Tuesday 13 October 2020

Karanta Manyan Siffofin Karuwai Da Rayuwar Su Cikin Sirri (1)

Tura Wannan Zuwa

Karuwanci tsohowar sana'ace ta iskanci da lalata wanda ya shafe shekaru masu yawa yana wanzuwa a duniya, mace ta mayar da farjinta gurin neman kuɗi, ta guje wa yin aure tana karuwanci a gida, ko ta tare a gidan haya tana sana'ar ta na karuwanci, ko matar aure mai cin amanar mijinta tana karuwanci.


Rayuwar Karuwai Cikin Sirri


Marubuci:- Datti Assalafy


Abubuwa da yawa ke jefa mata sana'ar karuwanci suna da yawa, amma manya daga cikinsu shine rashin tsoron Allah da rashin tawakkali, wasu saboda talauci da rashin haƙuri, auren dole, buri da kwaɗayin abin duniya, rashin sanin hatsari da ƙarshen makomar duk wata karuwa ko mazinaciya.


Rayuwar karuwa cikin sirri rayuwa ne na takaici, rayuwa ne na ƙazanta, rayuwa ne na cututtuka, rayuwane na rashin kunya da rashin imani, rayuwa ne na rashin daraja da rashin albarka, kuma rayuwa ne na ƙasƙanci da wulaƙanci, rayuwa ne na tsadar rayuwa, rayuwa ne na tsageranci walau ga karuwan da take karuwanci a gaban iyayenta, gidan mijinta ko karuwan da take karuwanci a gidan haya ko gidan da ta gina tana zaman kanta.


Duk wata karuwa mai zaman kanta kullum a cikin takaici da ɓacin rai take, hankalinta yana ga kwastomomi, duk wanda yazo ƙazami ne ko mai tsabta zata bashi jikinta indai yana da kuɗi, ga rashin daraja, alade ma yafi karuwa daraja, mai son tabbatar da wannan ya lura da yadda ake yiwa karuwa idan ta mutu a gidan karuwai.


Karuwa kullun a cikin tsadar rayuwa take, kuɗin da take samu baya mata albarka, saboda kuɗi ne da aka sameshi ta ƙazamiyar hanya, kullum a cikin sayan sutura da mayukan shafawa masu tsada take domin ta yiwa jikinta kwalliyar da zata janyo hankalin kwastomomi, duk wata karuwa ɓarauniya ce kuma maƙaryaciya, karuwa tana samun dama zatayi sata, ga ƙarya kamar aljana, zaku ga karuwai yanzu sunci gaba suna yaɗa hotunansu har a kafafen sada zumunta suna ƙarya da damfara, yanzu sun ɗan samu sauƙi saboda application na ado da kwalliya da suka bayyana a playstore.


Karuwa kullum a cikin jinya da cuta take, babu wata karuwan da take da lafiya kowacece ita, kuma karuwa ta fi komai da kowa yaɗa cuta mai hatsari ga lafiyar mutane, da zaran karuwa ta lura da lokacin jinin al'ada na zuwa mata sai tasha kwayoyin da zai hanata jini, wanda hakan cutarwa ne ga lafiyar jikinta, dole karuwa mai zaman kanta zata dakatar da jinin al'ada don tayi karuwanci ta samu kuɗin sayen abinci da biyan haya.


Daga cikin cuta da karuwai ke haifarwa kanta shine: Allah cikin hikimarSa bai halicci jikin mace don ta dinga karɓan miniyya daga maza mabanbanta ba a lokaci guda, sai dai ga namiji shi kaɗai, macen da maza da yawa suke jima'i da ita a tsakanin kwanuka ko a lokaci guda suna zuba mata miniyya yana bin jikinta; to hatsari ne ga lafiyarta, wannan bincike ne da ilmin Likitancin zamani ya tabbatar.


Na daga cikin dalilan da ya sa Allah Maɗaukakin Sarki yace mace ta auri namiji ɗaya, ba kamar yadda Allah Ya bawa maza damar auren mata har huɗu don ya rayu da su a lokaci guda ba, idan ya kasance mace zata auri maza biyu na farko za'a iya samun saɓani tsakanin mazajenta idan ciki ya shiga, na biyu miniyyinsu da yake shiga jikinta a lokaci guda illa ne ga lafiyar jikinta, wanda masana ilmin kiwon lafiya suka gano hakan.


Yanzu karuwai ɗin sunci gaba, suna da kayan gwajin cutar ƙanjamau, kwastoma na zuwa zata gwadashi idan yana son yin jima'i fata da fata (skin to skin), wanda ba sai mazinacin ya sa kwaroron roba ba, amma wannan karuwan tana da tsada, karuwai ɗin kuɗi-kuɗi ne kuma mataki-mataki, mafi rashin darajar karuwanci itace karuwan Naira 200 a yanzu, wannan ga wanda ta kusa zama guzumar karuwai kenan, cututtuka sun mata yawa a jika, tana neman abokin tafiya lahira.


DUBA WANNANKaranta Manyan Siffofin Karuwai Da Rayuwar Su Cikin Sirri (2)


Wanzuwar karuwai a cikin al'ummah ya taimaka wajen lalata tarbiyya da ƙaruwar munanan laifuka da ta'addanci, gidajen karuwai da manyan hotels da ake karuwanci ya zama babbar mafaka ga tsageru, jami'an tsaro sunsha bin diddigin manyan ɓarayi da masu garkuwa da mutane suna kamasu a gidajen karuwa da kuma hotel.


Zan cigaba a rubuta na gaba, zan shiga daku gidan karuwai, hotel  ɗakin karuwa kuji abinda yake wakana idan mazinaci yazo zaiyi zina da kuma bayan ya gama zina, zan kawo muku labarin wasu cases na karuwai da kashe-kashen da sukayi a junansu.


Zamu Ci gaba Insha Allah.


Allah Ka shiryar da karuwai mata da maza, Ka tsare al'ummar Musulmi daga sharrinsu Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user