Showing posts with label ALKUR'ANI MAI GIRMA. Show all posts
Showing posts with label ALKUR'ANI MAI GIRMA. Show all posts

Wednesday, 10 July 2024

Rayuwar Dan Aljanna

Rayuwar Dan Aljanna

Allah da ya halicci Ɗan Adam ya kuma saukar da shi a doron ƙasa, sai ya kimsa masa sha’awar samun canje-canje na yanayi da guri da hali. Yayin da ya daɗe a cikin wani yanayi ko guri ɗaya, duk yakan ji ya gundure shi, ya gaji da shi, komai daɗinsa, yana son ya ga wani canji.


Ɗan Aljannah Ba Ya Bukatar Wani Canji
Hoto: Just Dawah




Wannan yanayin halitta da Allah ya yi wa Ɗan Adam, ita ce take taimakon shi wajen kawo ci-gaba a rayuwa ta duniya, da raya ƙasa, da haɓaka ta, kamar yadda Allah ya nema daga wajensa.

Amma a Aljanna sai Allah ya cire masa wannan sha’awar, ya sanya masa tsananin ƙauna da sha’awar zama guri guda, ba tare da ya ƙosa ba, ko ya riƙa tunanin canji daga yanayin da yake ciki na ni’ima zuwa wani yanayi daban.

Wannan kuma shi ne ya fi dacewa da rayuwar Ɗan Aljanna wanda Allah ya masa tanadin duk wata buƙatarsa, ya samar masa duk wani abu na jin daɗi da morewa a cikin gidan Aljannah.

Da a ce, za a bar shi da waccar sha’awa ta shi, kamar yadda take a duniya, to da ya nemi Allah ya canza masa wata aljannar ba wadda yake ciki ba, domin ya gaji da ita.

Shi ya sa Allah ya ce mana, “Lallai waɗanda suka yi imani kuma suka yi aiki na ƙwarai, ajannatan Firdausi sun tabbata masauki gare su. Suna masu dawwama a cikinsu, ba su buƙatar wani canji game da su”. [Al-Kahfi, 107-108].

Thursday, 28 March 2024

Abubuwa 28 Wadanda Ya kamata Ku San Su Game Da Ranar Alkiyama

Abubuwa 28 Wadanda Ya kamata Ku San Su Game Da Ranar Alkiyama

Allah ya ambaci sunayen ranar alƙiyama da sunaye mabambanta har guda ashirin da takwas. Za mu yi muku bayaninsu ɗaya bayan ɗaya da ma'anoninsu da kuma ayoyin da aka ambace su a cikin Alkur'ani.


JERIN SUNAYEN RANAR ALƘIYAMA A CIKIN QUR'ANI TARE DA MA'ANONINSU
Hoto: Awaz The Voice


Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa


1- Ranar alƙiyama. An ambaci wannan sunan a wurare saba'in a Alkur'ani. Kamar faɗinsa maɗaukakin sarki

"  وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ تَرَى الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللَّهِ وُجُوهُهُم
مُّسْوَدَّةٌ
Ma'anar ranar alƙiyama shi ne ranar tsayuwa. Kamar inda Allah ke cewa" 
يوم يقوم الناس لرب العالمين"


2. An ambace ta da Yaulmul Aakhir wato ranar ƙarshe kenan wacce ba wata rana bayanta. Kamar faɗinsa Allah cewa" إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَادُوا وَالصَّابِئُونَ وَالنَّصَارَى مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَعَمِلَ صَالِحًا فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ


3. An ambace ta 'Assaa'ah' kamar faɗinsa Allah cewa "
إِنَّ السَّاعَةَ آتِيَةٌ أَكَادُ أُخْفِيهَا لِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍ بِمَا تَسْعَىٰ

Al'imam Alqurtabiy ya bayyana ma'anar Assa'ah da cewa "
أنّ الساعة تدلّ في اللغة على جزءٍ من الزمن دون تحديدٍ، وسُمِّيت القيامة بالساعة؛ إمّا من باب قُرب وقوعها، وإمّا تنبيهاً على ما فيها من أمورٍ عظيمةٍ، وقِيل لأنّها قد تأتي فجأةً في أيّ وقتٍ"

A harshen larabci kalmar saa'a na nufin wani yanki daga lokaci wanda ba a ƙayyade ba. An ambaci Alƙiyama da Assa'ah ne ko don kusancin faruwarta, ko don gargaɗi a kan manyan al'amuran da ke cikinta. An kuma ce ta kan zo kowanne lokaci wanda ba a yi zato ba.


