Friday 10 July 2020

Karanta Falala Guda Hudu Ga Mutumin Da Baya Taba Jikin Budurwar Sa

Tura Wannan Zuwa Ga
Duk mutumin da baya hiran batsa da budurwan sa kuma baya taɓa jikin ta idan suna hira to akwai falala guda huɗu da Allah zai yassare masa insha Allah.

Soyayyar Gaskiya

Marubuci:- Kamaluddeen Kmc

1. Allah zai sanya muku albarka acikin auren ku kuma ya kaɗe muku fitun tunu.

2. Zaku sami cikakkiyar zuri'a tagari saboda kafin auren naku baku chakuɗashi da saɓon Allah ba. don haka yaran ku ma suma Allah zai kare muku su daga sharrin maza ɓata gari.

3. Saboda jin tsoron Allah da kukayi kuka ƙi bin son zuciyarku wajen saɓawa Allah ta hanyar maganganun batsa ko taɓa juna to Allah zai sauƙaƙe muku hanyar da zakuyi aure batareda kunsha wuya ba.

4. Zaku sami kyakkyawan yadda dajunan ku dakuma aminta dajuna. idan kafita kayi dare awaje matarka tanada kyakkyawan zaton alheri agareka saboda tasan cewa, baka ɗaya daga cikin matasa masu lalata yaran mutane agari. Kamar yadda kaima zata sami kyakkyawan shaida daga gareka.

Duk waɗannan zaka samesu ne a dalilin kiyaye saɓon Allah wajen neman aure ta hanyar kiyaye maganar batsa ko taɓa juna ballantana akaiga yin zina.

Allah ta'ala ya ƙara karemu daga bin son zuciya Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user