Friday 9 March 2018

Shin dagaske ne Zainab Indomie ta yi Film din Batsa na Blue Films?

Tura Wannan Zuwa Ga
Tarihin rayuwa ta a takaice

Assalamu alaikum da farko dai sunana Zainab Abdullahi, wacce aka fi sani da Zainab Indomie. Ni cikakkiyar Bahaushiya ce, an haife ni a Abuja kuma ina zaune a Abuja.


Na yi makarantar Firamare da sakandare a Abuja, sannan na yi difloma a kan Ilmin Kimiyyar Kwamfuta a Kaduna.
Yadda na fara harkar fim
Ka san babu yadda Allah ba Ya yi da mutum. Tun ina karama nake sha’awar kallon fina-finan Hausa.

Ina jin dadi idan ina kallon fina-finan Hausa. Wannan ne ya ja hankalina, ya sa na yi burin a rika damawa da ni a harkar. A haka na tsinci kaina a harkar wanda har zuwa yanzu na zama wata aba a duniyar fina-finai.

Kafin na shiga harkar fim na yi fadi-tashi sosai. Ina cikin fadi-tashin ne Allah Ya hada ni da Ali Nuhu, bayan na fada wa iyayena sun amince sai suka damka ni a hannunsa a matsayin amana. Daga nan ne ya yarda ya kuma rika sanya ni a cikin fina-finansa. Ba ni da wani ubangida a harkar fim da ya wuce Ali Nuhu har yau kuma har gobe. Ya ma wuce ubangida ya zama uba kuma dan uwana. Fim din da na fara ko kuma na ce wanda ya haskaka ni shi ne ‘Garinmu Da Zafi’. Wannan fim din shi ne fim din da na fi so duk a cikin fina-finan da na yi.

Lakabin IndomieNa san mutane da yawa za su so jin yadda na samu lakabin ‘Indomie’ da kuma wurin da na same shi.

Wannan sunan ya samo asali ne tun ina firamare. Tun a lokacin babu abincin da na fi so kamar taliya, hakan ne ya sa na daukaka taliyar Indomie a kan kowane irin nau’in abinci. Wannan dalilin ne ya sa aka fara kirana da lakabin ‘Indomie’
.
Dalilin ramata
A baya idan mutane za su iya tunawa na yi jiki sosai, a gaskiya idan har kana da jiki to za ka sha wahala wurin gudanar da sauran ayyuka musamman ma mu ‘yan fim.
Idan akwai wani rol wanda ya shafi rawa ko gudu ko tsalle-tsalle, to dole idan har kana so ka sake, ka ji dadin jikinka sai idan ba ka da kiba, domin idan kana da kiba bayan an gama za ka ji ka wahala sosai, sannan ba za ka yi rol din yadda ake so ba. Don haka ba wai jinya ko tashin hankali ko tunani ko yunwa ba ne suka sanya na rame ba, a’a, na rage kiba ne, wanda ake kira ‘slimming’ da Turanci.

Hotunan tsiraiciA gaskiya ban san da su ba, mutane ne kawai suke yi don su bata mini suna. Ana yin hakan ne don a durkusar da jarumi don a daina yi da shi. A ce taurarinsa sun dusashe, amma duk wannan abin1 da ake yi mini Allah bai sa taurarina sun dusashe ba.


 Ana sona kuma masu kaunata ba su daina ba. Babu abin da zan ce ga masu yi mini wannan abin sai dai Allah Ya saka mini. Ka lura duk wanda ya ci gaba ko ya samu daukaka sai ya fuskanci irin wadannan abubuwa.

Rashin fitowa a fina-finai kwanan nanNa san mutane za su ce a yanzu an daina yi da ni, to su sani ba haka ba ne. Idan ba za ka manta ba a baya na ce maka na yi difloma a Kaduna, kuma kowa ya sani taura biyu ba za ta taunu ba.

Hakan ya sanya na ajiye harkar fim har sai da na kammala karatuna, amma nan ba dadewa ba masoyana za su fara ganin sababbin fina-finaina.Hotuna daga shafin MuryarHausa24.Com.NG

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN DUNIYA NA DAYA

Kalli Sababbin Hotunan Jaruma Rahama Sadau Tana Siyar da Masara akan Titi

Takaitaccen Tarihin Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria

Kalli Sabon Video Yadda Fati Washa Tayi Cikin Shege a gaban Mahaifinta


Source: Aminiya

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user