4. An ambace ta ranar tashi. Kamar faɗinsa maɗaukakin sarki cewa "
ثُمَّ إِنَّكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ تُبْعَثُونَ


An ambace ta da haka ne saboda a cikinta ne ake raya matattu ake tashinsu daga kaburburansu.


5. An ambace ta ranar fitowa kamar faɗinsa ta'ala cewa"

يَوْمَ يَسْمَعُونَ الصَّيْحَةَ بِالْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُرُوجِ


An ambace ta da hakan ne domin a ranar ne mutane ke fitowa daga kaburburansu zuwa tsayuwa.


6. An ambace ta ranar rarrabewa kamar faɗinsa Allah cewa "
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ


An ambace ta da hakan ne domin a ranar ne Allah ke rarrabewa tsakain halittu.


7. An ambace ta ranar buɗi. Kamar faɗinsa Allah cewa "
قُلْ يَوْمَ الْفَتْحِ لا يَنفَعُ الَّذِينَ كَفَرُوا إِيمَانُهُمْ وَلا هُمْ يُنظَرُونَ"


8. An ambace ta da ranar addini.

Faɗinsa cewa" مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ

Malamai suka ce abin da ake nufi da addini shi ne sakamako. A ranar ne Allah zai yi wa bayinsa sakamako a kan ayyukansu.


9. An ambace ta ranar ƙara saboda tsananin ƙarfinta. Faɗinsa Allah cewa " فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ


10. An ambace ta da Attammah Alkubrah. Faɗinsa Allah cewa
فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰ


Attammah a lugar larabci na nufin al'amarin da mutum ba zai iya da shi ba.


11. An ambace ta ranar hasara. Misali faɗinsa Allah cewa "
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ الْحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الْأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ وَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ


Hasara a lugar larabci na nufin nadama mai tsanani musamman ga 'yan wuta a kan ayyukansu.


12. An ambace ta Algaashiyah. Faɗinsa Allah "
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ

Akwai saɓanin malaman tafsiri a kan ma'anar wannan kalma. Kuma karatu ne mai zaman kansa ga shi ban son na tsawaita.


13. An ambace ta ranar dawwama.

Fadinsa Allah"
ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ الْخُلُودِ


Rana ce da 'yan aljanna ke dawwama a cikinta.


A taƙaice don kar na tsawaita ga ragowar sunayen da aka ambaci ranar alƙiyama da su a Alkur'ani.

14. يوم الحساب
15. الواقعة
16. يوم الآزفة
17.  يوم الجمع
18. الحاقة
19. القارعة.
20 يوم التلاق
21. يوم التناد
22. يوم التغابن
23. يوم الوعيد
24. اليوم العسير
25. اليوم المشهود
26. يوم عبوس قمطرير
27. النباء العظيم
28. الجاثية


Kowane suna yana buƙatar sharhi amma lokaci bai ba da haɗin kai ba.


Hikimar yawaitar sunayen alƙiyama shi ne kowanne suna yana bayyana wata siffa tsayayyiya. Hakan zai ƙara tabbatar da imani a zukata. Rayuka su zamanto shiryayyu saboda ranar alƙiyama.


Allah ka ba mu dacewa a gobe alƙiyama Amin.

Friday, 23 December 2022

Falala 8 Ta Karanta Alkur'ani Mai Girma Ga Musulmai

Falala 8 Ta Karanta Alkur'ani Mai Girma Ga Musulmai

Karatun Alkur'ani ibada ce mai girma wacce ake samun lada mai tarin yawa tare da samun Aljanna, wanda da yawan mutane a yanzu sun shagala ga barin haka, akan sami wanda idan ba a cikin sallah ba ya kan shafe watanni bai ɗauki Qur'ani ya karanta ba, wanda hakan ba ƙaramar tawaya da asara ba ce.


