Wednesday 3 November 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (41) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

WASU SIFOFIN SANIN MAKAMA


Ba duk wanda ya bi layin sanin makaman sana'a ake la'akari da shi a kan cewa ya ci nasara ba, zai yi kyau dai a san wasu 'yan sifofi da za su taimaka wa mai son kama sana'a ko canjawa daga wata zuwa wata: -


Hoto: Ilearnlot

Wasu Siffofin Sanin Makama

MarubuciBaban Manar Alkasim


1) Iya sayar da rai: Kamar ya? To kuɗinka da ke hannunka za ka zuba, ba ka san yadda za ta kasance ba, za ka kama hayar shago, za ka saro kaya, za ka ba da lokacinka gaba ɗaya sai yadda ta kasance, wannan in ma kasuwanci ne a ganina ya fi sauƙi, sana'ar hannu ta fi wahala a farkon farawa, don wata sana'ar sai ka biya, kuma ba ko sisin kwabo da za ka samu, duk abinda ka yi aiki aka samu maigidanka zai kwashe.


Wannan zai ɗauki lokaci sosai kafin ka gwanance ka fara samun ɗan na jefawa a bakin salati, in ka iya ɗin kuma aka yaye ka za ka yi naka shi ma wasu matsalolin ne, ƙila sai ka haɗa da bashi kafin ka sami hayar inda za ka kafa naka, kana buƙatar kayan aiki na zamani wanda za su jawo hankalin mabuƙata a matsayinka na mai buɗe sabon wuri, mutane na buƙatar ganin abinda ba su saba gani ba a inda suke zuwa a baya, ka ga rancen kuɗi ko narka wanda yake hannunka a wannan mataki sayar da rai ne, don ba ka sani ba ko su fito ko su nutse, shi kuma wannan matsayi da ake ciki dole ka ƙawata wurinka ko mutane su yi maka ƙaura, da ma can ba ka riga ka same su a hannu ba tukun.


2) ƙirƙirar sabbin abubuwa: In dai za ka zo wa mutane da abinda suka saba ne to ba dalilin da zai kawo su wurinka, ka lura in kana da shago 'yar naira uku (₦3) da za ka rage wa mace za ta iya tafiya mai nisa ta zo wurinka ta sayi kaya, a lissafinta ba za a cuce ta ba, in wurin sana'a ne ka ƙawata shi ka kawo sabbin kayan aiki na zamani, ka sanya wuta isasshiya kala-kala mai ɗaukar ido za su taimaka wurin kira maka mabuƙata, to bare kuma a ce ka yi mu'amala kuma ka iya aiki, na taɓa zuwa scanning da iyalina na ji tana yaba wa likitan kan ya san aikinsa, na tambaye ta yadda ta sani ta ce ba wani abu da take ji wanda bai tambaye ta ba, na ce gaskiya ne maganar ta wuce.


In za ka fara sana'a dole ka tabbatar mutanen wurin na buƙatarka, wani mai yi min aski ya faɗa min cewa zai buɗe wani shago a wani ƙauye, na tambaye shi dalili sai ya ce mutanen ƙauyen na shan wahalar zuwa gari aski. Na ce ba masu aski ne a can? Ya ce ba sa yin na zamani, kuma ya je ƙauyen ya lura ba wani shagon aski da aka ƙawata shi a matsayin na zamani, mutane na san tsafta da wayewa, ya ce zai fara tattaunawa da waɗanda suke shigowa don ganin yadda zai ci nasara a harkar, ina jin haka na san ya san abinda yake yi, ba sabon shiga ba ne, ya san dalilin da ya sa yake son buɗe shagon a can, ya fara bin hanyoyin da zai sami mabuƙata tun kafin ya samu shago ko ya kashe kuɗi wurin sayen kayan aiki.


