Saturday 7 March 2020

Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (1)

Tura Wannan Zuwa Ga
An hakaito cewa a cikin wani shuɗaɗɗen zamani mai tsawo da ya gabata, a cikin birnin Dimashka na kasar Sham, an yi wani Halifa mai suna Abdulmalik ɗan Marwan wanda yake shi ne Halifa na biyar a cikin zuri'ar Umayyad.

Hikayar Birnin Tagulla

Wata rana yana zaune cikin fadarsa, hakimansa da wazirai sun kewaye shi ana tsakiyar fadanci, sai aka fara labarin shugabannin da suka shuɗe a baya, da irin salon mulkinsu, har aka taƙalo maganar Shugaba Sulaimanu ɗan Dawuda (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su) irin yadda ya tafiyar da tsarin mulkinsa, da yadda Allah Maɗaukakin Sarki ya hore masa ikon mutane da aljanu da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari da iska da ruwa da giza-gizai. Sai Halifa ya ce, "An ce ba a taɓa yin wani Sarki da Allah ya ɗaukaka darajarsa ba kamar Shugaba Sulaimanu dan Dawuda, kuma ba za a yi wani ba a bayansa. An ce yakan ɗaure aljanu cikin batta ta farin ƙarfe ya like bakinta da darma ya buga hatimin da ke ga zobensa bisa marufin."

Daga nan sai wani mutum mai suna Dalibu ɗan Sahalu, wanda yake mai ilmin tafiye-tafiye ne, kuma masani akan dukiyoyin da mutanen da suka shuɗe suka binne a ƙarƙashin ƙasa, ya ce, "Ya Shugaban Muminai, Allah ya ba ka nasara, mahaifina ya taɓa ba ni labarin da kakana ya gaya masa, ya ce wata rana, shi kakan nawa, ya tafi tare da fatake zuwa ga birnin Sisili na ƙasar Girka. Suna cikin tafiya sai iskar teku ta taso musu, ta kwashi jirginsu ta canja masa tafarki. Bayan sun yi wata guda suna tafiya sai suka iso ga wani babban dutse a cikin wata ƙasa ta daga ƙasar Allah Madaukakin Sarki, ƙasar da babu ɗaya daga cikinsu da ya san ta.

Kakana da yake ba mahaifina labarin ya ce, "Da dare muka isa inda wannan dutse. Yayin da gari ya waye sai muka ga mutane, baƙar fata, suna fitowa daga cikin kogunan dutsen, kowanensu tumɓur yake babu mai ko bante, ga su nan kamar dabbobi. Babu mai jin Larabci cikinsu sai Sarkinsu kaɗai, shi ma irinsu ne. Lokacin da Sarkin ya ga jirginmu sai ya zo wurinmu tare da wasu mutane. Ya gaishe mu, ya tambayi labarinmu. Muka gaya masa labarinmu duka. Sai ya ce, "Ku saki ranku, babu abin da zai same ku."

Da muka tambaye shi labarinsu sai muka gane ashe dai su mutane ne da ba su da wani takamaiman addini, haka suke kara zube. Ba sun san da zuwan Annabi Muhammadu ba (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) balle su san ya faku. Sarkin ya ce mana, su ba su ma taɓa ganin wani ɗan Adam ya zo gare su ba, sai yanzu da Allah ya kawo mu. Ya ƙara kwantar mana da hankali, ya ce kada mu ji tsoron su. Suka marabce mu tsawon kwana uku, suna kawo mana naman dabbobi da tsuntsaye da kifi, ban da wannan ba su da wani abinci. A kwana na huɗu, Sarki da kansa ya ja mu zuwa bakin ruwa, wai mu ga yadda ake kamun kifi. Muka tarar da wani mutum ya jefa komarsa cikin ruwa domin ya kamo kifi. Yayin da ya jawo komar sai muka gan ta cike da kifi, har da wata kukuma ta  farin ƙarfe, an like bakinta da darma an buga hatimin zoben Shugaba Sulaimanu.

Mutumin nan ya ɗauki battar ya ɓalle bakinta, sai muka ga wani hayaƙi yana fitowa daga cikin battar, launin hayaƙin nan shuɗi ne. Hayaƙi ya hau zuwa ga sama ya taru wuri guda, sai muka riƙa jin wata murya mai ban tsoro ana cewa, "Na tuba, na tuba, ya Annabin Allah, ba zan ƙara saɓa wa umurninka ba har abada."

