Thursday 17 December 2020

Karanta Manyan Siffofin Karuwai Da Rayuwar Su Cikin Sirri (2)

Tura Wannan Zuwa Ga

Mai karatu kayi haƙuri da wasu kalmomi masu nauyi da zaka karanta cikin wannan rubutu na Datti  Assalafiy, idan buƙata ta kama domin a fahimtar da mutane musamman ga waɗanda basu da cikakkiyar fahimta na kalmomi to dole sai an fito da kalmomin a zahiri don a fahimta.


RAYUWAR KARUWAI

Marubuci:- Datti Assalafy


Ita dai Karuwa jakar gayu ce, duk wata karuwa jaka ce, domin yadda jakuna suke taruwa a kan jakanya guda suna jima'i da ita haka karuwa take, zaka samu akwai karuwa guda ɗaya da tayi jima'i da maza sama da dubu a rayuwarta, cutuka sun mata katututu a jikinta, idan ka tambayeta zatace ita rayuwar duniyar sam baya mata daɗi.


Rayuwar karuwai abin ƙyama ne, kuma rayuwa ne na ƙazanta, duk wanka da duk adon da karuwa zatayi ƙazamiya ce sai kaji tana wari da ƙarni, kuma yawanci karuwai ba sa yin wanka sai dai kwaskwarima sakamon cuɗanya da take da mazaje mabanbanta, wato warin da karuwa keyi yana bi har jinin jikinta, da kuma kasancewar miniyyi na mazaje mabanbanta dake shiga cikinta, shi yake haddasa mata irin wannan warin.


Karuwa bata da kunya, duk wani abu na rashin kunya da rashin mutunci karuwa zata iya aikatawa, duk wani marar kunya bashi da imani da faɗin Manzon Allah (S.A.W) imani bai zama a jikin mutumin da bai da kunya, hakanan kunya bai zama a inda babu imani, imani da kunya a haɗe suke, idan anaso ayi ma wani mutumin kirki sharri sai an haɗa da karuwa, na san wani Limamin Masallaci da aka shirya masa tuggu da wata karuwa, idan ya fito da asuba zai je masallaci ta rungumeshi ta sa ihu, da ƙyar Allah ya kubutar da limamin.


Karuwa kamar akuya take, dole tayi yawo tsirara domin ta janyo hankalin mazinata, dole ta sayi kaya masu bayyana tsiraici taje daƙin hoto a ɗauke ta a hoto ayi mata kwalliya a Photoshop Application wanda zata dinga ɗaurawa a kafofin sada zumunta na yanar gizo domin ta nemi kwastoma da abokan zina, kunga ta zama akuya.


Karuwa ƙazama ce, bata wanka, kun san yanayin jima'i musamman a lokacin zafi, ana yin zufa sosai idan ana yin jima'i, zufan jikin mutum yana ɗauke da cutuka, ko a binciken Likitanci ana so da zaran an kammala jima'i aje ayi tsarki da kuma wanka, amma karuwa bata wannan, zata share farjinta da tsumma ne, wani na waje yana jira, na ciki na fitowa na waje zai shiga ya ɗaura, kuma dole fatar jikinsu ya haɗu ko da sun sa kororon roba, anan zai kwaso cuta yaje ya yaɗawa iyalinshi ko abokanshi, shiyasa taɓa jikin mazinaci bai dace ba, domin zai iya yaɗa cuta da ya ɗauko daga jikin karuwa.


Karuwa kullun a cikin rayuwar takuri take da kuma ƙunci, shiga cikin ɗakin karuwa ka gani, ɗakine ɗan ƙarami tsukakke sai wari da hamami duk da ta kunna turaren wuta, zagaya gurin da suke wanka, babu wani tsayayyen toilet, idan wanka zatayi haka nan zata tsaya daga bakin ɗakinta ta watsa ruwa, ko bawali zatayi sai dai tayi a cikin baƙin leda a cikin ɗakinta ta goge da tsumma ta jefar a kwalbati, idan fitsari zatayi sai dai tayi a cikin bokiti ta fita waje ta watsar, haka mazinaci zai zo ya yabi guntun kashi da fitsari a jikin karuwa.


Ina mazinata masu zuwa gidan karuwai suna zina? Ku sani cewa yanzu matsafa suna amfani da maƙudan kuɗaɗe suna sayen miniyyin mazinata daga hannun karuwai suna tsafi da shi, wato maniyyin da aka zuba a cikin kororon roba, wanda idan mazinaci ya gama zina da karuwa zata cire ta saka a bokiti, da zaran an tafi da maniyyinka kamar sun tafi da ruhinka ne, za'ayi tsafi da kai a bayar da rayuwarka wa baƙaƙen aljanu, ko su nakasa rayuwarka, ko kuma su rabaka da duniya, wannan sabon abune da ya bayyana.


Mai son sanin wasu daga cikin sirrukan 'yan Luwaɗi ya je yayi hira da karuwai masu zaman kansu, musamman magajiyar karuwai, nemi kuɗi kayi mata kyauta zata lissafa maka manyan mutane a garinku waɗanda suke 'yan Luwaɗi, domin yanzu karuwan da tafi sauran karuwai kawo kuɗi itace karuwan da ake Luwaɗi da ita, akwai mazan da a yanzu ba suna zina da karuwai ta farjin su bane, haka nan ba suna auren mace don jima'i da ita ta farji ba, sai dai ta dubura.


Jama'a ku dena ganin waɗannan manyan 'yan mata 'yan boko masu zaman kansu a Abuja da sauran manyan birane suna sayan manyan gidaje masu tsada, suna hawa mota masu tsada, suna hawa jirgin sama su ɗauki hotuna suna fita ƙasashen waje suna yiwa mutane kallon ƙasƙanci da wulaƙanci, suna kafa kungiyoyin tallafawa marayu suna alfahari dashi don su yaudari al'ummah, wallahi yawancinsu riƙaƙƙun karuwai ne da ake Luwaɗi da su, domin yanzu fa zina bai kawo kuɗi sosai sai Luwaɗi.


To ƙarshen duk wata karuwa cutar kansa ne mai kisa, saboda irin mayukan shafawa da sabulun wanka masu ɗauke da sinadari da suke amfani da shi, da kuma miyagun ƙwayoyin da suke sha, anan cutar kansa zata kamasu, ba zai rabu da su ba sai sun mutu.


DUBA WANNAN: Karanta Manyan Siffofin Karuwai Da Rayuwar Su Cikin Sirri (3)


Don haka rayuwar  karuwa sam ba abin burgewa bane, kuma ba abin sha'awa bane, domin ƙarshen duk wata karuwa mai zaman kanta, ko wanda take gidan iyayenta, ko wanda take gidan kanta shine yin mummunan ƙarshe na wulaƙanci.


Ina muku albishir da wani rubutu da zan wallafa mai taken MUMMUNAR MANUFAR YAHUDAWA AKAN MATA rubutune mai matuƙar fa'idah, kada ku bari a baku labari.


Ina roƙon Allah Ya kare matan Musulmi daga faɗawa harkan karuwanci, Allah Ka tsaremu Ka tsare mana imanin mu Amin.


Zamu Ci gaba Insha Allah.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user