Tuesday 16 November 2021

Sana'o'in Da Za A Iya Farawa Ba Tare Da Jari Ba Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga

Kafin mu tsunduma cikin fashin baƙi, ya kamata mu fahimci cewa sana’ar da ta fi dacewa da kai ta danganta da abubuwan rayuwa da kake matukar sha’awa, da abubuwa da ka ƙware akai, sannan da ƙwarewar ka wajen ƙarawa duk abunda kake yi daraja, da warware wa jama’a matsaloli. Yanzu ina so ka ɗauki biro da takarda, zan yi tambayoyi, sai ka amsa su ɗaya bayan ɗaya.


Sana'o'in Da Za A Iya Farawa Ba Tare Da Jari Ba
Hoto: Goalcast


Marubuci: Bello Galadanchi


1. Me ka iya? Zai iya kasancewa koma mene ne, ba dole sai ana amfani da shi wajen samun kuɗi ba. Ko tuƙin keke ne, idan ka ƙware sosai, to ka rubuta akan takardar ka.


2. Menene ka yi matuƙar ƙwarewa akai?


3. Me jama’a suke tunanin ka iya sosai?


4. Wanne irin ilimi ko baiwa ne kake da shi wanda ba kowa ne yake da shi ba, kuma jama’a za su ƙaru da shi? Misali, shi ne “Zan iya wanke riga, in busar da ita, kuma in goge ta a cikin mintuna talatin”, ko “ni da abokaina za mu iya wanke mota (detailing) ciki da waje a cikin mintuna goma”, ko “na iya koyawa ɗalibai rubuta jarrabawar Jamb domin su samu maki ɗari biyu da talatin”.


5. Su waye masu buƙatar sana’arka?


6. Al'umma baki ɗaya ne ke buƙatar sana’arka, ko kuma wani rukunin jama’a ne?


Idan za ka iya amsa waɗannan tambayoyin, to za ka fahimci ko wace sana’a ce tafi dacewa da kai.


Mafi yawancin mutane, musamman matasa na kukan rashin jari kafin su fara sana’a. Sana’o’in da suka yi nasara waɗanda aka fara babu jari sun fi waɗanda aka fara da jari, saboda haka rashin jari ba wani abu bane. Abun la’akari shi ne, shi rashin jari na harzuƙa mutum ya zama mai tunani, hangen nesa da mallakar dabaru iri-iri. Waɗannan suna daga cikin ilimin harkar da za ka laƙanta har ka fahimci sana’ar yadda ya kamata a dai-dai lokacin da take ƙara girma, kuma take bunƙasa. Idan kuwa ba ka mallaki tunani, da hangen nesa da dabaru ba tun daga tushe, to duk girman jarinka sai ya rushe.


JAMA’A GA SIRRIN FARA SABUWAR SANA’A WADDA ZA TA KAWO MUKU ARZIKI


Ka ƙwaƙulo wata matsala da jama’a suke fama da ita, sannan ka ƙirƙiro hanyar warware wannan matsala yadda za ka share wa mutane hawaye a cikin ɗan ƙaramin lokaci, sannan cikin rahusa idan aka kwatanta da sauran hanyoyin da ke warware wannan matsala.


Ga misali, a kullum Hajiyata tana kashe ₦500 wajen cefanen kayan miya a cikin birnin Kano, sannan tana biyan kuɗin babur ₦100 domin bai wa ɗan aike. Idan ka yi lissafi, a wata ta na kashe ₦18,000 (N15,000 na kayan miya, N3,000 na babur), sannan a shekara za ta kashe ₦216,000 (₦180,000 na kayan miya, ₦36,000 na babur).


