haɗa da connections ma ba connection ba.

A zamanin jiya ne aure keyin albarka fiyeda yau, lokacin da Mata keyin auren biyayya kuma su zauna da mijinsu lafiya harma a hayayyafa.

Lokacin da Mata sukafi yin aure domin Allah, domin neman lada.

Lokacin sadaki ne ake biya babu al'ada sosai.

Mace saitayi shekara 50 a gidan miji amma bata taɓa yaji ba.

Amma yanzu fa?

Yanzu auren soyayya akeyi amma babu lokacin da aure yafi mutuwa kamar zamanin yau da muke ciki.

A zamanin jiya shuwagabanni keyin adalci suna tsoron zalunci.

Lokacin da albarkatun gona keyi batareda ansanya masa taki ba.

Lokacin babu cututtuka birjik irin na yau.

Lokacin da komai yafi inganci da aminci babu ha'inci irin na yau.

Lokacin da budurwa ke rufe jikinta gabaki ɗaya.

Lokacin da ƴaƴa ke tausayin iyayen su.

Lokacin da kwanciyar hankali ta yawaita.

Ashe da tafi daɗi, Ashe da tafi sauƙi.

Ya Allah ka sauƙaƙa mana kada ka kuntata mana.

اللهم يسر ولا ة اسر .

 ربنا اتنا ف الدنيا حسنة والاخرة حسنة وقنا عذاب النار.

Ya Allah ka karemu daga fituntunun ƙarshen zamani masu raba mutane da imani Amin.

امين يا الله.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user