Showing posts with label Ra'ayi Riga. Show all posts
Showing posts with label Ra'ayi Riga. Show all posts

Monday, 17 March 2025

Sana'o'in Da Ba A So Ka Yi Wa Mata Dariya Idan Kana Yin Su

Sana'o'in Da Ba A So Ka Yi Wa Mata Dariya Idan Kana Yin Su

Idan kana wannan sana'o'i guda biyar kada ka sake ka dinga yi wa mata dariya.


Ga su kamar haka:


Chajin Waya


Aradu idan ka yi wasa ko kuɗin fetur ɗin da ka siyo ba zai haɗu ba.


Sana'o'in Da Ba A So Ka Yi Wa Mata Dariya Idan Kana Yin Su
Hoto: New York Post

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Provision store


Aradu kafin ka ankare shagonka sai ya zama saura kwalaye sai sun bindige maka jari kamar yadda soja ke bindige ɗan ta'adda a daji.


Kayan kwalliya


Faka-faka za su kwashe maka ƴan mayukan shagon da kwalli da barbaɗa kumatu da jan baki, su bar ka ƙuda yana bin bakinka yunwa ta kassara ka.


KeKe Napep


Adai-daita shi ma kada ka dinga yi wa mata dariya musamman zawarawa, yanzu za su yi ta hawa suna sauka na fetur ma sai ka yi ciko su bar ka ku yi ta wasan ɓuya da mai mashin. Ka ci balas ƙarshe ya ƙwace mashin ɗinsa ka lashe kenan.


Mai Siyar da wayoyin hannu


Taɓ wannan idan ba ka yi wasa ba lokaci guda mace za ta mayar da kai ƙauye ta cinye jarin ta bar ka da ƙaton akwakun glass a gaba kana ta gogewa ƴan wayoyin ba su fi biyu a ciki ba.


Sai a lura masu irin waɗannan sana'o'in kada ku dinga yi wa mata dariya.


Ku ci magani kamar kakarku ta mutu kullum ko matanku sau biyu za ku dinga musu dariya a rana, sau ɗaya ƙarfe 10 na dare da kuma ƙarfe 2 na dare.

Tuesday, 4 March 2025

Abubuwan Da Sanin Su Ya Fi A Ba Ku Kyautar Kudi

Abubuwan Da Sanin Su Ya Fi A Ba Ku Kyautar Kudi

Kana canja tunaninka komai zai canja na jikinka tun daga suturar da kake sakawa, yanayin tafiyarka, abokanka da cin abincinka wani lokacin har matarka sai ta sauya ita ma.


Abubuwan Da Sanin Su Ya Fi A Ba Ku Kyautar Kudi
Hoto: Vecteezy

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Mata suna son jima'i kwatankwacin yadda suke son kuɗi, don haka tafiya ka bar matarka har wata shida ba ka da hurumin tsananta bincike akan yadda ta riƙe sha'awarta.


Idan ka ba wa abokinka hoto a waya ya gani kuma sai ya ci gaba da dudduba wasu hotunan ka rage yarda da shi da ka yi.


Maza na son mace mai biyayya fiye da yadda suke son jima'i, shiyasa wasu mazan suke ajiye kyakkyawar mace mai sura a waje su ƙi aurenta amma kuma suke auren mace mummuna mara ƙira indai tana kwantar musu da hankali.


Mace na son namiji mai ƙarfin hali da naci akan burikansu kuma wanda zai iya saurin rabuwa da ita cikin sauƙi.


Kaso 70 na maza suna soyayya ne da mace daidai ajinsu, haka kuma suna auren mace ne daidai ajinsu.


Mata ba kamar maza ba suna soyayya ne da ƙasa da su ko wanda ya fi su aji zai wahala ka ga mace na soyayya da daidai ita.


Idan kana son ka gane halin mutum lokaci guda ka ba shi rabon abincin taron mutane, wanda ya ɓoye abincin da zai ci kafin ya fara rabo azzalumi ne kada ka ba shi amana, wanda ya fara rabawa sai da abincin ya je tsakiya ya ware wanda zai ci wannan komai zai iya faruwa, zai iya cin amana zai kuma iya riƙe amana.


Wanda ya rabawa mutane sannan ya fara neman wanda zai ci wannan zai riƙe amana da kaso 70 cikin ɗari.


Mazan jigawa suna ƙaunar mace mai ƙaton bille a kumatu.


Kada ka tambayi mace shekarunta sai idan ita ce ta gaya maka.

Saturday, 22 February 2025

Matsalar Soyayya Da Namiji Mara Uzuri

Matsalar Soyayya Da Namiji Mara Uzuri

Idan kina nuna masa gaskiya, ya ce kin cika gardama, idan kuma kin yi shiru ya ce ke munafuka ce.


Matsalar soyayya da namiji mara uzuri
Hoto: Unair

Marubuci:- Ridwan Khan Adam


Idan ya kira ki a waya tana kashe, sai ya ɗauka kina tare da wani ne, sai ya aika miki da saƙo cewa, “Kar ki gaya min ba caji, don na san haka za ki ce”.


Idan kin nuna kin damu da shi ya dinga cewa kin fiye son sa da yawa, idan kuma kika nuna ba ki damu da shi sosai ba, ya ce kina da girman kai.


Idan ba ki son sa, ya yi ƙoƙarin yi miki asiri, in kuma kina son sa, ya miki wulaƙanci.


Ida kin cika kwalliya, ya ce kina janyo hankalin wasu maza, idan kuma ba kya kwalliya ya ce ke 'yar ƙauye ce.

Wednesday, 8 January 2025

Ɓata Lokaci A Soyayya

Ɓata Lokaci A Soyayya

Ka ga yarinyar nan da kake soyayya da ita yanzu, tana da damar samun ingantacciyar rayuwa fiye da kai.


Ɓata Lokaci A Soyayya
Hoto: Vecteezy

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Wannan shi ne dalilin da ya sa bai kamata ka ƙarar da duk ƙuruciyar ka ba don gina dangantaka kawai da mace ba.


Maganar gaskiya za ta iya rabuwa da kai  cikin sauƙi ta samu wanda ya fi ka ko wanda ya riga ya shiryawa yin aure wanda mata suke yi wa laƙabi da "Ready Made"  Mutumin da ya riga  ya gama ɗora rayuwarsa akan turba, mai kuɗi da isassun kayan aiki.


Lokacin da za ta ware ta bar ka cikin mummunan talauci da tarin tunani kala-kala kamar kanka ya yi bindiga, lokacin za ka gane asarar da ka yi wajen gina soyayya maimakon gina kasuwanci ko koyon wata sana'ar hannun.


Don haka ba kyautuwa ba ne ɓata lokacinka, tunaninka, kuɗinka, akan macen da ka san ba ka da tabbacin aurenta kuma ba ka da damar aurenta. 


Ita mace ba ta da asara kamar namiji a irin soyayyar nan don kuwa ita lokaci ne kawai take ɓatawa shi kuwa namiji yana rasa abubuwa da yawa, kamar kuɗi, rashin maida hankali wajen neman kuɗin kansa.


Ka san da cewa mata suna maleji ne da maza idan ba su samu wanda ya fi wanda suke tare da shi ba, da zarar ta samu wanda ya fi ka za ta iya barin ka da karyayyiyar zuciya, da rashin manufa a rayuwarka.