Muhimmancin Karanta Alkur'ani Mai Girma Ga Musulmai
Hoto: Pexels


Marubuci:- Imam Aliyu Indabawa


Alkur'ani rahama ne, ceto ne, kuma alkhairi ne ga mai karanta shi. Lokacin da Allah ke ambatar siffofin salihan bayinsa 'yan aljannah sai ya fara da makaranta Alkur'ani kamar faɗinsa cewa"


 إن الذين يتلون كتاب الله وأقاموا الصلاة وأنفقوا مما رزقناهم سرا وعلانية يرجون تجارة لن تبور 


"Waɗanda suke karatun Alkur'ani suke sallah a kan lokaci suke kuma ciyarwa a ɓoye da a bayyane suna ƙaunar kasuwanci mara yankewa".


Wasu daga malaman tafsiri suka ce kasuwanci mara ƙarewa da aka ambata shi ne rahama da lada.


An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara musu yarda, Annabi (S.A.W) ya ce " Babu hassada sai a cikin abu biyu, mutumin da Allah ya ba shi Alkur'ani ya ke karanta shi dare da rana, da wanda Allah ya ba shi dukiya ya ke ciyarwa dare da rana".


لا حسد إلا في اثنتين‏‏ رجل آتاه الله القرآن، فهو يقوم به آناء الليل وآناء النهار، ورجل آتاه الله مالا، فهو ينفقه آناء الليل وآناء النهار


Daga faloli da darajojin karanta Alkur'ani:


1. Samun ɗaukaka a wajen Ubangiji duba da hadisin da Manzo (S.A.W) ke cewa " Allah yana da waɗanda ke matuƙar ƙauna a cikin mutane, aka tambaya su waye ya rasulallah? Ya ce su ne makaranta Alkur'ani.". Ibn Maja ya rawaito shi, Albani ya inganta shi.


قال رسول الله صلى الله عليه وسلم

إن لله أهلين من الناس قالوا: يا رسول الله ، من هم ؟ قال: هم أهل القرآن ، أهل الله وخاصته.

رواه ابن ماجة وصححه الألباني


Manzon Allah ya ce " Mafificin cikinku shi ne wanda ya karanci Alkur'ani ya ke karantar da shi.


 خيركم من تعلم القرآن وعلمه


2. Samun lada mai yawa tare da kyakkyawa ababen ninkawa.


Kamar hadisin da Muslim ya fitar da shi cewa Manzon Allah (S.A.W) Ya ce " Shin ɗayanku ba zai yi sammako zuwa masallaci ya fahimci ayoyin Alkur'ani guda biyu ko ya karanta su ya fi masa da a ba shi Taguwa guda biyu ba, aya guda uku ta fi Taguwa guda uku, aya guda huɗu ta fi Taguwa guda huɗu.


أفلا يغدو أحدكم إلى المسجد فيعلم أو يقرأ آيتين من كتاب الله خير له من ناقتين وثلاث خير له من ثلاث وأربع خير له من أربع ومن أعدادهن من الإبل


Manzo ya ce " Wanda duk ya karanta aya ɗari a wani dare ba za'a rubuta shi cikin gafalallu ba, ko za'a rubuta shi cikin masu ibada".


ومن قرأ في ليلة مائة آية لم يكتب من الغافلين أو كتب من القانتين


3. Samun ɗaukaka a duniya.


Kamar hadisin da ke cewa" Allah na ɗaukaka wasu mutane da Alkur'ani ya kuma ajiye wasu".


إن الله يرفع بهذا الكتاب أقواما ويضع به آخرين


4. Samun daraja maɗaukakiya a Aljannah.


Hadisi ya bayyana cewa" Ranar alƙiyama za a ce da ma'abocin Alkur'ani karanta ka yi sama, rera kamar yadda kake rerawa a duniya, mazauninka zai tiƙe a ayar da ka tsaya." .


‏يقال لصاحب القرآن‏:‏ اقرأ وارتقِ ورتل كما كنت ترتل في الدنيا، فإن منزلتك عند آخر آية تقرؤها‏


5. Samun ceto gobe kiyama.


Manzo (S.A.W) Ya ce "Ku karanta Alkur'ani don zai zo muku mai ceto gobe ƙiyama"


6. Saukar nutsuwa.


Hadisi daga Abu-huraira: Babu mutanen da za su taru suna karanta Alkur'ani sai nutsuwa ta sauka a gare su.


 وما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله يتلون كتاب الله تعالى، ويتدارسونه بينهم، إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة، وحفتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده


7. Ninkuwar lada.


Annabi (S.A.W) Ya ce "Wanda ya karanta harafi guda daga Alkur'ani yana da lada, kowanne lada akwai ninkinsa goma.".


