Wednesday 10 November 2021

Karanta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (42) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

5) Bibiyar yanayi: Ɗan kasuwa da mai sana'a dole su riƙa bin duk yanayin da ake ciki, su riƙa lura da abinda mutane suke buƙata da lokacin da suke buƙatarsa. Misali: Kayan da aka fi buƙata a lokacin sanyi ka kawo shi a lokacin, waɗanda kuma lokutansu ya wuce sai ka ajiye su ka canja, ka riƙa karantar mutane da abin da suke so, in ka san mutanen wurin masu son banza ne to ka kawo musu irin kayan da za su yi daidai da su, idan ka saba sayar da kaya a ƙauye ka zo ka sami kanka a GRA dole ka karanci irin mutanen da ka shigo cikinsu, ka gano irin nau'in kayan da suka fi so ka zo musu da shi, hatta magana dole ka koyi irin wadda za ta yi daidai da su, don za ta bambanta da wacce kake yi a tasha.


Muhimmancin Sanin Makaman Sana'a Hoto: Grow.rootworks

MarubuciBaban Manar Alkasim


6) Kayan da za ka sayar: Kaya suna suka tara amma sun bambanta a kuɗi da dandano wannan kamar abinci kenan, sai kuma yawa da ƙarko. Wasu mutanen sun yarda da cewa arha ba ta ado, duk wani kaya in bai da tsada ba za su saya ba, ko makaranta za su saka yaransu suna son su ji kuɗin, in ya yi arha da yawa to ba ta yaransu ba ce, suna ƙimanta makarantar da irin tsadar da take da shi ne, za su tambaye ka kuɗin makarantarka, wasu har albashin da kake ba malaman sai sun ji kafin su saka yaransu, wasu za su je su leƙa ko'ina har banɗaki, ba ma za su tambaye ka abinda kake koyarwa ba don kuɗi ne ke yin komai. A taƙaice dai ka fara ƙimanta abinda za ka bayar tukun, bayan ka lura da irin mutanen wuri, amfanin sanin makama kenan.


MAHIMMANCIN SANIN MAKAMAN SANA'A


Sanin makaman sana'a na taimakawa sosai wurin bunƙasa irin sana'ar da mutum yake ƙoƙarin shiga, ko wanda yake ƙoƙarin komawa lura da abubuwan da za mu ambato a ƙasa: -


1) Tabbatar da aikin yi: Wannan sanin makaman yakan taimaka sosai wurin samo aiki, domin idan mutum yana sha'awar aiki kuma ya yanke zai fara ko ya fara ɗin bai nufin aikin ya dace da shi, wasu da dama sukan fara sana'ar daga baya su gudu su bar ta ko su yi ta fama da ita sakamakon rashin ɗauko ta ta fuskar da ta dace, sanin makama kan taimaka wurin goce wa hakan, ya kuma tabbatar da sana'ar mutum ta wurin samar masa da gwanancewa da dabarun tafiyar da sana'ar, da juriya kan sauyin yanayi, da iya ɓoye matsaloli don ribatar wasu abubuwa masu alfanu.


2) Ƙirƙira: Wannan bayan an tabbatar da fara sana'ar to ai ba za a rasa gasa ba, mai maƙwabtanka suke sayarwa? Idan ka samu cewa abinda mabuƙata ke buƙata duk suna sayarwa to me za ka ƙara ka bambanta da sauran? Karanci mabuƙatan sosai da yadda maƙwabtanka ke sayar musu da kaya, in ana tauye mudu kai kar ka tauye, in ana tsada kai ka sauƙaƙa, in mu'amallar da ke tsakanin mai saye da mai sayarwa ba kyau kai ka gyara taka, lura da abin da mutane ke so wanda ba a kawowa saboda bai da riba kai ka kawo, samo wasu kayan da ba a san su ba kai ka shaharantar da su, sanin makama ne ke koyar da wannan.