Lokacin za ka gane kuskuren da ka yi na ba wa soyayya dukkan ƙarfinka da tunaninka da lokacinka, don kuwa ita ta samu wani wanda ya fi ka hali da rufin asiri tuni zai tsame rayuwarta daga ƙuncin da kuke ciki ya aure ta kai kuwa fa? Idan ba kai da kanka ba ba ka da wani mataimaki sai Lillahi.


Wannan shi ne dalilin da ya sa a matsayinka na matashi, ba lallai ba ne ka yi amfani da duk lokacinka wajen maida hankali da bin mata da neman soyayyarsu ba, kana ta bin su kamar karen da ya ga sabon ɓarawo. Mata su kansu suna ƙaunar namiji ne wanda ke da manufar da ya sa a gaba ba mai iya tsara kalaman soyayya ba kawai da yawan kiraye-kirayen waya ba.


Ka himmatu da gina kanka, ka ɗauki rayuwarka da muhimmanci, karanta littattafai, koyon sababbin abubuwa, yadda za ka haɓaka sana'arka, sa ka hannun jari da sauran su.


A ƙarshen wannan shi ne kawai abin da ba zai taɓa barin ka ba, a lokacin farin ciki da na baƙin ciki.

Monday, 30 December 2024

Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi

Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi

Abubuwa biyar yana da kyau duk wani matashi ya sani kuma ya kiyaye su. Idan kai matashi ne ya kamata ka san waɗannan abubuwa biyar ɗin.


Ga su kamar haka:


 1. Lokaci


A halin da kake kana cikin wani lokaci ne wanda Allah ya ware maka na musamman a rayuwarka, ƙarfin ka ya kai ƙarfi, tsokar jikinka da gaɓoɓin jikinka duk suna nan lafiya, sannan ƙwaƙwalwarka na saurin yanke shawara.


Ƙaramin yaro ba zai samu wannan damar ba, sannan tsohon mutum ba zai samu ba sai kai.


Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi
Hoto: Adobe Stock

Marubuci:- Khalid A Gombe


Duk abin da za ka nema ka neme shi a wannan lokacin kada ka bari lokacin ya wuce maka. Da zarar ka kai shekaru 20 to kana da sauran shekaru 20 da Allah ya albarkace ka da su.


Ka nemi duniyarka da lahirarka ba tare da  gajiya ba.


2. Abokai


Ka zagaye kanka da abokai nagari waɗanda suke da natsuwa. Zama da mutum na gari zai sanya ka zama nagari.


Duk yadda mutumin banza yake son ka da abota kada ka sake ka yi abota da shi. Ka yi abota da mutanen da suka yi nasarar rayuwa, kai ma za ka yi nasara.


3. Zamani


Ka kula da zamani sosai domin shi ne abin da ya fi ruɗar mutane. Idan ka ga ana yayin wani abu sai ka ji kana son mallakar abin.


Kada ka mallaki abu don kawai ana yayin sa ko don ka burge wani, ka mallaki abu domin kana da buƙatar abin kuma domin amfanin da abin zai maka.


4. Ka maida hankali


Kada ka zama mai sa'ido akan harkokin wani maimakon haka ka maida hankali wajen tafiyar da naka harkokin.


Matuƙar kana so ka ci gaba to dole sai ka daina shiga abin da bai shafe ka ba. Ka yi ƙoƙarin gano laifinka kuma ka gyara laifin ya fi ka dinga bincikar laifin wani.


5. Haƙuri


A duk abin da kake nema to ka sani haƙuri ne kaɗai zai ba ka abin.


Kada ka damu don abokanka sun riga ka samun arziki kai ma naka na zuwa a lokacin da ya dace.


Wani zai iya riga ka aure kuma ka riga shi haihuwa haka wani zai riga ka samun arziki amma ka zo ka fi sa arzikin. Don haka ka kwantar da hankalinka lokacinka zai zo.

Friday, 27 December 2024

Matsalar Matan Hausawa A Soyayya

Matsalar Matan Hausawa A Soyayya

Akwai ƙananun abubuwa da suke sa namiji ya ji yana bala'in son mace wallahi, amma matan Hausawa ba su ankare da su ba kuma sam ba su ba su muhimmanci ba, su kawai burinsu a yi ta zuba kalaman soyayya kuma namiji ya yi ta musu hidima kamar sun siyo bawa a kasuwa.


Matsalar Matan Hausawa A Soyayya
Hoto: Zawaj

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Akwai abubuwa da yawa wanda za ki ja hankalin namiji wanda wallahi mai raba ku sai rabbul samawa wati ina magana akan 'yammata ne ba masu aure ba.


Yi masa 'yar kyauta kamar saya masa maɓalli hannun riga (Links), ɗan turare, 'yar hula mara tsada,  ɗan silifas ko na shiga wanka ne, na taɓa wata budurwa da take saya min irin waɗannan abubuwan duk da na san cewa hidimar da nake mata ta fi abin da take min wallahi duk abin da ta saya mini sai na ji na fi sonsa akan wanda na saya da kuɗina koda kuwa ya fi nata tsada.


Mun sani cewa mata mugayen marowata ne shi ya sa namiji yake tabbatarwa duk macen da ya ci kuɗinta koda kaɗan ne to ya tabbatar tana son sa da gaske ba wasa ba.


Amma matan Hausawa ba su cika wannan ba sai wadda wayewarta ta kai, su burinsu su yi ta karɓar naka kamar tsofaffun almajirai, ko kuma sun yi ƙoƙari su girka maka wata bushashshiyar dafaduka (Jallop) ko mai bai ishe ta ba da wani lemo ɗan haɗi, kuma wasunsu da wata manufa suke yi.


Idan kina da hali wani lokacin ki turawa saurayinki kati ko data shi ma fa mutum ne akwai lokacin da yake buƙatar su kuma wallahi ba shi da ko sisi haka zai ji son ki ya ƙara ƙaruwa a ransa.

Tuesday, 17 December 2024

Gajerun Kalaman Hikima Na Rayuwa

Gajerun Kalaman Hikima Na Rayuwa

Abokina kada ka damu don ka rasa wanda zai kula da kai a rayuwa, domin mutane da dama sun kasa kulawa da kansu ma ballantana kuma har su kula da wani, kai dai kawai ka damu da kanka.


Gajerun kalaman hikima na rayuwa
Hoto: UCSF

Marubuci:- El-Nass


Mutanen kirki tamkar bishiyar mangwaro suke, a yayin da kake jifansa shi kuma a lokacin yake sako ma 'ya'yan shi masu zaƙi domin ka sha.


Kada ka zama mai ƙyashi da hassada ga samun wani, domin ba za ka mutu ba har sai ka samu duk abin da Allah ya yi nufi za ka samu a duniya.


Ba laifin ka ba ne ka zama mummuna ta fuskar halitta, ko ka zama talaka domin ba kai ka yi kanka ba, Allah ne ya so ya gan ka a haka amma laifin ka ne ka zama mai mummunan hali domin hali shi ne mutum.


Mace na iya yafe maka duk laifin da kai mata amma ban da laifi ɗaya wato shi ne laifin rashin ba ta kulawa ta fuskar soyayya.


Ni ma anan zan iya yafewa duk wanda ya yi mini laifi ta fuskar zamantakewa amma ban da cin amana.


Duk wanda ya ce zo mu zauna to masoyinka ne kada ka sake shi.