قال: من قرأ حرفا من كتاب الله فله حسنة، والحسنة بعشر أمثالها


8. Darajar kasancewa tare da Annabawa da manzanni.


Hadisi daga Nana Aisha (R.A), Manzo (S.A.W) Ya ce" Mahiru da Alkur'ani yana tare da Annabawa da manzanni, wanda ke karanta Alkur'ani yana sassarƙewa don wahala yana da lada biyu.".


الماهر بالقرآن مع السفرة الكرام البررة والذي يقرأ القرآن ويتتعتع فيه وهو عليه شاق فله أجران


Ma'anar Mahiru shi ne wanda ke karanta Alkur'ani ya ke kiyayewa da shi ya ke kuma aiki da shi.


Allah ya tabbatar da mu tare da Alkur'ani ya sa ya kasance ceto a garemu gobe ƙiyama Amin.

Thursday, 31 October 2019

ME KUKA SANI GAME DA  LITTAFIN KU AL-QUR'ANI MAI GIRMA?

ME KUKA SANI GAME DA LITTAFIN KU AL-QUR'ANI MAI GIRMA?

ALQUR'ANI littafi ne da Ubangiji Ya saukarwa Annabi Muhammad (s.a.w) wanda ake bautawa Allah da karanta
shi.

Yayin Karanta Al-Kur'ani Mai Girma


Qur'ani na da sunaye kamar
haka;

1. Alfurqan
2. Attanzeel
3. Azzikir
4. Alkitab
5. Alwahay
6. Ahsanul Hadith
7. Assiradul Mustaqim
8. Al'urwatul Wuthqa
9. Arruuhu
10. Alqaulu

Yawan suna na nuna darajar abu.

Qur'ani an saukar da shi cikin
shekaru 23

Qur'ani an fara saukar da shi
a daren Lailatul ƙadar, a
karshen Ramadan bayan
Manzon Allah (s.a.w) ya kai
shekaru 40 a shekara ta 610
mldy.

Marubuta Qur'ani cikin
Sahabbai sun hada da;

1. Abubakar RA
2. Umar RA
3. Usman RA
4. Aliyu RA
5. Ubayyu bn Ka'ab RA
6. Zaidu bn Thabit RA
7. Zubair bn Awwam RA
8. Mu'awiyya RA

Surah da ta fi tsawo a
Qur'ani ita ce Suratu Baqara.

Ayoyin ta 286

Aya mafi tsawo a Qur'ani ita
ce aya da tayi magana akan
bashi, aya ta 282 a Baqara,
kalmomin ta 128.

Qur'ani na da surori 114.

Qur'ani na da ayoyi 6236.

Qur'ani na da kalmomi
77,439.

Qur'ani na da harrufa
323,015.

Qur'ani na da Juzi'i 30.

Qur'ani na da Hizbi 60.

Qur'ani na da rubu'i 240.

Qur'ani na da ushuri 480.

Surorin Makkah 85.

Surorin Madinah 29.


Surorin da suka fara da
Alhamdu guda 5

Surorin da suka fara da
Tasbihi guda 6

Surorin da suka fara da
harrufa guda 19

Guraren Sujjada a Qur'ani
guda 15.

Farkon wanda ya fara
bayyana karatun Qur'ani cikin
Sahabbai a Makkah shi ne
Abdullahi bn Mas'ud

Kalma mafi tsayi a cikin
Qur'ani ita ce
'Fa'asqainaakumuhu' ta na da
harrufa 11 a rubutun ta na
larabci.

Qira'ar da tafi shahara
wajen karatun Qur'ani ita ce
wayar Hafs daga Aasim.

Hafs ya bar duniya a shekara
ta 180 H, Asim kuma 127H

Tsuntsaye da aka ambaci
sunayen su a Qur'ani;

1. Alba'ubh
2. As Salwa
3. Al Guraab
4. Al Jarad
5. An Nahl
6. Al Hudhuda
7. Az Zubab

Sahabin da aka ambaci
sunan sa a Qur'ani Zaidu bn
Thabit a cikin Suratu Ahzab.

