Sunday 1 August 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (37) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa

MATAKI WANI IRI?


Kar ka taɓa cewa sai ka samu komai ɗari bisa ɗari ko ka ɗauki mataki, ka dubi kanka ka gani, ba komai kake yinsa yadda kake so ba, wani sa'in da kanka za ka gane ba daidai kake tafiya ba bayan ka gajiyar da kanka, akwai wanda ya fara sana'a ko shekara bai yi ba ya ce ya ga kamar ba zai kai labari ba sai ya canja, kafin shekaru biyar ya yi sana'o'i kusan takwas, cikinsu ba ko guda ɗaya ƙwaƙƙwara, na ce ya yi gaggawa, ko kogi da kake ganinsa cike da ruwa da yayyafi ya taru.


Ɗaukar Mataki


MarubuciBaban Manar Alkasim


Banda wannan ma mutum ya leƙa irin rijiyoyimmu na dauri waɗanda aka yi musu tsarin kwakware zai ga cewa igiyar da ake jan ruwan a hankali ta ci kututturen ta raba shi biyu, har ta kai ga ƙarfen, shi ma ta yi masa illa tana ƙoƙarin raba shi biyun, kai ma ka san ba aikin kwana ɗaya ne ko biyu ba, yau da kullum kenan, mutum bai gaza ba idan ya zaɓi aikin da yake ganin zai iya yi a hankali, har ya kai ga inda yake so, in ma bai kammala ba ne ya yi ƙoƙari ya samu matsaya, duk lokacin da ya dawo ɗorawa kawai zai yi daga inda ya tsaya, ba komawa baya zai yi ba.


Muna maganar cin nasara ne a duk ɓangarori na rayuwa, wata rana wani bawan Allah ya sami matsala da matarsa a gidan haya, sai ya yi ƙoƙarin sakin matar, har ya ce mata ta tafi gidansu zai zo ya same ta, to Allah ya sa maigidan bai riga ya fita ba, matarsa ta gaya masa cewa mai haya a gidansu fa yana ƙoƙarin sakin matarsa a kan kaza da kaza, sai maigidan ya kira shi ɗakinsa ya tambaye shi ko ya san ranar da ya yi aure?  Yaron ya amsa cewa bai sani ba, sai ya ce masa "Shekara kaza kenan tun baka yi wayau ba, matarka ba ta wuce sa'ar ɗiyata ta uku ba, amma wallahi har yanzu fama nake da ita".


Ya ce "To ka taɓa jin na ce zan sake ta?" Yaron ya girgiza kai wato a'a, ya ce "To haka kowa ka gani yana zaune lafiya da matarsa haƙuri ya fi ka, ba wai tsabar zaman lafiya ne ya kawo haka ba, in bai yi haƙuri ba a ƙarshe sakinta zai yi, ya koma ya sake auro wata macen, sai ka ji ana yi wa mutum lissafin yawan matan da ya saka, wani mai gidan hayan ko yaushe yana cikin korar mazauna gidansa ne, haka wasu masu wuraren sana'a, yau in ka ga wannan gobe ka ga wani daban, wai yaran ba su da kyawawan ɗabi'u, wani kuma mota ce a gabansa, da wahala ya shekara da mota guda, kar ka yi zaton duk in ya rabu da motar zai kawo wace ta fi ta baya ne, wani sa'in gwara jiya da yau.


Wanda ya fi ban takaici ma ƙananan yara 'yan makaranta, yau ka gansu a wannan makarantar gobe a wata, a kullum cikin kai kuka ne, yaran sun kasa samun makaranta ɗaya da za su yi karatu, ba wai yara ba hatta manyan, zan ba ka misali: Wata rana ina zaune a aji sai ga wata mata ta zo koyon Larabci take ce min ta shiga makarantu da dama, wasu da ta lissafo sun fi ƙarfin makarantarmu, saboda sanin malaman da suke koyarwa a ciki, amma na karɓe ta duk da haka, sai ya kasance ba kullum take zuwa ba, in ta zo wannan makon ƙarshe wani makon za ta gaya maka cewa tana da sha'ani a wani ƙauyen, wata ƙila ma ba za ka gan ta ba sam-sam sai bayan mako biyu, ta ya mutum zai iya harshen bayan bai mai da hankali ya koya ba?


Can sai na ji wata na ba da labari wai wannan matar na surutu a wani wuri tana cewa ba wani bambanci tsakanimmu da saura, ta ce ga shi ta haɗa shekara ko kyakkyawar jumula ta Larabci ba ta iya haɗawa ba, amma kuma ba ta sheda musu cewa matsalar daga wurinta take ba, galibin matsalolinmu da za mu yi haƙuri mu bi tsari da komai ya yi kyau, na ga yarinyar da aka maimaita mata aji, amma uwarta ta saɓa gyale ta zo wurin malamar ajin ta gaya mata cewa ɗiyarta na da ƙoƙari ba wani dalilin da zai sa a koma da ita baya, duk bayanin da malamar ta so ta yi mata ta ƙi fahimta, haka dole aka kai yarinyar gaba kuma ba abinda take fahimta, uwarta ta ja mata.


Wani abokin karatuna da muke ɗaki guda a wata ƙasa ya gano cewa yarinyar da aka damƙa masa a hannunsa amana ba ta kwana a gida, kullum tana wurin samari, karatun ma ta bari ko an kore ta, haka ya kira ubanta ya gaya masa gaskiyar abin da yake faruwa, lokacin da uban ya gaya wa mahaifiyar a nan cibi ya zama ƙari, ta kira abokin karatun nawa ta wanke shi tas wai ya yi wa ɗiyarta sharri, a ƙarshe ma ta zo ƙasar ta ce ya cire hannunsa a kan ɗiyarta kar ya ƙara sanya baki a kan abinda ba a saka shi ba, anan kam ba ta taimaki ɗiyarta ba.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (38) Cikin Sauki


Duk irin waɗannan abubuwa in za a duba su da idon basira sai ka ga an yi aiki da rashin lissafi wurin neman nasara, kamar maza ne tare da iyalinsu, ga su mazaje ne amma ba mazaƙuta, kamar dai yadda matan suke faɗi, sai dai ka ji ana tambayarsu "Har ka zo ne" shi kuma ya ɓata rai, in ya ji abin ya yi yawa ya fara neman maganin mazaƙuta, a maimakon ya ga likita, da yawan maza ba su da ƙarfi a kan ƙaramar cutar da za a iya magance ta, wallahi wasu amosani ne ya riƙe mararsu, ko maɓuɓɓugar maniyyinsu, in an ba su shawarar su ga likita don ba sa jin zafi sai su ce maka su lafiyarsu lau, bayan ba lafiyar, shi ma wannan mummunan ɗaukar mataki ne.


Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user