3) Tasirin matattara da ci-gaba: Duk matattarar da ta girma za ka tarar akwai hada-hada da yawa, kuma buƙatun kaya kan daɗa yawa, musamman wannan zamani na faɗaɗar gefen birane a dalilin hijira ta mutanen ƙauye da zaman lafiya ta wuyata a ƙauyukansu, akwai buƙatar buɗe makarantu, da ƙaruwar sana'o'in hannu wanda zai sa a hana samari zaman kashe wando, kuma su sami ababan sauƙaƙe rayuwa, ƙila ma su iya ɗaukar nauyin kansu ta fuskar rayuwa da karatun addini da na zamani, akwai sana'o'in hannu da za su sami shiga sosai yanzu yadda ake sabbin gine-gine a ko'ina ka zaga a Arewacin ƙasar nan (Najeriya), duk sana'ar da mutum ya sa a gaba zai iya samun alfanu, amma wace sana'ar za ta fi shiga a yankinka, in ka shiga za ka iya dogaro da kanka? Mai ka ke so ka zama wanda za ka riƙa sakawa a gabanka a matsayin ma'auni?


4) Daga matsayin mutum a rayuwa: Akwai wanda yake sana'a don ya sami abinda zai ci kawai, wani zai ce don ya ciyar da iyali, wani zai ƙara da cewa don ya sami abinda zai yi zumunta da shi, wani zai ce don ya bar wa yara abinda za su tsaya da kansu, wani ya ce yana so ne ya kai wane a kuɗi ko shuhura a sana'a, kowa dai a cikinsu yana aiki ne don ya isa inda yake ƙoƙarin zuwa, ba yadda za a yi mai neman na bakinsa kawai ya yi aiki kan jiki kan ƙarfi kamar wanda yake son ya zama kamar mai gidansa a sana'ar da yake koyo, sanin makama zai ƙarfafa wa mutum gwiwa ta yadda zai faɗaɗa burinsa kuma ya yi ƙoƙarin cimma sa.


Mai kamfanin da kake lebura ko mai koyon aiki ko kasuwanci bai kwanta ranar Talata da daddare ya farka Laraba ya iske kansa mai kuɗi ko mai dukiya haka ba, bincika wasu hanyoyi ya bi ya zama haka? In ka samo to mai zai hana ka bi su tunda duk abinda yake da su na halitta kana da su? Ƙila ka ce ya yi aiki da wasu damammaki waɗanda kai ba ka da su yanzu, to an zo wurin, yanzu me ye damammakin? Kai ma ya za a yi kasame su? Abinda za ka saka a gaba kenan sai yadda hali ya yi, sanin makaman sana'a zai yi aiki sosai a wannan fannin, musamman wurin zaɓen hanyoyin da za a bi da aiki da lokaci da neman masu gidan rana, gami da sanin dabarun rayuwa.


DUBA NA GABAKaranta Hanyoyin Samun Nasara A Rayuwa (43) Cikin Sauki


5) Ba da damar yin bincike: Sanin makama kan sa a fara binciken kayan da mutane ke so, da wanda suke buƙata ba a kawo musu ba ko ba a san suna so ba, za a yi bincike a gwada sannan a ƙirƙiro kayan a kawo musu, ƙasar Sin wato "China" ta yi nisa a wannan fannin, sukan yi wa musulmai jallabiyoyi masu aiki, darduman sallah tasbahohi na ja da latsawa da dai sauransu, musamman lokutan aikin Haji, kuma suna samun kasuwa ba 'yar ƙarama ba, idan ka lura ba sa son Musulunci, amma tunda musulman suna buƙatar waɗannan kayayyakin sai a sayo musu, wani malamin zaure da na yi karatu a wurinsa yana ƙyamar taɓa sosan gaske, amma kuma yana sayar da ita a shagonsa, ga alama sanin kasuwancin ya fi yin rinjaye anan.


Za mu Ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user