Tuesday 15 September 2020

Sauke Kundin Sakonnin Soyayya Audio Na Yusufuddeen A Yusuf

Tura Wannan Zuwa Ga
Wannan KUNDIN SAKONNIN SOYAYYA cike yake da daɗaɗan saƙonni masu ratsa sassan zukatan masoya, idan har kana sauraro to bazaka san lokacin da shauƙin soyayya zai ziyarci farfajiyar zuciyar ka ba, abin dai ba a magana.


KUNDIN SAKONNIN SOYAYYA

Idan har kana soyayya, lallai wannan Audio na KUNDIN SAKONNIN SOYAYYA zai faranta maka rai, haka kema idan kina soyayya, karku sake a baku labari.

Wannan tataccen saƙonni ne masu daɗin gaske da ratsa zuciya wanda aka fassara su daga ƙundin shahararren malami kuma sufi wanna ake kiransa Sayyadi Rumi wanda sunansa shine Jalāl ad-Dīn Muhammad Rūmī. Sayyadi Rumi ya shahara sosai ba ma a ƙasar Larabawa ba kawai, harma da ƙasashen yamma wato turai da ƙasashen africa musamman ƙasashen africa ta yamma da ta arewa.

Kalli Bidiyon Kai Tsaye Cikin Hotuna...

Wanda Yusufuddeen A. Yusuf ya gabatar, lallai kada ku bari a baku labari.

Idan kana da matsala a Soyayya musamman wajen tura Saƙonnin Soyayya, kasani wannan KUNDIN SAKONNIN SOYAYYA zai nishaɗantar da kai ya kuma ƙara tasirin soyayya a farfajiyar zuciyar Ka.

Karanta kaɗan daga cikin Saƙonnin Soyayyar da suke cikin wannan Audio:

MASARAUTAR KI

Ke ce Sarauniya acikin masarautar zuciyata! Gani gareki, hadimi a gareki, a cikin masarautarki, babu abinda nake ƙauna sai umurnin Ki da hidimta miki a gareki. A koda yaushe ina nan a gareki da’iman abadan!

MUHIMMANCI

Wata rana zaki tambaye Ni, wanne abu ne yafi muhimmanci a gare Ni? rayuwar Ki ko rayuwa ta?? Masoyiyata Ni kuma zan amsa miki da cewa rayuwata tafi muhimmanci a gare Ni, a wannan lokaci zaki nisanta da Ni, zaki guje Ni, zaki rabu da Ni, alhalin baki fahimci cewa Ke ce rayuwa ta ba, Ke ce mafi muhimmanci a gare Ni, idan babu Ke babu rayuwa ta.

SO DA KAUNA

Ni ba mai Dukiya bane, ba Attajiri bane, ba ɗan kowa bane, Asalina ba koman komai bane, idan kyau kike nema bana tunanin zanyi miki, idan kuɗi kike So lallai Ni ba wajen samun su bane, idan ɗaukaka ce bana tunanin na taka ko shingenta, SO DA ƘAUNA Idan shi kike biɗa zan baki babu wani haufi.

TARKO

Masoyiyata na faɗa tarkon ƙaunar Ki a lokacin dana fara ganin Ki a cikin mafarkina, Soyayyar Ki ta kasance cikakkiyar Aljannar Duniyata! Mun kasance tamkar wasu tattabaru masu shawagin ƙauna a sararin samaniya! Ni ne jarumi, mayaƙin da zai ƙwaci ‘yancin soyayyar mu, zamu tashi sama cikin soyayya har mu wuce gajimare da taurari, Masoyiyata zan kasance miki tamkar wani bango kuma shamaki da zai tsareki daga dukkan cutarwa.

MURMUSHI

Tauraruwar Zuciyata, Kin shigo cikin rayuwata! Kin cikata da farin ciki, walwala da jin daɗi, Kin cire min raɗaɗin zuciyata tamkar naki, Kin bani ƙauna da soyayya da babu mai iya bani. Ke ce tubali na da babu Ke da na faɗi war-was! Murmushinki shine sinadarin Ci gaban rayuwata. Babu wani abu mai kyawun kallo kamar murmushin da ke fuskarki a duk lokacin da muke tare.

DA SAURAN SAKONNIN SOYAYYA MASU RATSA SASSAN ZUCIYA

Wato tsayawa bayyana abinda wannan Saƙonnin Soyayya su ƙunsa kamar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke Audio na Kundin Sakonnin Soyayya yanzu a kyauta domin sauraro.

SAUKE AUDIO ANAN

KADA KU SAKE A BAKU LABARI

Ku Ci gaba da kasancewa da mu , domin samun Labarin Soyayya ko Kalaman Soyayya cikin Audio (Wanda zai sauƙaƙa matuƙa wajen sauraro koda kuwa kana cikin Uziri ne) ko kuma Video (Wanda za a iya Kalla gami da Sauraro).

Dafatan KUNDIN SAKONNIN SOYAYYA zai Ilimantar ya kuma Faɗakar da al'umma, musamman masoya (Samari da 'Yam Mata).

Sauke Zafafan Kalaman Soyayya Guda 32 Masu Ratsa Zukatan Masoya na Zamani

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za ayi sauraro lafiya cikin Nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user