Kada ka damu don ka rasa wani abu mai kyau wanda kake so, sau da yawa sai ka rasa abu mai kyau sannan kake samun mafi kyau.


Ka zama mai ra'ayin kanka domin ka rayu a kan abinda kake so, idan har ka rayu akan ra'arin wani har ka mutu burinka ba zai cika ba domin kuwa ba ka rayu akan ra'ayinka ba.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.


Allah ka ba mu abokan zama na gari Amin.

Monday, 9 December 2024

Kafin Fara Magana Da 'Yammata Ku Duba Wannan

Kafin Fara Magana Da 'Yammata Ku Duba Wannan

1. 'Yammata sun fi damuwa da saurayin da suka ga 'yammata 'yan uwansu yana birge su.


2. "Yammata sun fi soyayya da wanda ya fi ƙoƙarin guje musu.


3. Kowacce yarinya tana jin daɗi yayinda ƙawayenta suka yaba wani abu game da saurayin da take so


Kafin Fara Magana Da 'Yammata Ku Duba Wannan
Hoto: Atikinka2/ISTOCK PHOTO

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


4. Kowacce yarinya ta na yin wasu ɗabi'u kamar na ƙaramar yarinya, idan tana tare da wanda ta fi so.


5. Duk girman mace tana matuƙar son mijinta ko wanda take so ya dinga yi mata kallon ƙaramar yarinya.


6. Idan yarinya ta yi maka girki to alamu ya nuna ta damu da kai.


7. 'Yammata suna fara son su ga sun aure ka ne idan suka gamsu da asalinka.


8. Ka guji yarinyar da mahaifinta bai ba ta kulawa ba a matsayin sa na mahaifi, yawancinsu su kan tsani maza har ƙarshen rayuwarsu. Kuma ba komai za ka yi mata ya burge ta ba.


9. Kyawawan 'yammata sun fi sha'awar samari masu tsafta sosai.


10. Idan yarinya tana matuƙar son ka, za ta dinga duba bayananka na shafukan sada zumunta wato social media akai-akai.


11. Kowacce yarinya tana sha'awar a ce yau tana kula da namiji tare da mu'amalantar sa.


12. Kowacce yarinya ta san abin da saurayi ke ƙoƙarin faɗa, kawai tana basarwa ne don jan aji.


13.Idan soyayya ta kama mace tana ɗabi'antar masoyinta da ɗabi'u irin na uwa.


14. Idan yarinya tana son saurayi da gaske to ta kan gaya masa idan wani saurayin ya nemi yin lalata da ita.

Friday, 15 November 2024

Bambancin Soyayyar Mace Da Soyayyar Namiji

Bambancin Soyayyar Mace Da Soyayyar Namiji

Ya kai Ɗan Saurayi ka sani soyayyar da mace ke yi wa namiji ba irin ta namiji ke yi wa mace ba.


Bambancin Soyayyar Mace Da Soyayyar Namiji
Hoto: Set my wed/Pinterest 


Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ga abun dalla-dalla:


Mace


Mace tana son namiji ne don zai biya mata buƙatunta na yau da kullum, kamar ci da sha sutura, kiwon lafiya, da muhalli mai kyau har da bonus wato garaɓasa na kuɗi idan ta samu, wanda dukkanin wannan idan babu kuɗi so kawai ba zai gamsar ba.


Namiji


Namiji shi kuma yana son mace ne saboda halittar da Allah ya yi masa na buƙatuwa da ita a tsarin halittarsa, ita ma mace tana da wannan buƙatar, don haka ko ba kuɗi namiji zai iya zama da mace yayin da ita kuma mace idan babu kuɗin biyan waɗancan buƙatu nata zamanta da namiji ba zai yiwu ba.

Sunday, 10 November 2024

Alaƙar Ɗabi'un Mace Da Na Mahaifiyar Ta A Soyayya Ko A Aure

Alaƙar Ɗabi'un Mace Da Na Mahaifiyar Ta A Soyayya Ko A Aure

Yadda take magana


'Ya tana ɗauko yadda mahaifiyarta ke magana ne a yawancin lokuta ban ce kowacce ba amma kaso 99 na 'ya'ya mata suna magana yadda mahaifansu mata ke magana ba wai murya ba sam, ina nufin idan uwa masifaffiya ce to haka za ta taso da magana kamar ana yaƙi babu tausasawa, kuma haka za ta dinga yi maka idan kuka samu saɓani maƙwabcinku na uku ma sai ya jiyo abinda ake yi daga gidansa.


Alaƙar ɗabi'un mace da na mahaifiyarta a soyayya ko a zamantakewar aure
Hoto: Rahhal/Shutterstock

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Matuƙar da gaske kake so za ka auri mace to ka tabbatar ka san wasu da yawa daga halayyar mahaifiyarta.


Eh mahaifiyarta nake maka magana wadda ta haife ta za ka ji abun kamar izgilanci sam ba haka ba ne.


Saboda akwai halayen da 'ya mace take ɗauka wajen mahaifiyarta ko ana ha maza ha mata dole sai ta kwaso wannan halayyar matuƙar ita ta haifetan kuma ita ta tarbiyyantar da ita.


Kada soyayya ta rufe maka ido, soyayya kawai zallar ta ba ta iya riƙe aure har zuwa shekara da shekaru.


Tsara kashe kuɗi


Kaso 100 na halayyar mata suna gado mahaifansu mata ne ta ɓangaren almubazzaranci ko alkinta kuɗi. Idan surukarka almubazzara ce to matarka ma haka take kwabo da kwabo, haka idan surukarka ta iya tsumi da tanadi haka matarka za ta kasance.


Dabara da wayo da fasahar magana 


Kusan kaso 80 na mata suna kwaso dabara da wayo na mahaifansu mata ne, tun daga dabarar iya sarrafa abinci da wayon zama da miji, da fasahar magana.


Haƙuri da juriya


Kaso 90 na haƙurin mace tana kwaso shi ne daga wajen mahaifiyarta haka juriyar zaman gidan miji.


Mu'amala


Dukkan ɗabi'u na mu'amala da mutane  mace tana kwaso su ne daga wajen mahaifiyarta, idan babarta tana da mu'amala kyakykawa da mutane haka 'yar ta za ta taso.


Bari na fito maka a mutum idan surukarka ba ta da kyakyawar mu'amala da dangin mijinta wato dangin baban matarka kenan, to ina tabbatar maka ita ma matarka ba za ta gina kyakyawar mu'mala da danginka ba saboda ta taso a gida ta ga mahaifiyarta haka take. Don haka ita ma ba za ta maida hankali wajen damuwa da su ko girmama su ba.


Kula da gida


Wannan babu ja yadda surukarka take wajen tsaftace gida da kula da gida haka matarka za ta kasance a gidanka. Idan babarta ƙazama ce wajen kula da gida haka za ta zo gidanka ta yi ta ƙazantarta, idan kuma ka yi sa'a kuma surukarka mai tsaftace haka matarka za ta kasance.


Don haka idan za ka nemi aure a gida ka yi ƙoƙari ka san halayyar surukarka domin kuwa ita ce halayyar da matarka za ta kasance ciki idan ka aure ta.

Saturday, 9 November 2024

Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi

Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi

Idan kana da burin da kake son cimmawa, sai kuma ya zama abokai da makusanta ba sa mara maka baya, to ka sani ba haƙƙin ka ba ne a kansu sai sun mara maka baya, duk da cewa ya kyautu su yi hakan, hasali wannan jarrabawa ce mai fayyace cancantar ka a kan wannan buri ko akasin haka.


Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi
Hoto: Psychowellness center

Marubuci:- Buzu Danfillo


Shin za ka iya tsaya wa kanka yayin da hatta na kusa da kai sun yi wasarere da mafarkin ka ko burin ka? Ko kuma nasarar ka ta raja'a ne a kan ra'ayoyin waɗanda ba su da fahimta ko ilimi akan abun da ka sa a gaba? Wannan jarrabawa ba tsakanin kai da su ba ne, tsakanin kanka da kanka ne.


Za ka iya hawa hanyar muradin ka kai kaɗai ko sai da 'yan rakiya?


Yadda ba dole ba ne sai sun mara maka baya, kai ma ba dole ba ne sai ka yi da su, ba a shafi ɗaya kuke ba, hakazalika ba amo ɗaya kuke yi kai da su ba, don haka ba za ku taɓa fuskantar juna ba.


Yayin da ƙasa ta ƙi karɓar shuka ba shukar ake sauyawa ba, ƙasar ake sauyawa don haka idan mafarkin ka ko burin ka ya ƙi shukuwa a ƙasar gaban ka, to tuge shukarka ka nema mata ƙasar da za ta girmar da ita, babu riƙo ba ƙullaceceniya. 


Sai dai zuwa gaba idan ka yi nasara, kada ka ba kowannen su damar haskawa tare da kai wato shining da kai. Irin "Ai wane ga gidan mu ga gidan su". Ɗin nan. Kawai ka fuske irin na rashin ganewa ɗin nan, ehi.


Waɗanda suka fi mu ci gaba a duk faɗin duniya ba basira ko baiwa suka fi mu ba, tsari, ɗabi'a da ɗa'a suka fi mu.


Baiwa da Fikira ba su da al'umma, addini, jinsi, ƙabila, yare/harshe ko ƙasa. Lamunci hakan ka samu sa'ada.

Saturday, 26 October 2024

Shin A Zahiri Akwai So Ko Duk Ƙarya Ce?

Shin A Zahiri Akwai So Ko Duk Ƙarya Ce?

In dai akwai wani abu wai shi dangi na so, to ina son yake, kuma yaya yake? Ni dai ra'ayina tuni na fidda a fili domin kuwa ni a tawa fahimtar ba wani abu wai shi so, Malumfashi (1988).


Shin so da soyayya na ƙulluwa ne a lokacin da aka yi aure?
Hoto: About Islam

Marubuci:- Ibrahim Malumfashi


Sai dai kar ka ɗauka na ci kubeji a wannan ra'ayi nawa, domin kuwa masanin Falsafar nan Schopenhaber kamar yadda ya yi bayani a cikin Encyclopedia of Philosophy, yana mai ganin cewa ba wani abu wai shi so a tsakanin mutane, sai dai a tsakanin mutum da mahalicci. Wannan ne ya sa yake faɗar cewa, mawaƙa da marubuta Larabci na ɓata lokacin su ne kawai wajen rubutu, domin kuwa abin da suke ma laƙabi da so, ba so ba ne, sai zagi, cin mutunci, batunci/ɓatanci, kisa da sauran munanan al'amura, wanda kamar yadda ya bayyana, hakan na faruwa ne saboda mawaƙa da marubuta sun maido so a matsayin saduwa a tsakanin mace da namiji.

 

Na san za a so a san dalilin da ya sa na ɗau wannan tsattsauran matsayi, to kada mu nemi kai ruwa rana. In dai so shi ne ƙawa-zuci a tsakanin mutane da abubuwa, to me ya sa a kullum na dubi rayuwarmu ta yau da kullum sai yawan yaji mata ke yi, sai tashin hankali a tsakanin ma'aura? Shin me ya sa, yawancin waɗanda ake ce wa masoya, in ka kalle su; sai ka ɗauka aradu ce ta faɗa musu? 

 

In dai akwai so, ta yaya kullum muke ta fama da tsintattun 'ya'ya da uwayensu suka yi watsi da su, bayan haihuwa? Mace nawa muke jin a yau za ta yi da-na-sani dangane da auren mijinta (wanda a da take matuƙar so)? Shin mazaje nawa ne yau za ka ji na faɗar, ai gidan bai shigo, domin kurar nan, na ciki (ita fa ce masoyiyar)? Yau maza nawa ke a asibitin mahaukata, saboda irin kisan mummuken da matansu (masoyansu?) Suka yi musu a gida? Shin nawa ne daga cikin mutane muka ji sun ɓata, saboda so, so fa ne ke sa ai kisa! Na ga wadda mijinta ya watsa mata fetur, alhali kafin su yi aure, ta fi farin wata haske a wajensa. Na ga mai ƙafa ɗaya. Na ga mai fasasshen kai. Na ga mai ido ɗaya. Na ga mai fasassar mota. Na ga mai yagaggar riga. Na ga wadda ta daɓa wa mijinta wuƙar fawa. Na ga wadda ta ƙone mijin ƙurmus. Duk wai saboda me? So!

 

Shi kuwa wannan abu so, zan so in gan shi, don kuwa ko bom ya shafa masa lafiya wajen ɓarna. Wai ma mun manta cewa, karuwa mai neman maza da mace mai maɗigo, da namiji mai neman mata, da namiji mai yin luwaɗi, duk bisa ginin so suke waɗannan abubuwa? Shin mazinaci da mazinaciya, masu aure da marasa aure, shin me ke kai su ga haka, so! Kai lallai da sake game da fahimtar da ake da ita ta so da kuma soyayya. 

 

Kuma lallai in har biyan buƙata ba shi ne so ba, a'a shi dai ne ƙololuwar so, to ina son yake? In an ce taɗi da zance da hira da namiji ke yi da mace kafin su yi aure ko su sadu (ba ta hanyar aure ba), waɗannan matakai na kai wa ga so, to ina son yake? Ni a nawa ɗan guntun tunanin, sai na ga cewa, batun da ake yi na cewa akwai so har iri huɗu: 

 

1. Na so-an-so (Soyayya).

2. Na-so-an-ƙi (Soƙiyayya).

3. Na-ƙi-an-so (Ƙisoyayya).

4. Na-ƙi-an-ki (Ƙiyayya).

 

Waɗannan abubuwa ba su bayyana mana mene ne so ba, in har ka-so-an- so, wato soyayya ta ƙullu, mene ne son, shin dariyar da macen ta yi maka, ko kuwa amsar da ta yi maka hannu bibiyu, ko kuma amsawa da ta yi ni ma ina son ka, shi ne so da soyayya? Me ka so, me ta so, kuma yaya son yake? Shin so shi ne biyan buƙata, kashe zalaƙar zuci, ko kuwa kwanciyar hankali? In dai waɗannan su ne so, to me ke kawo bala'i da tashin hankali a ranar da mutum bai kai ga manufarsa ba? Sai dai in ba daɗi ba ne so, sai dai bala'i. Ni dai har yau biɗa nake ko akwai wanda ya ga so, ya kawo mini shi zan ba shi kyauta, domin kamo mana wannan mugun abu don mu yi gaba da shi daga rayuwarmu.

