Saturday 11 July 2020

Shin Ko Kasan Dubban Kudaden Da Zaka Kashe Idan Kana Son Auran 'Yam Matan Maiduguri?

Tura Wannan Zuwa Ga
Da Allah zai sa acikin masu kuka da lefen nan su taro aure a maiduguri da sun gane cewa hausawa ba lefe suke ba.

Ni ne Shaida Wallahi

Marubuci:- Faruk Abubakar

Ga kaɗan daga cikin jeri abinda na sani:

1. Lefen kansa aƙalla ana son akwati huɗu ko biyar.

2. Kayan uwar (ita ma akwati daban)

3. Kayan uba (aƙalla kayi masa ɗinkin auren, kuma ka saka hula da turare a akwatin uban 'yar)

4. Kayan uwar ɗaki (wato su mutanen maiduguri idan yarinya ta girma ba komai uwarta zata ke ji daga bakinta ba, sai dai ita yarinyar ta samu wata a unguwar ta zame mata uwar ɗaki)

5. Kayan takwara (wato matar taka idan tana da takwara a danginsu to sai ka siyawa takwarar atamfa)

6. Kuɗin anko ( kafin aure dole ka bawa amarya da ƙawayenta kuɗin anko)

7. Kuɗin lalle da fulawa (akalla kuɗin ya zama ₦5,000)

8. Kuɗin kitso (aƙalla shima ₦2,000)

9. Kayan ƙannen uba mata da ƙannen uwa mata (suma akwati daban)

10. Kayan alwali da matarshi (shi ma dai atamfa biyu ko uku za'a bashi)

11. Kuɗin turaren wuta (aƙalla zaka bada ₦5,000)

12. Kuɗin cincin (aƙalla ana son ganin ₦3,000)

13. Kuɗin dafa abinci (amarya da ƙawayenta zasu dafa abinci, kai zaka bayar aƙalla shi ma ₦10,000)

14. Sadaki aƙalla a talauce yana kaiwa ₦100,000 ko kuma ₦150,000, wannan ma yayi sauƙi kenan.

A iya tunanina da nazari na babu ƙabilar da suke aure a ɓagas kamar  hausawan Mu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user