Matsalar anan itace kullum sai ta bai wa yaro kuɗi ya je ya sayo. Idan yau yaron ya je da wuri ya kawo, to gobe yana iya yin jinkiri, jibi kuma ya dawo yace ledar ta ɓarke akan babur. Kun ga akwai rashin tabbas da zaman ɗar-ɗar. To idan kai mai dabara ne, sai ka kafa sana’ar safarar kayan miya daga ƙauyuka ko wajen gari zuwa gidaje a birni. Yadda za ka yi shi ne, ka samu kasuwa a wajen gari da ba ta da nisa sosai inda akwai kayan miya masu kyau kuma masu sauƙi, sannan ka ƙulla amintaka da masu sayarwa. To sai ka samu gidaje kamar huɗu zuwa biyar su zama kwastomominka na farko. Ka buga waya, ko ka aika saƙonnin WhatsApp domin jin ko na nawa suke buƙata kafin goma na safe (10:00 am), sannan ka sayo ka kai musu kafin ƙarfe goma sha ɗaya na safe (11:00). To tunda daga wajen gari kake kawo kayan, dole ne su fi sauƙi. A cikin gari, kayan miyan ₦500 ba su fi ₦300 ba a wajen gari. Kai kuma sai ka sayar wa Hajiya ₦450 ba tare da ta biya kuɗin babur ba. Yanzu ka warware mata matsaloli uku. 


Na farko, shi ne ka rage mata wahalar aika yaro da ɓata lokaci wajen yi masa kwatance da kuma zaman rashin tabbas. 


Na biyu, shi ne za ka kawo ma ta kayan miyan da wuri, saboda haka hankalinta ba zai tashi ba wajen makarar ɗora murhu.


Na uku, kuma mafi muhimmanci shi ne ka kawo ma ta kayan da sauƙi. Da can tana kashe ₦600 kullum, amma yanzu ya zama ₦450. A shekara ka rage ma ta ₦54,000, kai kuma ka samu ₦54,000. To idan gidaje biyar kawai kake hulɗa dasu, za ka tashi da ₦270,000 a shekara. Idan kuwa gidaje talatin kake sayarwa kayan miya, to za ka tashi da ₦1,620,000 a shekara. Ka ga yanzu harka ta ƙara girma, saboda haka dole ne ka ɗauki yara aiki. Idan ka tashi, sai ka koma ofis kana hulɗa da kwastomomi ta waya, su kuma yaran suna kai-kawo. Idan kana hulɗa da gidaje ɗari biyar, to za ka tashi da ₦27,000,000 a shekara, ka ga cikin shekaru goma kana da miliyan ɗari biyu da saba’in (₦270,000,000). Kar ka ga wai don kana da digiri ko matakin karatu na biyu ko na ƙarshe, ka ce a’a kai kafi ƙarfin sana’ar kayan miya. Yau da gobe za ka fi masu digiri samun arziki, kuma dole ne su kira ka miloniya.


To kaɗan kenan, amma a duniyar nan, akwai sana’o’i masu matuƙar yawa, kuma kowanne da irin albarkar da Allah ya yi mishi idan ka laƙanta. To tunda ba ka da jari, ga wasu sana’o’in da za ka iya farawa ba tare da kuɗaɗe ba, amma idan ka tashi, sai ka dubi ta yadda za ka bunƙasa yadda ake tafiyar da wannan sana’a yadda za ka rage wa kwastomomi adadin kuɗin da suke kashewa, da ɓata lokaci. Ka laƙanci waɗanne hanyoyin zamani ne za ka iya sanyawa a cikin harka domin jama’a suyi sha’awarta.


1. KULA DA DATTAWA DA TSOFAFFI: Akwai masu hali da yawa waɗanda suke buƙatar wanda zai kula da iyayensu da kakannin su, saboda harkoki sun yi musu yawa, ko ba’a garin suke ba. Hakan zai iya zama share musu inda suke zama, yi musu wanke-wanke, kai su unguwa, da taya su hira, yi musu karatun Alƙur’ani da warware musu matsalolinsu, duk abunda ka samu, ka tara. Ka tuna, kar ka kashe sama da rabin albashin da kake samu. Idan ka iya harkar sosai, kuma ‘yan uwa da sauran dangi suka ji labarinka, to za ka ga ana nemanka. Kai kuma sai ka nemi wanda ka san zai iya wannan aiki, ka bashi kwangila. Duk abunda ya samu, akwai kwamashonka a ciki.


