Saturday 2 May 2020

Nasiha Ga Mai Azumi

Tura Wannan Zuwa
Bismillahirrahmanirrahim, Yakai ɗan uwa musulmi, ka sani cewa Azumi garaɓasa ce ta musamman da Allah ya baiwa wannan al’umma ta Muhammad (S.A.W).

Guzirin Watan Ramadan

Marubuci:- Mahmud Isah Yola

Cikin ta ana buɗe ƙofofin Aljannah don masu shiga, ana kulle ƙofofin wuta Saboda ba’a fatan a samu masu shiga.

Shaiɗanu masu umurtan mutane da miyagun ayyuka an ɗaɗɗaure, ko wani dare Allah yana ‘Yanta dubban bayi ya musu kyautar Aljannah ya kuma amintar dasu daga Wuta, a cikin ta akwai wani dare, da ibada a cikin shi yana dai-dai da ibadan shekara tamanin da ‘Yan Kai.

Ya kai Mai fatar rahamar ubangijinsa, yawaita ayyukan alkahairai cikin wata domin samun yardan ubangijinka.

Ya kai mai aikata saɓo ko laifi, ka sani ya wajaba a kanka ka bari cikin wannan wata, in har ko ka ƙi, tsinuwan Manzon Allah (S.A.W) ta tabbata a kanka, duk wanda annabi ya tsine masa kuwa ya halaka.

Wani al’amari na musamman:

Allah ta’ala na cewa:

”Lallai mun saukar da wannan Kur’ani cikin dare mai albarka………. A cikin ta ake rarrabe dukkan al’amari…”

Suratud Dukhan.

Wannan aya Malaman tafsiri sukace:

Tana nuna cikin Ramadan ake ƙaddara abubuwan da zasu auku ga bayi a shekara, na alkhairi ko sharri.

Saboda haka ka dukufa wajen addu’an Allah ya sada ka da alkhairan da kake buƙata, ya kuma kare ka daga sharrin da kake tsoro.

Addu’ar mai azumi karɓaɓɓiya ce.

Kenan za’a baka alkhairan da ka nema, a kuma kare ka sharrin da ka nemi tsari daga gare shi.

Ya Allah ka sada mu da alkhairan wannan wata, ka kare mu dukkan sharri, ka kuma buga mana hatimin ‘Yan aljannah Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user