 

Na faɗi haka ne don ganin cewa ban ga wanda ya sami so ba hankalinsa kwance, ko nata kwance. Shin akwai wanda ya taɓa ganin waɗanda suke soyayya suka kwashe ƙalau? Shin tatsuniyarmu kullum tana wuce ta Laila da Majnun ko Romeo da Jullet? Kai ai nan da sake don ko waɗannan ba soyayya suka yi ba, sai wahalar da kai da hauka.


Manta da waɗancan ma, dawo nan kusa, shin ka taɓa ko kin taɓa tambayar ma'aurata biyu da suka shekara 20 tare, suka faɗa maku/muku cewa ai soyayya ƙalau, in ma da akwai ta? Ƙila wani ya ce ai ba so sai na uwa da ɗanta, ƙila kai a wurinka, ai mahaifiyarka abin so ce abin ƙauna ce, kuma ba wadda kake so irin ta, amma shin ka taɓa tambayar mahaifinka ka ji irin zafin da take ba shi? Don haka ba ni jin cewa lallai akwai so, tatsuniya ce kaɗai, ba batun gaskiya a ciki? 

 

Mu yi tunani bisa wannan batu fa da kyau. Me ke sa mace ta ce wai ta mace wa yaro. Me ke sa yaro ya sami yarinya ya dinga zabga mata ƙarya, ke ce rayuwata, ke ce abin tunanina, ke ce abin ƙaunata, ke ce tauraruwata, ke ce zan so da ƙauna, sai mutuwa ka raba. Ana ɗaura musu auren, tana tarewa, tana haihuwa, sai ka ji ya fara 'yar murya, ni fa amarya zan yo?  

 

Me ya sa mace za ta auri namiji su yi shekara 20 tare, suna ta soyayya, amma ranar da Azara'ilu ya zo ya ɗauke mijin, sai 'yan koke-koke da 'yan murje-murjen ƙarya, bayan 'yan watanni sai ka ji ta sake wani auren? Shin wannan shi ne so da soyayya? Me zai hana ta zauna ba aure har abada tun da shi marayin/ɓarayin rayuwar ya tafi?

 

Shin nawa daga cikinmu (maza) muke turke yarinya muna faɗa mata, ni in ba ke ba sai dai rijiya. In ba ke ba masai. Ni in ban same ki ba, rayuwata ta lalace. A buga, a raya, a kuma yi tattaki bai same ta ɗin ba. Wani can ya aure ta. Amma wannan bawan Allah bai faɗa masan ba, bai faɗa rijiyar ba, bai kashe kansa ba. Can sai ka ji ya faɗa neman wata can daban, idan aka yi sa'a kuma ya same ta, sai ka ji yana faɗar, rashin wance da na yi, ai ɓata lokaci ne kaɗai, idan mata ne ba ga su nan kamar jamfa a Jos ba. Ni kuma na ce ai ka san da su a jamfa a Jos ɗin, amma ka liƙe wa wancan ɗin da ba ka samu ba. Shin so shi ne ƙarya in har akwai shi? Shin wai mene ne so? Ina kuma yake? Yaya kamarsa  take? 

 

Mai sauraro shin me kyarkyarar zakara ke nunawa gare mu? Shin me barbarar taure ke neman fahimtar da mu? Kana jin cewa ba su kama da ƙaryar da namiji ke yi wa mace da zaran ta saki jikinta da shi, gobe sai ka ji ya sake  sheƙa? 

 

Shin so da soyayya na ƙulluwa ne a lokacin da aka yi aure? Shin soyayyar da ba ta kai ga aure ba me za a kira ta? Wahala ko soyayya? Shin mene ne bambanci tsakanin tsarkakakkiya da kuma ɓatacciya? Shin wai don an nemi yarinya an kuma sadu da ita, soyayyar ta ɓaci ke nan? Ana nufin cewa duk irin soyayyar wai da ke nan tsakanin mace da namiji wadda ba ta kai ga aure ba, ita ba soyayya ba ce? Idan haka ne ashe su dabbobi da ƙwari da tsirrai su ba su da so balle soyayya? Don kuwa ba a taɓa ban goro ba aka ce mana an ɗaura aure a tsakanin akuyar gidan Malam Mande da ɗan akuyar gidan Malam Mati.


Ashe mai karatu darbejiyar/dalbijiyar ƙofar gidan Malam Musa na da miji ni ban sani ba. In dai ba su da aure irin wanda muka sani, to mene ne soyayya in akwai ta? A bisa gaskiya zan so na sami bayani game da yadda soyayyar taure, in har akwai ta, take? Ƙila kuma tashi ma soyayyar ta aure ce. In kuwa ta aure ce, shin wace ce matar tasa, mahaifiyarsa? Ƙanwarsa? 'Yarsa ko kuma ɗiyar da ya haifa? Wai shin mene ne so in har akwai shi? Kala yake canzawa kamar hawainiya duk lokacin da ya ji ya gaji da waccen kalar, ko kuma kamar dala yake, tsuntsuwar nan mai ɗauke da launi-launi a jikinta a lokaci guda, in fa akwai shi, ina nan jira ina kuma saurare!

Wednesday, 23 October 2024

Alamomi 12 Na Tabbatarwa Mace Ta Kamu Da Tsantsar Soyayyar Ku

Alamomi 12 Na Tabbatarwa Mace Ta Kamu Da Tsantsar Soyayyar Ku

Idan mace ba ta yi maka waɗannan halaye  da zan lissafa to ka cire kanka daga cikin wanda take so, kuma ka nisance ta babu soyayyarka sam a ran ta.


Alamun Mace Ta Kamu Da Tsantsar Soyayyar Ku
Hoto: Fizkes/Shutterstock

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


1. Ta ƙi ɓoye maka labarai na halayenta, da ɗabi'unta munana da kyawawa da makamancin abubuwa masu muni da masu kyau da suka faru da ita a rayuwa.


2. Sannan Duk abin da za ta yi takan tuntuɓi shawararka ko ya shafe ka ne ko bai shafeka ba, koda a kan ƙawayenta ko akan iyayenta ne.


3. Ta dinga ƙarfafa maka gwiwa akan sana'ar da kake yi ko kasuwanci, da kuma ƙoƙarin sanin komai da ya dangance ka da duk wani motsinka.


4. Ta dinga tsara yadda rayuwarta za ta kasance anan gaba da kai, kowanne tsarin rayuwarta idan ta faɗa za ka ji tana sako ka a ciki.


5. Ta dinga tsawatar maka akan abu kaɗan kamar jinjirin yaro misali, ta ce "Dan Allah ka daina zuwa filin ball ɗin nan wallahi ba na son aji maka ciwo ne". Da irin dai maganganu na nuna cewa ba ta son wani abu ya same ka ko ta ce idan za ka zo yau kada ka biyo ta bayan layi wallahi wani gida sun kawo kare yana nan yana ta haushi.


6. Ta dinga kambama ka a loƙacin da kai kanka ka tabbatar ba ka cancanci a yaba maka ba.


7. Ta dinga zancen wasu samari a gabanka wai dan ta tabbatar kana kishinta ne ko a'a.


8. Abu kaɗan idan ka yi ko ba na dariya ba ne sai ka ga yana ba ta dariya.


9. Ta dinga riƙe zantukan da kuka yi da ita koda an daɗe.


10. Ta dinga ƙoƙarin zama wata mara wayo a gabanka idan kuna magana.


11. Ta dinga kwaikwayon wasu kalamanka wanda kake gaya mata da kuma yadda kake motsi idan kana magana.


12. Ta dinga neman shawararka akan abu ƙalilan wanda ba ma ya buƙatar sai ta nemi shawararka kamar tace "Baby yau zan je unguwa ya kake gani na saka wannan atamfar wadda ka zo zance ranar juma'a ka same ni da ita?".


