Sunday 18 August 2024

Karanta Hakikanin Asalin Sunayen Hausawa Tare Da Ma'anonin Su

Tura Wannan Zuwa Ga

A zamanin da kafin zuwan musulunci ƙasar Hausa babbar hanyar samun sunaye ta dogara kacokam a kan faruwar wani muhimmin abu sai Bahaushe ya laɓe da guzuma ya harbi karsana, ma'ana ya laɓe da faruwar wannan abu ya sa wa yaro ko yarinya suna.


Asalin Sunayen Hausawa Tare Da Ma'anonin Su
Hoto: Hausa Naija News


Kasancewa ta mazaunin Kano sai na fara binciken nawa da ma'anar sunan.


Ga kaɗan daga cikin binciken da na gudanar zan gutsura muku ku lasa:-


1. SHEKARAU :- Yaron da ya shekara a ciki shi ake kira Shekarau mace kuwa ana kiranta SHEKARE ko SHEKAU.


2. TANKO :- Shi ne namijin da aka haifa bayan haihuwar mata da yawa.(ya ɗan bambanta da mati kaɗan).


3. DELU :- Yarinyar da aka haifa bayan maza da yawa.


4. GOSHI :- Yarinyar da lokacin haihuwar ta aka samu arziki mai yawa ba zato ba tsammani.


5. YALWA :- Yarinyar da aka haifa iyayenta na cikin wadata.


6. MAITAMA :- Yaron da aka dawo ɗibar TAMA aka tarar an haife shi.


7. ƊAN DARE :- Yaron da aka haifa da daddare.


8. TINAU :- Yaron da haihuwa ta ɗauke wa mahaifiyar shi sai bayan lokaci mai tsawo aka haife shi, shi ake kira TINAU.


9. SO-DANGI :- Yaro ko Yarinyar da iyayen  ke zaune nesa da dangi sai zama ya ƙare musu suka tashi suka dawo cikin dangi uwar na ɗauke da tsohon cikin shi ana zuwa aka haife shi, shi ake kira SO-DANGI.


10. GAMA :- A zamanin da ana aure bisa cancanta ne, to duk lokacin da wani da bai cancanta ba ya yi sa'a ya auri wata isassa/isasshiya to ɗan da ta haifa sai a sa mai suna GAMA.


11. SADAU :- Yaron da uban ya ɓata da uwarshi daga baya suka shirya to duk yaron da ta fara haihuwa sai a kira shi da SADAU.


12. AUTA :- Ƙarshen haihuwa.


13. KYAUTA :- Yaron da uwar sa ba ta taɓa haihuwa ba shekara da shekaru sannan aka haife shi.


14. DAWAI :- Saɓanin da ya kai ga saki sannan uwar ta yi kome to ɗan da ta haifa shi ake kira DAWAI.


15. BAKWAI :- Yaron da aka haifa cikin shi na da wata bakwai (Bakwaini).


16. SHAWAI :- Yaro/yarinyar da aka sha wurin haifuwar shi/ta.


17. GWAMMA :- Yarinyar da aka haifa lokacin da ake da burin haihuwar ɗa namiji.


18. MARKA :- Yarinyar da aka haifa lokacin ruwa na marka-marka.


19. AMARYA :- Yarinyar da aka haifa ranar da jinjirin wata ya tsaya, namiji kuma ana kiran shi MAGAWATA.


20. BUJI/HAZO :- Yaron da aka haifa lokacin da ake hazo.


21. CI-TUMU/SHA-GERO/SHAGE :-Yaron da aka haifa lokacin nunar gero.


Za mu kawo muku ƙari akan wannan kamar su Makwashi, Mati, Tsoho, Ɗan Dare, Talle, Magaji, Babangida, Mai Damma, Ayashe, Ajuji, Yaduwa, Bawa, Barau, Barmani, Dan Wabi, Ƙosau, Jimrau, Nomau, Wada, Gayya, Mayau, Na Hantsi, Gambo, Kadarko, da sauran su.


Tushe/Asali: Waziri Aku

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user