Thursday 28 October 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (40) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

3) SANIN MAKAMA GA MANYAN KAMFANONI


Akan samu manyan kamfanoni da ke juya lamuran kasuwanci, sukan tsayu da gindinsu ne wurin kawo sabbin kaya da sabbin tsare-tsare, 'yan canje-canjen da ake samu na ƙirƙirar sabbin kaya kan samu ne a dalilin ƙalu-ɓale na kasuwanci da riƙe sana'a, dole a sami sabbin mabuƙata, a kutsa cikin gasa ta ƙirƙiro kaya ko ƙara musu ƙawa ko ƙarko, ko sassauta wa al'umma don kiran mabuƙata.


Sanin Makama Ga Manyan Kamfanoni

MarubuciBaban Manar Alkasim


Wannan aiki da kamfanoni za su yi sayar da rai ne bai yuwuwa a yi shi ido-rufe, ana buƙatar masana makaman sana'a da za su ƙimanta komai, kasuwar ita kanta, da kayan da za a ƙirƙiro da kuɗin da za a narka, da wanda za a dawo da shi in har mutane suka karɓe shi.


4) A TSAKANKANIN AL'UMMA


Wannan akan ƙirƙiro kaya ne don amfanin al'umma a matattara don warware matsaloli ba tare da tunanin riba ko abinda za a samu ba, ko wannan ɗin sai an bi wasu matakai, don ba dole ne al'ummar ta amfana ba, kodai ta ƙyamaci kayan saboda wani dalili aka soki kayan da shi, ko wasu su yi awon gaba da shi kafin ya kai hannun al'umma, dole masana su shigo tsakiya.


BAMBANCIN MAI SANIN MAKAMA DA ƊAN KASUWA


Waɗannan mutane ne mabambanta, amma kuskure kan sa mu ɗauka mutum guda ne, ɗan kasuwa dai ya san hanyarsa da yake bi kullum don isa ga manufofinsa, bai da buƙatar wani tsari ko tunani na daban shi kuwa mai neman sanin makama zato yake yi na cewa in ya bi wannan hanyar zai sami alkhairi saboda wani abu da yake zato ko yake gani da idanunsa, kenan ɗan kasuwa yana da iliminsa da komai tun farko, mai neman sanin makama kuwa yanzu za a fara sana'ar, mai dabara shi yake jewa ya sami tsaffin hannu na masu sana'a ya zauna da su ya koya, a ƙarshe shi ma zai zama ƙwararren.


DAN KASUWA


Ɗan kasuwa shi ne mutumin da yake gudanar da kasuwancinsa ko ya kama wata sana'arsa wacce tsohuwar hanya ce tun dauri yake gudanar da lamuransa, a kullum tunaninsa shi ne wacce hanya zai bi don haɓɓaka lamuransa kasuwanci ne ko sana'ar hannu? Anan akan ɗan sami gasa gami da ƙalubale domin akwai 'yan kasuwa ko masu sana'a irinsa, duk yadda ya bambanta da tsararrakinsa bambancin zai iya taimaka masa wurin janyo hankalin mabuƙata, kamar faɗaɗa shago, gyara shi, cika kaya kala daban-daban, kawo sabbin kaya ko sauƙaƙe farashi, in mai sana'a ne kuma ƙawata wurin, yi wa mutane aikinsu kan lokaci, samar da kyau gami da ƙarko, riƙe gaskiya da sauƙaƙa musu, ko kyakkyawar mu'amala, duk yadda mutum ya ɗan yi ƙoƙarin bambanta kansa da sauran zai iya samun alkhairi.


Akwai ƙarancin tsoron faɗuwa ga ɗan kasuwa don da ma sana'arsa ce da ita yake rayuwa, ya san inda ake samo kayan da yadda ake shigar da ita da inda mabuƙatanta suke, in kuma sana'ar hannu ce to da ma yana da mabuƙatansa, ko bai fito ba za su buga masa waya, akwai waɗanda suka fi shi komai amma ƙila bai tsawwalawa ko bai da ƙyuya, ko kuma gaskiyarsa ta taimaka masa, in har zai canja sana'a ba zai yi saurin sakin na hannu ba, misali bakaniken dake gyaran mashinan haya, wanda yake son komawa roba-roba saboda gasar da ta yi yawa a sana'ar farko, dole ya riƙa yi wa mabuƙata bayanin faɗaɗa sana'ar amma ba zai saki ta farko ba, sai dai ya haɗa biyu har masu roba-roban su gano shi, in ya ga ya karɓu sannan yana iya sakin sana'ar farko ta yi tafiyarta.


Haka ma telan maza, in ya yi tunanin komawa ɗunkin mata, gaskiya ba su san yana yi ba, ba su san gwanancewarsa da sauƙin da yake da shi ba, kafin su san shi zai ɗauki lokaci to kar ya saki sana'ar farko, ba laifi ya haɗa hannu da wani telan mata ya ɗan riƙa turo masa aiki in ya yi masa yawa, sai ya rage kuɗin da zai riƙa ɗunkawa don dai alaƙar ta ɗore, haka macen da ta yi fice a koko da ƙosan safiya, in ta ga za ta koma na yamma musamman a ranakun Litini da Alhamis don ta sami damar kawo sabuwar sana'a da safe kamar waina, duk da haka ta riƙe sana'ar farko ta riƙa yi wa mabuƙatanta bayanin ci-gaban da aka samu, kar ta katse rana tsaka.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (41) Cikin Sauki


2) Mai neman sanin makama kamar yadda muka gani a baya mutum ne da ke ƙoƙarin fara wata sabuwar sana'ar, ko sabon tsari da ya bambanta gaba ɗaya da wanda yake tafiya a kai, wannan akwai abubuwa da dama a kansa don dole sai ya hau gadar kasada, jarinsa zai girgiza, kuma zai iya rabuwa da tsaffin mabuƙatan tsohuwar sana'arsa ga sabbin ba su riga sun shiga hannu ba, ya tabbatar da cewa tsarin da yake da shi a hannu zai iya maido masa da jarinsa, kuma ya sami sabbin abokan hulɗa, shi yanzu yana matakin kashe abin hannunsa ne da burin cewa za su dawo cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ƙila ma su fi na da.


Za mu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin

aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user