Wednesday 29 May 2024

Karanta Hikayar Wasu Mabarata Biyu Da Wata Gimbiya

Tura Wannan Zuwa Ga

An hakaito cewa a cikin birnin Bagadaza, zamanin mulkin Halifa Al-Mansur, an yi wasu mabarata guda biyu da kodayaushe ba su da wurin allazi wahidun sai ƙofar fada. A kullum mabaraci na farko ba shi da baran da ya wuce, "Allah ka wadata ni daga cikin taskar Abbasiyawa. Shi kuwa ɗayan sai ya ce, "Ya Allah ka wadata ni daga cikin taskarka."


Hikayar Gimbiya da Mabarata 
Hoto: Look and learn


MarubuciBukar Mada


To, a kowace rana idan gimbiya Zubaidah za ta shige tana jin waɗannan mabarata. Idan ta shiga gida sai ta aiko wa mabaraci na farko, mai cewa Allah ya wadata shi daga cikin taskar Abbasiyawa, dafaffiyar kaza. Ta kuma ba da dirhamai biyu a kawo wa na biyun mai cewa Allah ya wadata shi daga cikin taskar Allah.


Aka yi kamar kwanaki goma tana yi musu wannan alheri. Ran nan sai ta ji mabaraci ɗaya kurum ke baran, wanda take aika wa da kaza. Sai ta sa aka kira shi. Da ya zo ta tambaye shi, "kai kuwa ka roƙi Allah ya wadata ka daga taskarmu, mun kuwa yi iyakar ƙoƙarinmu. Shin abin da muka ba ka bai wadace ka ba ne har yanzu?"


Sai mabaraci ya ce, "ranki ya daɗe ai ni ba wani abu da ake ba ni sai kaza kullum."


Ta tambaye shi, "to me kake yi da kazar idan an ba ka?"


Ya ce, "abokin barana nake sayar wa dirhami biyu, domin na fi son kuɗin da kazar."


Sai Zubaidah ta ce, "tsarki ya tabbata ga Allah. Haƙiƙa wanda duk ya roƙe shi kai tsaye to ya rabauta." 


Ta dubi mabaraci ta ce, "ka sani cewa a duk lokacin da na ba abokinka dirhamai biyu, to kai kuma ina cusa dirhamai goma a cikin kaza a kawo maka domin dai mu wadata ka daga taskarmu, kamar yadda ka roƙa. Ashe dai babu mahaluƙin da ya isa ya wadata wani sai Allah."


Shi kuwa wancan mabaraci da ya ga ya tara kuɗin da za su ishe shi jari, sai ya watsar da baran ya rungumi kasuwanci. Allah kuwa ya buɗe masa ƙofofin arziki, ya zama mawadaci a cikin Birnin Bagadaza.


Roƙi Allah a kan komai, shi ne mai biyan buƙatun bayi.


Don ci gaba da samun ire-iren waɗannan, ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user