Idan dole sai ka dinga ba ta kuɗi kafin ka samu kulawarta sosai, malam ba budurwarka ba ce haya kawai kake ɗaukarta. Ka cire ƙaya ka huta.


Idan ba ka samun waɗannan halaye daga budurwarka, kawai ka yi ritaya da soyayyar.

Thursday, 19 September 2024

Abubuwa 20 Na Yadda Za Ka Martaba Kanka A Cikin Jama'a

Abubuwa 20 Na Yadda Za Ka Martaba Kanka A Cikin Jama'a

Sanin waɗannan abubuwa ashirin ɗin za su taimake ku a rayuwa.


 1. Kada ka je inda ba a gayyace ka ba.  Kuma idan an gayyace ka, kada ka wuce gona da iri.


Abubuwa 20 Na Yadda Za Ka Martaba Kanka A Cikin Jama'a
Hoto: Business insider


Marubuci:- Idris Abubakar Idrisia


 2. Ka daina maula a wajen mutane.


 3. Ka daina surutu fiye da yaddda ya kamata.


4. Idan mutum ya wulaƙanta ka, koda a rashin sani ne, ka sanar da shi kaitsaye.


5. Kada ka ci abincin mutane fiye da yadda suke cin naka.


6. Ka rage yadda kake ziyartar wasu. Musamman idan su ba sa ziyartar ka.


7. Ka zuba jari, koda kuwa ba yawa.  Ka farantawa kanka rai ba sai ka dogara da wani ba.


8. Ka daina yin maganar wasu mutanen, idan ba sa wajen.


9. Ka yi tunani kafin ka yi magana. Kashi 80% na yadda mutane ke daraja ka shi ne ta abin da ke yawan fitowa daga bakin ka.


10. Koyaushe ka zama mafi kyawu. Ma'ana cikin tsafta. Ka kasance cikin ado da kwalliya yadda ya kamata.

 

11. Ka kasance mai yawan kyauta. Ka shagaltu da cimma burin ka.


12. Ka girmama lokacinka.


13. Kada ka zauna a cikin mutane da dangi wanda ba su ɗaukar ka da kima.  Ka tafi ka bar su.


14. Ka koyi kashe kuɗi a kan kanka.  Ta haka ne mutane za su amfane ka kuma su ba ka girma.


15. Ka kasance mai rauni wani lokacin.


16. Ka kasance mai bayarwa fiye da mai karɓa.


17. Ka daina neman wanda ba ya nemanka.


18. Kake yi wa mutane daidai da abin da suka cancanta.


19. Indai mutum ba ya bin ka bashi to zai kira ka a ƙalla sau biyu. Idan har da gaske yana ganin daraja ka.


20. Ka kyautata ga duk abin da ka kasance kana aikatawa.  Kasance mafi kyau.


Allah ka tsare mana mutuncin mu da girman mu, ka wadata mu da arziƙi mara yankewa duniya da lahira.

Saturday, 31 August 2024

Asalin Mace Mai Aji Da Jan-aji

Asalin Mace Mai Aji Da Jan-aji

Mace mai aji ita ce mai zaɓar saurayi guda ɗaya mai son ta da gaskiya ta nuna masa soyayya ta zahiri mai tsafta, wadda babu gaurayen yaudara ko ƙarya a cikin ta.


Mace Mai jan-aji
Hoto: Quora


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Jan-aji ba yana nufin wulaƙanci ba, a'a, yana nuna, mace wadda ta san kanta, ba ballagaza ba wadda take kula kowanne irin namiji ko duk saurayin da ya ce yana son ta.


Ki bayyana wa saurayin da kike so kina son shi, ki kuma nuna masa soyayyar a zahiri, amma kar da gurin nuna masa soyayya ki manta matsayinki na 'ya mace mai daraja wadda a ka san ta da jan-aji.

Friday, 23 August 2024

Karanta Yadda Ake Gina Soyayya Mai Dadi A Tsakanin Budurwa Da Saurayi

Karanta Yadda Ake Gina Soyayya Mai Dadi A Tsakanin Budurwa Da Saurayi

Shin ko kin san yadda ya kamata ki tarbi masoyinki kuwa a lokacin da ya zo wajenki zance? Duk da kin sani akwai buƙatar ki san da cewa da farko kamar yadda kika sani ne, akwai buƙatar ki ɓata lokaci a gaban madubi wajen yi wa saurayinki da kike so kwalliya ta musamman, a dukkan lokacin da ya shirya kawo miki ziyara.


Gina Soyayya Mai Dadi A Tsakanin Budurwa Da Saurayi
Hoto: Nada Yousuf


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Ki zaɓo kaya masu kyau daga cikin kayanki ki yi masa ado da su. Ki kasance mai sanya kayan da za su rufe miki jikinki su fito da ke a macen da ta san abin da take yi kamar yadda na san kin riga kin san da wannan tini, hakan zai sa ki yi kwarjini a cikin idanuwansa.


Bayan kin futo wajensa, tattausan murmushi shi ne abun da za ki fara jifansa da shi, bayan nan sai ki yi masa sallama tare da yi masa barka da zuwa.


Ki kasance mai ƙawata muryarki a yayin da kuke hira, wato ki yi masa magana cikin nutsuwa da kuma furta masa zaɓaɓɓun kalmomi daga cikin bakinki. 


Ki kasance mai mayar masa da amsoshin maganganunsa cikin salo na burgewa kar da ki yawaita ce masa "E, a'a." 


Kar da ki yawaita yin maganganu mara ma'ana a gabansa, ki kame kanki cikin salo na jan-aji.


Kar da ki nuna ƙosawa da jin abun da yake faɗa ko hirar da yake yi miki, a lokacin da kuke tare. 


Idan lokacin da kike son komawa gida ya yi, shi kuma a daidai wannan lokacin sai ya kasance ya na jin daɗin hirar da kuke yi, sai ki sanar da shi kina son za ki koma gida cikin nuna yanayin ba ki so faruwar hakan ba, wato ba ki so rabuwar taku ba a daidai wannan lokaci, har ki ba shi haƙuri gami da sanar da shi za ki kasance cikin kewarsa har zuwa ranar da za ku sake haɗuwa ko ma shi ya ce zai tafi to ki nuna ba ki ji daɗin rabuwar taku ba a daidai wannan lokacin. 


Hakan zai ƙara bayyanar masa da adadin yadda kika damu da shi.


Kar da ki buɗe wa saurayi ƙofar da zai raina ki, ya daina ganin girmanki da kimarki har yake nuna ai ke kike son shi, ba shi ne yake son ki ba, ta hanyar nuna masa azababbiyar soyayya fiye da yanda yake nuna miki domin hakan zai iya sanyawa ya rage kulawar da yake ba ki, yana mai fariya da ai ba za ki iya rabuwa da shi ba.


A dai lokacin da kuke tare, kar da ki manta da yi masa tattausan murmushi, domin kuwa shi zai ke gani a duk lokacin da ya rintse idanuwansa bayan kun nesanta da juna. 