Rabe-raben Qur'ani ;

Akwai Surori masu suna;

As Saba'ud Diwaal- sune
Bakara, Aali Imran, Nisa'i,
Ma'ida, A'araf, An'am, Yunus.
Su 7 ne, su suka fi tsayi.

Akwai Almi'aini; daga bayan
Yunus zuwa Surorin da suka
kai ayoyi 100 ko kusa da
haka:

1. Almathani
2. Almufassal su ne kananan
surori daga 'Qaaf' ko 'Hujrat'

Surah mafi girma ita ce
Suratu Fatiha.

Yayin Karanta Al-Kur'ani Mai Girma

Aya mafi girma ita ce Ayatul Kursiyyu.

Shugaban masu Tafsirin Qur'ani shi ne
Imamud Dabariy.

Annabin da aka fi ambaton
sunan sa a Qur'ani shi ne
Annabi Musa (s.a.w) sau 136

Sura ta karshen sauka cikin
Qur'ani ita ce suratun Nasr
(Iza ja'a)

Aya ta karshen sauka a
Qur'ani ita ce aya ta 281 a
cikin Bakara (Wattaquu
yauman) a magana mafi
inganci

Surorin da aka ambace su
da sunan dabbobi;

1. Baqara-Saniya
2. Namli-Qudan Zuma
3. Ankabut-Gizo Gizo
4. Nahli-Turuwa
5. Fiyl-Giwa.

Surorin da aka ambace su da
sunayen Annabawa;

1. Suratu Yusuf
2. Suratu Hud
3. Suratu Ibrahim
4. Suratu Muhammad
5. Suratu Nuh
6. Suratu Yunus

Surorin da aka ambace su
da sunayen su taurari;

1. Suratut Najm
2. Suratul Qamar
3. Suratud Dariq
4. Suratush Shams
5. Suratul Buruj.

Surorin da aka ambace su da
sunayen lokuta;

1. Suratul Fajr
2. Suratul Laili
3. Suratud Dhuha
4. Suratul Asr

Dabbobin da aka ambace su
cikin Qur'ani;

1. Baqara Saniya
2. Ba'ubha Kwarkwata
3. Zubaab Quda
4. Namli Tururuwa
5. Hudhuda tsuntsu
6. Naaqah Raquma
7. Khail Doki
8. Bighaal Alfadari
9. Himar Jaki
10. Qusuurah Zaki
11. Jaraad Fari
12. Zi'b Kerkeci
13. Kalb Kare
14. Guraab Hankaka
15. Fiyl Giwa
16. Ankabuut Gizo Gizo
17. Nahl Zuma
18. Su'ban
19. Ibil Rakumi

Sunayen Mala'iku da ya zo
cikin Qur'ani;

1. Jibril
2. Miika'iil
3. Maalik
4  Haruut
5. Maarut.

Daular da aka ambace ta cikin
Qur'ani ita ce daular Rumawa-
Ruum

Qabilar da aka ambace ta a
cikin Qur'ani ita ce qabilar
Quraishawa-Quraish

Littattafan Tafsiri da suka fi
shahara;

1. Tafsirud Dabari
2. Tafsiru Ibn Katheer
3. Tafsiru Ruhul Ma'ani-
Aluusiy
4. Tafsirul Qurdabi
5. Tafsiru Mafaatihul Gaib

Gurare huɗu 4 sunan Mai Gidan
mu (Annabi Muhammad S.A.W) ya zo a cikin Qur'ani;

1. Aali Imran aya ta 144
2. Ahzab aya ta 40
3. Muhammad aya ta 2
4. Fathi aya ta 29.

Anyi wannan binciken daga
littafin

ﻣﺎﺫﺍ ﺗﻌﺮﻑ ﻋﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻭﺍﻟﻨﺒﻲ


MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA YADDA LITTAFIN BIBLE YA TABBATAR DA ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

Download Complete Tafseer Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Audio

KARANTA DUMBIN LADA MAI TARIN YAWA DAMAI KARANTA AL-QUR'ANI YAKE SAMU

Shin ko kasan cewa idan ka dauki Al-Qur'ani a hannuka shaidan yana fushi.

Idan ka budeshi shaidan yana kuka.

Idan kayi bismilla kuma ya kan gudu.

Idan kashiga karatu kuma yakan samu kunci a zuciyar sa.

Qur'ani abin alfaharin mu ne,
Allah Ya bamu haddar sa da
ikon aiki da shi Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode