Monday 6 July 2020

Karanta Hakkin Sallah Akan Kowanne Musulmi

Tura Wannan Zuwa
Mafi yawa zaka ga Limamai ko dai Malamai ne ko Ɗalibban ilimi ko Alarammomi, amma da ƙyar ka samu masu waɗannan siffofin suna kiran Sallah. Mafi yawan Ladannai basa da alaƙa da ilimi ta kusa ko ta nesa.

Bamu Baiwa Kiran Sallah Haƙƙin Sa

Marubuci:- Dr. Jabir Sani Maihula

Wannan ya haifar da matsaloli kamar haka:

1. Akan samu kurakurai na lafazi da na sifa wajen kiran Sallah. Hadisan da sukayi magana game da kiran Sallah basu da yawa kamar hadissan Sallah, amma duk da haka zaka samu  mutum yana kiran Sallah amma baisan Hadisi ko ɗaya da ya koyar da kiran Sallah ko lokutan Sallah ba, kuma bai karanci kiran Sallah a wani littafin fiqhu ba.

2. Kuskuren lokaci: Akan samu wasu masu kiran Sallah suna kira kafin lokaci yayi musamman a sallar la'asar da Magrib saboda basu san yadda ake gane lokaci ba, kuma wasun su ko karatun Boko basu iya ba, ballantana su yi amfani da jadawali da ake sakawa a masallaci.

Babbar matsala shine waɗannan Mutanen suke ɗauke da loudspeaker, ana jin muryar su a ko'ina, don haka sun zama abin koyi ko dai-dai suke yi ko ba dai-dai ba. Na kan shiga masallaci sai naga ladani zai kira Sallah alhali saura minti uku ko biyar lokaci ya shiga, sai nace dashi lokaci baiyi ba, sai yace gayacen an kira wancen masallacin! Waya Kira? ya san lokacin Sallah da yadda yake shiga?? kawai yana da loudspeaker ana jin muryarsa, don haka ya zama hujja!!!

Muna buƙatar mu duba muga ta ya zamu yi maganin wannan matsalar. Ko dai Ɗalibban ilimi su kusanci wannan aikin mai ɗumbin lada ko a yiwa masuyin aikin bita da koyar wa. Na taɓayin wannan na biyun a Masallatai biyu na unguwar mu, kuma naga alfanun sa matuƙa.

Allah Ya Shiryar da mu ga abinda Ya ke so kuma Ya yarda da shi Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user