Kar da ki manta da ƙawata muryarki wadda gwalagwalan kalmomi za su ke futa daga cikin ta, domin kuwa ita ce sautin da zai fi maimaituwa a cikin ƙwaƙwalwarsa a dukkan lokacin da zanen kyakkyawar taswirar surarki da ya gan ta cikin ƙawatacciyar kwalliyarki ta bayyana a cikin tunaninsa.


Kar da ki kasance mai yi masa kowacce irin hira. Ki ke tantance labari kafin ki ba shi. Ki kasance mai kama kanki a gabansa. 


Kar da ki yarda ya san wani sirrinki wanda mijinki ne na aure kawai ya kamata ya san shi, ko da kuwa a na saura awa guda a ɗaura muku aure ne, balle a haɗuwarku ta farko ko a rayuwarku ta soyayyar samartaka da 'yammatanci.


Wannan 'yar shawara ce, kar da ku ɗauka iyakacinta kenan. Ku yi hankali da dafin soyayya, domin kuwa ya fi dafin maciji illa.


Ina yi muku fatan alheri.

Thursday, 22 August 2024

Manyan Shubuhohi 8 Na Zamani

Manyan Shubuhohi 8 Na Zamani

A wannan zamani namu babu shubuhohin da suka fi yaɗuwa da karɓuwa a wajen mabiyan Shaiɗan kamar Shubuhohin kore samuwar Allah Ta'ala da ƙaryata dukkannin addinai da kafirce musu , da kuma ƙaryata sahihan hadisan Manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da yin fatali da fannonin iliman Tafsiri da Hadisi da Fiƙhu wajen fahimtar addini. 


Shubuhohi 8 Na Zamani
Hoto: iStock


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Shaiɗan da mabiyansa ba su taɓa yin ƙasa a gwiwa ba wajen ƙago shubuhohi da yaɗa su a cikin al'umma.


Manyan Shubuhohin masu ƙaryta hadisai sahihai na wannan zamani namu su ne: 


1. Da'awar cewa Ƙur'ani kaɗai ya isa a yi musulunci da shi ba sai an haɗa da hadisi ba. 


2. Da'awar cewa wasu hadisan sun saɓawa Ƙur'ani mai girma. 


3. Da'awar cewa wasu hadisan wai sun saɓawa hankali. 


4. Da'awar cewa wai hadisan sun saɓawa ilimin kimiyya. 


5. Da'awar cewa hadisan sun saɓawa tarihi ko kuma abin da yake faruwa a yanzu (واقع) wato lokacin su ya wuce sun yi esfaya (expire)


6. Zargin Sahabbai da Tabi'ai da Malaman hadisi da na Fiƙhu da ƙirƙirar hadisai da hukunce-hukunce don daɗaɗawa Sarakuna da ƙarfafa mulkin su. 


A kan haka har ma kafirta Sahabban suke yi ko ce musu fasiƙai ko munafuƙai ko maƙiya Manzon Allah da iyalansa masu yi masa zagon ƙasa. 


7. Munana zato da shakku akan magabata da tabbatattun nassosi. 


Abu na farko da yake zuwa ran su da sun ji abin da bai kama ƙwaƙwalwar su ba, ko ya saɓawa ra'ayinsu shi ne mummunan zato da shakka da zargi da tuhuma, maimakon binciken inganci ko ma'ana ko manufa ko hikima ko bayani daga masana. 


8. Ba su da wasu magabata managarta ko malamai sai su kan su da kuma tsirarun fanɗararrun mutane da kuma kafirai da suka ƙago shubuhohin suke yaɗa su irin su Mahmud Abu Rayyah , Mabiya addinin Shi'a Goldziher, Morgolioth da sauran su. 

Tuesday, 6 August 2024

Asalin Samuwar Shubuhohi A Musulunci

Asalin Samuwar Shubuhohi A Musulunci

Shubuhohi suna samun asali ne daga: 


1. Jahilci


2. Son zuciya 


3. Kare bidi'a


4. Yaɗa ɓata


5. Son a karkatar da musulmi daga tafarkin sunna. 


Asalin Shubuhohi A Musulunci
Hoto: Depositphotos


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Waɗannan su ne muhimman dalilan da ke haifar da shubuhohi da yaɗawar su a cikin al'umma. 


Yahudu da Nasara da 'yan kanzagin su daga fanɗararrun musulmai masu ƙirƙirar bidi'o'i da yaɗa munanan aƙidu, da munafukai, su ne suke ta fafautukar zaƙulo shubuhohi da ƙera su da yi musu kwalliya tare da yaɗa su. 


Allah Ta'ala ya ce 


يااهل الكتاب لم تلبسون الحق بالباطل وتكتمون الحق وانتم تعلمون


"Ya ku ma'abota littafi me ya sa kuke cuɗanya gaskiya da ƙarya , kuma kuke ɓoye gaskiya alhali kuna sane ? 


Al-Imran : 71. 


Halayen masu yaɗa shubuhohi suna da ban haushi da mamaki ta yadda ƙiriƙiri suke ƙoƙarin ta kowane hali sai sun mayar da baƙin abu ya koma fari, ko kuma su munana fari wai sai ya koma baƙi. 


Ibnul Ƙayyim Rahimahullahu ya ce: 


"Yana daga siffofin munafukai ɓoye gaskiya, da kawo ruɗani ga masu bin gaskiya, da aibata mutane da laifukan da su ne suke aikata su. "


Idan suka ga wasu suna ƙoƙarin hana ɓarna da kawo gyara sai su tsane su, su rinƙa ce musu maɓarnata masu haddasa fitina. Alhali Allah da Manzon sa da dukkannin muminai sun san cewa su ne cikakkun maɓarnata fitinannu.


Idan Malamai magada Annabawa suka kira su zuwa ga littafin Allah da Sunnar Manzon sa sai su rinƙa kiran su da sunan 'yan bidi'a ɓatattu. 


Idan suka gan su ba su damu da abin duniya ba, sai su ce ƙaryar Zuhudu suke yi mayaudara ne. 


Idan suka bayyana gaskiya sai su kawo ƙarerayi su haɗe su da wannan gaskiyar su muzanta wannan gaskiyar a idon jahilai da masu raunin fahimta, don su ruɗa su, su karkatar da su , su hana su fahimta da bin gaskiya. 


Suna ɗauko ƙarya su lulluɓa mata riga ta gaskiya don a yarda da su da wannan ƙaryar ta su. "


(طريق الهجرتين ٦٠٢_٦٠٣)


Wato dai Shubuhohi su ne tushe kuma ƙashin bayan duk wani ɓata da wata bidi'a a wannan duniya, tun daga kan Ibilis har ƙarshen duniya. Ba don shubuhohi ba da ba a samu wani kafirci ko bidi'a ko munafunci ko fasiƙanci ba a duniya.

Friday, 2 August 2024

Karanta Siffofi 11 Na 'Yan Shubuha

Karanta Siffofi 11 Na 'Yan Shubuha

Masu ƙago shubuhohi da yaɗa su sukan ɗaure su a wasu turaku domin nuna cewa su ma suna da hujjoji da dalilai a kan abubuwan da suke faɗa. 


Siffofin Masu Shubuha
Hoto: Seekers guidance


MarubuciAhmad Murtala Mansur


Manyan turakun shubuhohi su ne: 


1. Murguɗa ma'anar ayoyin Alƙur'ani da canja musu fassara idan sun saɓawa ra'ayin su. 


Sau da yawa sukan fake da cewa ba zai yiwu a kafa hujja da zahirin aya ba , sai dai a yi mata Tawili . Sukan fake da amafani da kalmar Majazi (مجاز) musamman kan ayoyin siffofin Allah Ta'ala. 


2. Ƙaryata ingantattun hadisai da yi musu mummunar fassara ta son rai wacce take cike da ɓatanci ga Allah Ta'ala ko Manzon sa ko Alƙur'ani ko Musulunci. Sai kuma su ƙagawa Sahabbai da Malaman musulunci wannan fassarar. 


3. Kafa hujja da hadisan ƙarya da ruɓaɓɓun ruwayoyin tarihi, alhali ga sahihan hadisai da babu wani rikici a cikin su, amma sai su yi fatali da su su maƙalƙalewa waɗannan ruɓaɓɓun. 


4. Cushe a cikin ruwayoyin hadisai da na tarihi, sai su cusa wata kalma ko jumla a cikin ruwayar domin cim ma mummunar manufar su ta kawo ruɗani ga musulmi. 


5. Rusawa babu ginawa. Aikin masu ƙago shubuhohi a kodayaushe shi ne su rusa tabbatattun abubuwa na musulunci ba su gina ba. 


Za su kawo rikici amma ba za su kawo hanyoyin warware shi ba. 


6. Kafa hujja da maganganun kafirai da sauran ɓatattu fanɗararru da goya musu baya. 


7. Cika baki da kuri da da'awar ilimi, da yi wa Malamai ba'a da izgilanci da nunawa mutane cewa su malaman jahilai ne. 


8. Kambama al'amura da zugwigwita su da tayar da ƙura da mayar da allura ta zama garma, da yawan surutu da sunan karatu, duk don su jawo hankalin mutane su saurare su kuma su yarda da su.  


9. Tawaye da tsageranci ga magabata matattu da rayayyu da nuna su a matsayin daƙiƙai , jahilai, maha'inta, gidadawa , maƙaryata da sauran miyagun siffofi domin su raba su da mutane su zama ba sa sauraron kowa sai su kaɗai. 


Da tsaurin ido da cin mutuncin duk wanda ya saɓa musu koda kuwa ya wuce shekaru dubu da mutuwa. 


10. Da'awar jaddada addini da ba shi kariya da tsaftace shi da kuma zamanantar da shi. 


A kan haka suke cewa wai su kare martabar Manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da Muslunci suke yi. 


11. Da'awar jarumta da nuna su ba sa tsoron kowa kuma wai su don Allah suke yin abin da suke yi ba neman suna ko muƙami ko wani abin duniya suke ba. 


Da waɗannan turaku da makamantan su masu yaɗa shubuhohi suke amfani domin ɗaure mabiya da kifa musu kwando su yi ta bin su a makance suna yi musu tafi da jinjina da maimaita waɗannan shubuhohin nasu kamar 'yan amshin Shata. 

Monday, 17 June 2024

Ire-iren Matan Da Za Ku Daina Yin Soyayya Da Su

Ire-iren Matan Da Za Ku Daina Yin Soyayya Da Su

A lokacin da na karanta rubutun Fakihu M.Sani Jingir da yake cewa, "Duk macen da tun kafin ka aure ta, Allah Ya sa ka fahimci cewa, idan ka aure ta akwai yiwuwar za ku rabu, saboda wasu ɗabi'unta waɗanda ba su yi maka ba, ina mai ba ka shawarar ka rabu da ita tun kafin ka aure ta, kada sai bayan ka aure  ta, ta haifo maka 'ya'yan da ba za su girma a ƙarƙashin kulawar uwarsu ba, bayan ka sake ta, daga baya 'ya'yanka su zamar wa al'umma matsala." Na fahimci muna da ra'ayi iri ɗaya.


Ire-iren Matan Da Za Ku Daina Yin Soyayya Da Su
Hoto: The press radio 


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Duk tsananin son da nake yi miki, ban ga amfanin kin ce kina so na, ni ma na ce ina son ki ba, amma tun kafin mu yi aure idan na ce ki bar yin kaza ba za ki bari ba, idan na ce gyara kaza ba za ki gyara ba, idan na ce ki daina kaza sai ki kasa dainawa, idan na ce ba na son kaza, sai ki nuna kamar a lokacin ke kuma  ki ka fara son shi?


Wace irin rayuwar aure kake hango wa waɗannan masoyan idan suka yi aure a haka? Ko kana tunanin za ta yi masa biyayya ta ba shi kulawar da yake buƙata, wadda ta kasa ba shi ita tun suna rayuwar samartaka, lokacin da ake sa ran akwai soyayya tsantsa a tsakaninsu da kunya da kara da kuma haƙuri da juna?


Idan har ka fahimci wadda kake ƙauna, ba za ta iya yi maka abin da kake tsammani daga gare ta ba, idan kun yi aure, irin su; biyayya, ɗaukar shawara, nuna kulawa, damuwa da damuwarka, kuma ka gano akwai wata a gefe da take tsananin ƙaunarka, tana jin maganarka, tana ɗaukar shawarwarinka masu amfani a gare ta, to ina mai ba ka shawara ka zaɓi wannan ta biyun komai muninta, ko ba mai siffarta kake nema ba, ka karɓe ta, ka mutunta ta, ka ba ta kulawa.


Bayan aurenku, za ta bi ka sau-da-ƙafa, za ta riƙe ka, ta ririta ka, za ta ɗauke ka tamkar wani Sarki da za ta rayu a ƙarƙashin inuwarsa, rayuwa ta har abada.


Idan kuwa ka biye wa kyawu, da soyayya ta fatar baki, a ƙarshe za su tafi su bar ka a cikin duhu da cizon yatsa, da yin da-na-sani na tsawon rayuwa, wanda daga ƙarshe sai ɗayanku ya buƙaci SAKI! Domin neman makararriyar mafita, 'ya'yan da kuka haifa su zama marayun ƙarfi da yaji, su gaza samun ingantacciyar rayuwa irin ta iyaye.


Shi aure ba soyayya kawai yake buƙata ba, yana buƙatar fahimtar juna, kyautatawa, da kuma tausayawa daga kowane ɓangare na namijin da na macen, saboda a ƙarshe dole kyawun da ake ji da shi da soyayyar da ake ji da ita, da kunyar da take a tsakani su gushe, sai ya rage saura zaman HAƘURI. 


Wannan ita ce rayuwar kowane gida mai tsari.


Idan har ke da nake ƙauna, fiye da kowace budurwa a faɗin duniya, kina karanta wannan saƙon nawa, ki sani, a duk lokacin da ki ka ji na ce mu rabu, to wannan tunanin shi ne yake zuwa a cikin zuciyata, ba wai don na daina son ki ba ne ba.


Kin kasa sauyawa zuwa yadda nake hasashen za mu iya rayuwa a tare, ba tare da kin cutar da ni ko ni na cutar da ke ba. 


Zan iya jure zafin rabuwa da abin da nake fatan ya zama nawa, amma ba zan iya jure raɗaɗin rabuwa da abin da ya zamo nawa ba, na san zai haifar min da miki mai yaɗuwa a cikin zuciyata da ba shi da magani.


Ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe, don ci gaba da samun zafafan saƙonnin soyayya da kalaman soyayya na saurare da na karantawa.


Allah Ka haɗa mu da mata na-gari, waɗanda za mu yi kwaɗayin ci gaba da rayuwa tare da su, a gidan Aljanna.