Sunday, 10 May 2020

Karanta Addu'a Yayin Da Wani Abu Wanda Baka So Ya Faru Ko Kuma Abinda Yafi Ƙarfin Ka

Tura Wannan Zuwa
Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Mumini ƙakƙarfa ya fi alheri kuma ya fi soyuwa ga Allah daga mumini mai rauni, a tare da kowanne daga cikinsu kuma akwai alheri".

Addu'a Takofin Mumini

Ka yi kwaɗayin abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah; kada ka gajiya. Idan wani abu ya same ka, ka kada ka ce; da na aikata kaza da kaza, da kaza ya kasance, sai dai ka ce;

قَدَرُ اللهِ وَمَا شَاءَ فَعَلَ.

Kadarullahi Wama Sha'a Fa'ala
Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi yake aikatawa; domin da na sani tana buɗe kofar aikin shaiɗan.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user