Ko shago za ka buɗe ka yi ƙoƙarin sanin abubuwan da mutanen wurin suke buƙata, in za ka ƙara wani abu to ka tabbatar ka ɗaure shi da abinda dole mutane za su zo wurinka a dalilinsa. Wani ya taba yi min kukan cewa katin wayan da yake sayarwa ba riba ko kaɗan, na ce to ya bari mana ya kama wanda zai sami nasa a ciki, sai ya ce "Ai wasu kayayyakin shagon suna samun shiga ne a dalilin katin, sai ya buga misali da ni, kati na zo saya amma na sayi kayan ƙwalaman yara da buredi a dalilin rashin canji, koda mutum bai samun riba a wasu kaya, in dai za su iya kawo masa mabuƙatan da za su sayi wasu kayan to ya zama dole mutum ya ci gaba da saro wannan, koda kuwa faɗuwa yake yi a ciki, don zai auna alfanun da yake kawowa ne.


3) Iya ƙimantawa da kintatawa: Ga mai fara sana'a dole ya zama mai iya ƙimanta abu da kintata yadda zai kasance koda kuwa bai yi makaranta ba, na taɓa ba wani ɗan kasuwa shawarar ya saro hatsi da yawa musamman yadda ake buƙatarsa yanzu ga shi ƙara tsada yake yi, sai ya ce zai saro amma ba da yawa ba, na tambayi dalili sai ya ce sabbin makani, doya da rogo sun fara fitowa, domin nan gaba kaɗan za su cika kasuwa, mutane za su koma musu, in suka yi sauƙi, wurin abincin rana da na dare, wannan zai sa kasuwar hatsi ta ɗan ja da baya kaɗan, kafin ta gyagije ta komo hayyacinta sabon hatsi ya shigo, sauƙin da yake da shi kuma zai sa a koma masa, dole sai mutum ya yi a hankali, kai da jin maganarsa ka san ba ido rufe yake sana'ar ba.


Akwai nau'o'in sana'o'in da ba zai yuwu a yi su a wasu wuraren ba, kodai don mutanen wurin ba su buƙatarsu, ko kuma ba su ƙimanta su yadda ya dace, wani ya nemi mu buɗe wata makaranta irin ta share fagen jami'annan a ƙauyensu, musamman yadda babu ko ƙwara ɗaya a wurin, na tambaye shi yadda suke son karatun, ya kambama abin sosai, na ce kamar nawa kake ganin za su iya biyan kuɗin makaranta ba tare da matsala ba, ya ce ko nawa ne za su biya in dai suna son karatun, amma da na bincika sai na ga wasu makarantun da suka mutu duk a kan biyan kuɗin makaranta ne, ka ga duk yadda suke son karatun, ko rashin makaranta a wurin in ba ka da jarin da za ka ɗauki nauyin malamai na tsawon shekaru kafin mutane su gane muhimmancin karatun su fara biya wannan wurin ba naka ba ne ka nemi wani wuri kawai.


DUBA WANNANKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (42) Cikin Sauki


4) Wayewa: Dole dai mutum ya shigo zamani a yi da shi, idan kai tela ne ka lura da irin ɗunkin da mutanen wurin suke so, ko kana da naka wanda kake ganin ya fi, in dai ba kai za ka saka ba to ka yi musu wanda suke so, haka kafinta mai yin kayan ɗaki, shi ma ya lura da yayi, komai ƙarƙon kaya in dai ba zai ba da sha'awa ba mata ba su cika so ba, kai ko indomie kake sayarwa matuƙar akwai wani kamfani da aka fi saye shi ya kamata ka kawo, koda kuwa samunsa da wahala, ba matsala ka tattauna da mabuƙatan ka nuna musu irin matsalar da kuma canjin da za a iya samu na farashi, in sun yarda ka kawo kaɗan a matsayin gwaji, in ka ga yana shiga sai ka riƙa kawo musu, domin su ne ƙashin bayan zamanka a wurin.


Za mu Ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user