Saturday 31 July 2021

Sauke Wakokin Alkhairi EP Album Na Hamisu Breaker A Kyauta

Tura Wannan Zuwa

Kamar Yadda Shafin MuryarHausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku sababbin Waƙoƙin Soyayya har ma dana Siyasa Yau ma gamu tafe da waƙoƙin  Soyayya na ƙundin waƙoƙin Alkhairi EP.


Ƙundin Waƙoƙin Alkhairi EP

Muryar Hausa24 yau ma gamu ɗauke da  sabon ƙundin wakokin  fitaccen mawakin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood wato Hamisu Sa'id Yusuf (Hamisu Breaker) .

Idan ba za ku manta ba a baya mawaƙin ya saki ƙundin waƙoƙin shi na Dalilin So, wanda a sanadin fitar wannan ƙundin ya janyo ra'ayoyin jama'a da dama suka fara son waƙoƙin shi.

Bangon ƙundin waƙoƙin Alkhairi EP

Bayan shafe tsawon lokaci yana yin aikin wannan ƙundin don ɗebe muku kewa da ƙoƙarin faranta muku rai, mawaƙin ya saki ƙundin waƙoƙin shi mai suna Alkhairi EP.


Bangon ƙundin waƙoƙin Alkhairi EP

An shirya wannan ƙundin domin ya tayaku nishaɗi, mawaƙin kuma ya yi matuƙar ƙoƙari wajen sanya muku irin abubuwan da suka fi dacewa da ku.

Ƙundin Waƙoƙin Alkhairi EP

Wato tsayawa bayyana abin da wannan ƙundin waƙoƙin ya ƙunsa tamkar ɓata lokaci ne, abin sai wanda ya saurara.

Kardai mu cika ku da surutu ku hanzarta sauke waɗannan waƙoƙin yanzu domin sauraro;


1. Manyan Mata


2. Assalamu Alaiki


3. Habibty

4. Soyayya5. Ki bani Dama
6. Na fara Soyayya7. Muradin Zuciya8. Gimbiya9. So Gaskiya Ne10. Sirrina11. Kada Ki Barni


12. Da Ni da Ke13. Sarauniya ta ɓoye

14. Jinin Jikina


Garaɓasar waƙa guda ɗaya


1. Ɗan DakoJerin sunayen waɗanda suka taimaka wajen shirya wannan ƙundi har ya samu damar iso wa zuwa gare ku, gami da tace sautin kiɗa da na murya;

1. Kasheepu
2. Prince na Kasheep
3. Zaharadden Amjad
4. Naziru mai Atamfa
5. Abdul Ziro
6. Isma'il Guiter
7. Midget Mix

Domin samun sababbin wakokin siyasa, wakokin Soyayya, wakokin bege, wakokin gargajiya da sauran su akan lokaci ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng farin cikin ku shine farin cikin mu.

Zaku iya sauke sababbin wakokin Hamisu Breaker harma da tsofaffin wakokin Hamisu Breaker a kyauta idan ku latsa rariyar liƙau ɗin dake ƙasa.

SABABBIN WAKOKIN HAMISU BREAKER

Ku Ci gaba da kasancewa da Mu domin samun Cikakken Tarihin Hamisu Breaker nan bada daɗewa ba Insha Allah.

MURYAR HAUSA24 Muna fatan za a yi sauraro lafiya cikin nishaɗi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user