2. KOYARWA A BAYAN FAGE: Akwai ɗalibai masu yawan gaske waɗanda suke buƙatar taimako wajen fahimtar darussan su na makaranta. Musamman lissafi, turanci da kemistri. Idan ka ƙware a ɗaya daga cikin waɗannan, to, babu shakka kana da kadara mai daraja da za ka iya amfani da ita wajen fara sana’a. Idan aka ji daɗin koyarwarka, kuma aka fahimci cewa kana da hankali da nutsuwa, to wasu iyayen za su neme ka don ka koya wa ‘ya’yansu. Idan sana’a ta ƙara girma, to sai ka nemi abokanka waɗanda ka san za su iya wannan aiki su zama malamai a makarantarka. Yadda ake karɓar albashi a wannan harka shi ne tsadancewa za ka yi. Kowane a sa'a ɗaya nawa za’a ba ka? Sannan a sa'a nawa ake so a kowace ranar koyarwa? Kuma sa'o'i nawa za ka koyar da ɗaliban baki ɗaya?


3. GYARA DA WANKIN MOTA: Idan karatun injiniya ka yi, to mai zai hana ka fara gyaran mota? Idan abunda ka karanta bai shafi mota ba, to za ka iya wanke ta. Idan Alhaji yana kashe naira dubu biyu (₦2,000) a wanke masa motarsa (detailing) a cikin sa'o'i biyu, to mai zai hana ka caji naira dubu ɗaya (₦1,000) kuma ka kammala a cikin mintuna arba'in da biyar? Hakan zai sa mutane da yawa su komo wajenka, kai kuma sai ka ɗauki yara ka koya musu yadda ake wannan aiki da saurin gaske, sannan idan abubuwa suka bunƙasa, ka fara bin kwastomomi har zuwa inda suke, wato gida ko ofis kana wanke musu mota. Sai ka ɗinka wa yaranka kayan aiki, sannan ka horar dasu a ɓangarori da dama kamar ladabi da biyayya, amana, kamun ƙafa, tsafta, kula da aiki da barkwanci. Na ba ka shekara ɗaya, duk garinku sai an ji labarinka da kamfaninka na wankin mota.


4. HAYA: Ka bada hayar komai naka, kama daga teburi, zuwa mota, babur, wayar hannu, babbar riga, takalma da komfuta idan kana da ita.


5. SHARA DA WANKI: Waɗannan sana’o’i ne da jama’a suka raina, amma idan har ka fara, kuma ka ƙulla dangantaka mai ƙwari da kwastomominka, to a cikin watanni kaɗan za ka ɗauki yara, suna aiki a kamfaninka, yayin da kai kuma kake ƙara bunƙasa ta zuwa wasu unguwannin.


6. SAYAR DA ABINCI DA KAYAN DAƊI: Za ka iya farawa a gidanku kana rabawa ‘yan uwa da abokai. Idan akwai daɗi, to za su fara biyanka. Kai kuma sai ka tara, ka fara bin jama’a a waje kana yi musu talla. Sannu a hankali za ka buɗe shago.


7. RUBUTU: Idan Allah ya ba ka baiwar rubutu, to kar jikinka yayi sanyi don babu wanda ya buga littafinka. Ka binciki ko waɗanne irin labarai jama’a suke sha’awa, sannan ka rinƙa rubuta musu kana aika musu ta shafin sada zumunta na Facebook ko na WhatsApp. Idan suka ji daɗin labaranka, to duk ranar da ka tashi buga sabon littafi, to za ka samu wanda zai ɗauki nauyinka saboda ya san za’a samu alheri. Kai kuma daga nan, sai kawai ka ci-gaba da rubutu kana ilimantarwa da nishadantar da al'ummarka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user