Nan take sai hayaƙin nan ya juye shirgegen ƙato dogo, saboda tsayi har kansa ya shiga cikin gajimare, girmansa kamar kubba. Kafafuwan kuwa sun tokare ga ƙasa kamar bishiyoyin rimi, kafin mu gama kallonsa har ya ɓace cikin iska, muka yi kamar za mu some ɗon tsoro. Amma bakin mutumin nan bai ko yi gezau ba, kamar kunama ta harbi dutsi. Muka tambayi Sarki wannan abu mai ban mamaki, sai ya ce mana, "Waɗannan irin aljanun nan ne da Shugaba Sulaimanu kan kulle a cikin batta, idan sun yi masa laifi, ya jefa battar a cikin teku. Battar nan ita ce kamar kurkukun aljanin da aka ɗaure a cikinta. Sau da yawa mutanenmu kan tsamo waɗannan battoci yayin da suke kamun kifi. Idan suka buɗe battar sai aljanin ya fita yana cewa, 'na tuba ya Annabin Allah,' su a zatonsu a gaban Shugaba Sulaimanu suke."

Halifa ya yi mamaki da jin wannan labari na Dalibu dan Sahalu, ya ce, "Tsarki ya tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Haƙiƙa Allah ya ba wa Sulaimanu ɗan Dawuda mulki mai girma."

Nabigatul Zubiyanu na cikin wannan faɗa, sai ya ce, "Haƙiƙa Dalibu ɗan Sahalu ya yi gaskiya, labarinsa ya yi daidai da wannan fadar:

"Yayin da Ubangiji ya ce wa Sulaimanu, na hore maka mulki dukansa, ka yi adalci da gaskiya. Ka kyautata wa wanda ya yi maka biyayya, ka ɗaure wanda ya saɓa maka."

Duk kuwa wanda ya saɓa umurninsa sai ya ɗaure shi cikin batta ya jefa cikin teku."

Halifa ya yi shiru yana mamaki, can sai ya ce, "Wallahi ina so in ga irin wannan batta da Shugaba Sulaimanu kan ɗaure aljanu a cikinta da idona, domin ita gargaɗi ce ga masu hankali."

"Ya Shugaban Muminai," in ji Dalibu, "ai wannan ba wani abu ne mai wahala ba gare ka. Ka aika zuwa ga ɗan uwanka Abdul'aziz ɗan Marwanu, ya rubuta wa Musa ɗan Nusairi takarda, wanda yake shi ne Shugaban ƙasashen Magarib wanda ka naɗa ni a matsayin wazirinsa, ya aika manzo da doki zuwa ga dutsen nan da na ba ka labari, ya samo maka waɗannan battoci adadin waɗanda kake buƙata. Domin kuwa dutsen nan yanzu yana cikin yankin kasashen da Musa ɗan Nusairi ke mulki."

Halifa ya amince da shawarar Dalibu ya ce, "Ka faɗi gaskiya ya Dalibu. Amma yanzu kai ne manzon da zan aika ga Musa ɗan Nusairi. Zan ba ka dukkan abin da kake buƙata na guzuri, kuma zan riƙa kula da iyalinka har zuwa lokacin da za ka dawo."

"Na kuwa ji daɗi da ka zaɓe ni bisa ga wannan kuduri naka mai matukar muhimmanci, ya Sarkin Muminai." In ji Dalibu dan Sahalu.

Halifa ya ce, "Ina yi maka fatar Allah ya tsare ka da dukkan wahala yayin wannan tafiya taka."

Halifa ya rubuta wasiƙa zuwa ga ɗan uwansa kuma wakilinsa da ke mulki da ƙasar Misira watau Abdul'aziz ɗan Marwan. Haka kuma ya rubuta wata wasiƙar zuwa ga Musa ɗan Nusairi wanda yake wakilinsa ne mai mulki da ƙasashen baƙar fata na ɓangaren Yammaci da Arewacin duniya, ya umurce shi ya tafi da kansa tare da Dalibu zuwa ga dutsen nan na baƙaƙen mutane domin samo masa battar Shugaba Sulaimanu ɗan Dawuda. A cikin wasiƙar ya kara da cewa, ya yi duk yadda za ya iya domin ganin cewa an samo masa battar nan, ba shi da wani uzuri da zai bayar idan ba a sami battar ba.

Halifa ya kawo takardun nan biyu ya ba wa Dalibu dan Sahalu, ya shirya masa guzurin tafiya mai yawa tare da rakiyar askarawa wasu a kan dawaki wasu a ƙasa. Ya aika wa iyalinsa da buhunnan abinci da kuɗi masu yawa. Dalibu ya tafi tare da askarawa, ba su gushe ba suna tafiya har suka iso Misira.

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Fassar:

Ibrahim Malumfashi

Danladi Haruna

Bukar Mada

Ga waɗanda basu samu damar karanta hikaya ta biyu ba to ga tanan mun kawo muku.

Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (2)

Za mu Ci gaba ranar Asabar mai zuwa dai-dai wannan lokaci (ƙarfe 9:00 PM, na dare), In Sha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: