Showing posts sorted by date for query M. Kabiru Muhammad. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query M. Kabiru Muhammad. Sort by relevance Show all posts

Thursday, 19 December 2024

Tafi Sama

Tafi Sama

Duk abun da ya yi sama ka jira zuwan shi ƙasa lokacin da zai faɗo ƙasa babu wanda ya san zai faɗo, to haka ma ɗaukaka take zuwa ta kuma tafi lokacin da ba ka tunani.


Tafi Sama
Hoto: Stock Adobe

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Allah ya sa mu dace Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Friday, 6 December 2024

Rasa Komai

Rasa Komai

Za ka iya rasa komai a rayuwa, ka mayar da shi ko mafiyin sa amma ba za ka iya mayar da iyayenka da su riga mu gidan gaskiya ba.


Rasa komai
Hoto: fran kie/Stock Adobe

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Sannan ba za ka iya mayar da duk daƙika ɗaya da ta wuce ba (Duk damar da ta wuce ko kuma duk lokacin da ya wuce ya riga ya tafi kenan) sai dai wani ba shi ba.


Allah ka jiƙan iyayenmu waɗanda suka riga mu gidan gaskiya ka sa Aljanna ce makomar su, idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Saturday, 30 November 2024

Dalilin Mamaki

Dalilin Mamaki

Ba shakka za ka yi matuƙar mamaki fiye da misali idan har abubuwan da ba ka yi tsammani ba suka faru.


Dalilin Mamaki
Hoto: South agency/ISTOCK PHOTO

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kuma yadda duk kake tsammanin ganin su sai ya kasance sun wuce duk yadda kake yin zato.


Ka ga kuwa, daga ƙarshe, lallai ne cewa kalmar 'MAMAKI' ta biyo baya.


Allah ya sa nasarar mu a kodayaushe ta zamo abar da za ta bai wa kowa mamaki Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Thursday, 28 November 2024

Soyayyar Dole Ko Soyayyar Tilastawa

Soyayyar Dole Ko Soyayyar Tilastawa

Shi so ba a yi masa tilas. Duk wanda ya cusawa zuciyarsa abin da ba ta yi na'am da shi ba (Ba ta aminta da shi ba a karan farko) daga ƙarshe ladama/nadama ce za ta biyo baya.


Soyayyar Dole Ko Soyayyar Tilastawa
Hoto: Shutterstock da Salsa 4 life


Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Shi so ba a yi masa dole. Idan ba a son ka, kar ka tsananta, duniya da faɗi, je ka nemi daidai da kai domin a lokacin da wani ya tsane ka, a lokacin wani yake masifar son ka.


Allah ya haɗa mu da masu son mu saboda shi, kuma su guje mu saboda shi Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Tuesday, 26 November 2024

Wanda Ka Raina Shi

Wanda Ka Raina Shi

Wanda ka raina, sai ka ga Allah Ya ɗaukaka shi. Kai dai kawai nema a wajen Allah Maɗaukakin Sarki.


Wanda Ka Raina Shi
Hoto: Namibian

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kar ka tsaya jiran wani ya taimaka maka.


Yi ƙoƙarin ka fahimci abin da kake son cimma a rayuwa.


Kada ka manta ba kowacce dariya ko murmushi da mutane suke yi maka yake zama so ba, amma ka sani a ko'ina ba a rasa na banza, haka ma a ko'ina ne ba a rasa na kirki.


Kai dai kawai miƙa al'amuran ka ga Allah (S.W.T).


Allah ya sa mu dace duniya da lahira Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Sunday, 24 November 2024

Babu Amsa

Babu Amsa

Mu dinga yi wa juna uzuri Dan Allah. Idan  kana ganin mutum a Online kodayaushe, hakan ba ya nufin ba shi da aiki ba ne, don haka kar ka yi masa mummunar fahimta.


Babu amsa
Hoto: Meaww

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Idan kana aikawa da saƙonni ka ga ba a dawo maka da amsa wato Reply, kar ka yi fushi, saboda ba kai kaɗai ba ne kake tura masa da saƙonni. Don haka ka yi masa uzuri.


Idan kana ganin mutum a Online cikin dare 12:00am,1:30am har zuwa 4:00am ko 5:00am, ka tura masa da saƙonni babu Reply wataƙila bacci ne ya ɗauke su.


Da yawa ba sa sanin lokacin da suke barin wayar akan yanar gizo-gizo wato Internet, musamman masu amfani da wayar Android, amma masu amfani da ƙananan wayoyi to su idan suka bar wayar tasu akan yanar gizo-gizo idan aka ɗan jima tana sauke kanta daga kan yanar gizo-gizo har sai dai idan kai ne ka ci-gaba da amfani da ita.


Dan Allah mu rinƙa kyautata kyakykyawar fahimtar junan mu.


ALLAH ya sa mu dace da dacewarsa Amin ya ALLAH.

Monday, 18 November 2024

Kowa Kotu Kawai

Kowa Kotu Kawai

Hmm Nigeria kenan, da an yi magana kotu, kowa idan abu ya yi zafi ba zai iya haƙuri ba sai ya ce "Mu haɗu a kotu.".


Kowa Kotu Kawai
Hoto: Chris Ryan/iStock photo

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kada ka biyewa son zuciya ko kuma abokai masu karancin tunani su kai ka su baro, saboda da yawa daga cikin su suna tare da kai ne domin su cimma manufar su a kanka.


A  ganina duk abin da haƙuri bai bayar da shi ba to tabbas akasin shi ba zai bayar ba.


Idan kai haƙuri komai zai wuce, sannan za ka ga nasara akan haƙurin da ka yi.


Nazari aikin mai hankali.


Allah ya sa mu dace Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Friday, 15 November 2024

Darasi A Rayuwa

Darasi A Rayuwa

Rayuwa gaba-ɗayan ta darasi ce ga mai hankali, haka kuma ilimi ce ga mai tunani da aiki da abin da ya ji ko ya gani, ya san yadda zai tafiyar da shi.


RAYUWA GABA ƊAYAN TA DARASI CE GA MAI HANKALI
Hoto: Be slick

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Duniya kuma makaranta ce, wasu sun yi nasara. Wasu kuma akasin ta.


Allah ya sa muna cikin waɗanda za su yi nasara anan duniya da kuma lahira Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Friday, 8 November 2024

Kyautata Zato Ga Kowa

Kyautata Zato Ga Kowa

Ka kyautata zato ga mutane, wasu lokutan mafi yawancin abin da muke zargi ba gaskiya ba ne.


Kyautata zato ga kowa
Hoto: M. Kabiru Muhammad/Facebook 

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Shiyasa ma a addini aka haramta yin zato (Koda ya kasance gaskiya ne).


Saboda ba a kodayaushe ne yake kasancewa gaskiya ba, kashi 99% duk ƙarya yake kasancewa, ka ga kenan babu amfani.


Allah Yasa Mu da ce

Tuesday, 5 November 2024

Wednesday, 30 October 2024

Saurin Yarda Da Jama'a

Saurin Yarda Da Jama'a

Duk wanda muka haɗu da shi a rayuwata, ina yarda da shi 100%. Ina mutunta shi 100%, koda kuwa bai cancanci samun hakan ba. Ina ba shi amana 100%.


Saurin Yarda Da Jama'a
Hoto: Vmove 

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Ina gasgata furucinsa, koda kuwa ba gaskiya ba ne 100%.


Ina yi masa biyayya, koda kuwa na girme shi 100%.


Ina ba shi lokaci na 100%, koda kuwa bai dace da samun hakan ba.


Ina yin iyakar bakin ƙoƙarina a kan duk abin da muke yi tare da shi don ganin ba a samu matsala ba, sai dai da sannu zai sauya yardar da na yi masa, idan da ma can tun farko ba halinsa ba ne.


A hankali zai fara sa wa na yarda da cewa, shi maƙaryaci ne.


A kwana a tashi zai sa amintar da na yi masa tun farko ta kuɓuce masa, zai sa na dinga kallon sa a matsayin maci amana.


Girman da nake ba shi na yi masa biyayya ba don komai ba sai dai saboda girmama mutane ɗabi'a ce ta masu hankali, amma watarana da kanshi zai sa na daina girmama shi, idan har da ma can tun farko ba halin sa ba ne.


Mutunta shi da nake yi, a kwana a tashi, zai sa na daina mutunta shi yadda ya kamata, idan da ma can bai cancanci samun hakan ba.


Lokacin da nake ba shi, bisa tunanin cewa, yana da muhimmanci, kasancewar shi mutum, da sannu zai sa na daina ba shi lokutana, idan da ma can bai ɗauki lokaci a matsayin abu mafi muhimmanci a cikin rayuwar shi ba.


Da akwai abubuwa masu yawa idan na ce zan yi muku bayanin su.


Da yawan mu mu ne muke sa wa a daina aminta da mu, shi ya sa idan ka ga mutum yana tantama a kanka to kai ne ka sa hakan, haka kuma idan ka ga yana gasgata ka kai ne ka sa hakan, sai dai ba kowa ba ne mutumin kirki haka kuma ba kowa ba ne mutumin banza.


Allah yasa mu da ce, ya kuma zaɓa mana mafi alkhairi a cikin dukkan al'amuran mu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Tuesday, 29 October 2024

Gajeriyar Shawara Ga Dan Kasuwa

Gajeriyar Shawara Ga Dan Kasuwa

 ASSALAMU ALAIKUM!


Shawarar da zan ba ka a yau.


Ka zama mai yawan haƙuri, don watarana sai labari, kuma za ka ga amfanin hakan, sannan ya dace ka dinga kyautata mu'amalarka da kwastomominka, duk abin da za su yi maka ka yi haƙuri, ka jure, don su ka fito. 


Gajeriyar Shawara Ga Ɗan Kasuwa 
Hoto: Scientific world info 

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kowacce nasara ba a cimma ta cikin sauƙi. 


Kasuwanci ba gasa ba ne, amma akwai guraben da za ka iya yin hakan, ta hanyoyin da suka dace, cikin hikima da lura. 


Musamman idan ka fahimci gurbinka, da ire-iren kwastomominka.


Na san cewa, ba ka buƙaci shawarar nan ba, na ba ka ita ne saboda ita ce kawai nake da ita.


FATAN ALKHAIRI! 100%

Monday, 28 October 2024

Tafiya Daidai Da Ra'ayin Kowa

Tafiya Daidai Da Ra'ayin Kowa

Duk irin yanayin yadda ka kai ga kyautata wa mutane, akwai dubban zukatan da sam ba sa yin farin ciki da kai, koda kuwa za ka zama jagora wajen cimma dukkan muradan rayuwarsu, haka kuma a ƙarƙashin zukatansu sam ba sa yi maka fatan alkhairi a iya tsawon rayuwarka.


Tafiya Daidai Da Ra'ayin Kowa
Hoto: Real people group/iStock photo

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Haka ma duk yadda ka kai ga ƙuntata wa mutane, akwai ɗaruruwan zukatan bayin Allah waɗanda suke yin farin ciki da kai, kuma sam ba sa son ɓacin ranka, sannan kuma ba za su gushe ba face sun kasance suna masu yi maka kyakkyawan fata gami da kyautata maka zato, koda kuwa ka fi kowa hatsari a cikin rayuwar al'umma baki-ɗaya.


Shawara ta a gare ka: Kai dai komai za kai, ka yi shi da kyakkyawar manufa da zuciya ɗaya, don neman yardar mahaliccin ka, ba neman yardar wasu ƙatti ba. 


Sannan ka sa wa ranka cewa, ba za ka iya farantawa kowa rai ba, haka kuma ba za ka iya burge kowa ba.


Amma muddin ka ɗauki aniyar tafiya daidai da ra'ayin kowa, ba shakka ka ɗauki aikin da sam ba a iya kammala shi har abada, koda kuwa a tsakanin 'yan uwan ka ne ko kuma iyalanka.


Kai dai kawai, ka yi iyakar abun da za ka iya yi, wanda ba zai takura ka ba. Ka manta da irin yanayin zantuttukan da mutane za su yi a game da hakan. 


Watarana komai zai zama tarihi a cikin rayuwarka gaba-ɗaya!


Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sa dukkan Ibadun mu karɓaɓɓu ne, Ya kuma yi mana katangar ƙarfe da gurɓatattun mutanen cikin mu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

Saturday, 26 October 2024

Tsammani Ga Mutane

Tsammani Ga Mutane

A rayuwa kawai kada ka taɓa tsammanin cewa mutane za su iya yi maka abin da duk kake yin tsammanin samu daga gare su a kodayaushe.


Tsammani Ga Mutane
Hoto: Unsplash

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kai dai kawai ka yi ƙoƙari ka fahimci abin da kake son cimma a iya tsawon rayuwarka. Watarana sai labari!


Idan har ka san cewa kana tafiya a kan daidai, ba buƙatar lallai ne cewa sai kowa ya gamsu da tsarin dukkan irin abin da kake yi.


Abu mafi muhimmanci a rayuwa, ka koyi yanayin yadda za ka yi mu'amala da mutane a dukkan inda ka tsinci kanka a faɗin duniya.


Idan har kana buƙatar ka fahimci yanayin mutum yadda ya kamata, ka mu'amalance shi na tsawon lokaci, za ka iya fahimtar ko wane ne shi? Fiye da duk yadda kake yin zato.


Allah ya kyautata al'amuran rayuwar mu baki-ɗaya, ya sa mutuwa ta zamo hutu ga kowannen mu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Tuesday, 22 October 2024

Su Ma Mutane Ne Kamar Ka

Su Ma Mutane Ne Kamar Ka

Ka tuna wa kanka cewa su ma ɗin irinka ne (Mutane). Idan ka yarda da kanka 100%, za ka iya ƙirƙirar abun da su ɗin ba su samar ba a duniya.


Mutane ne kamar ka
Hoto: Tamil Comedy Memes

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Mai yiwuwa ma na kan ya fi na sun komai.

Tuesday, 15 October 2024

Ka Lura Da Abokan Ka Ko Aminan Ka

Ka Lura Da Abokan Ka Ko Aminan Ka

Tara abokai a wannan zamanin abu ne mai matuƙar sauƙi, kowa zai iya zama abokin ka amma ba lallai ba ne kowa kuma ya zama aminin ka.


Tara abokai
Hoto: Vancomm

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Ka yi nazari kafin ka yanke shawarar zaɓar amini, aminintaka tana da amfani sosai amma kuma tana da matuƙar haɗari a wannan zamanin da muke ciki.


Wanda ka aminta da shi , da shi za'a haɗa hannu wajen cin amanar ka, zai nuna maka shi masoyin ka ne na haƙiƙa, da ma kaɗan yake jira domin cimma manufar shi a kanka, da zaran ya biya buƙatar shi za ka neme shi ka rasa, tamkar ba ku taɓa kasancewa a tare ba, ko haɗuwa ku yi da shi sai ka ga yana kame-kame domin a lokacin ba ka da wani sauran amfani a gare shi.


A mafi yawancin lokuta idan hali ya zo ɗaya to aminantaka ta kan zo cikin sauƙi.


Ka zaɓi amini nagari ba amini na banza ba, ba lallai ba ne kowa ya zama mutumin kirki, haka ma ba lallai ba ne kuma kowa ya zama mutumin banza.


Allah ya zaɓa mana abokai nagari, ya kuma sanya su zama alkhairi a gare mu duniya da lahira Amin.

Wednesday, 22 July 2020

Mafarin Samun Nasara A Rayuwa

Mafarin Samun Nasara A Rayuwa

Karka damu kanka da waɗanda suka fara yi maka dariya a farkon fara yin wani abu a cikin rayuwarka.

Mafarin Nasara


Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Kai dai ka aminta da kanka ɗari bisa ɗari fiye da yadda kake kwatanta hakan a kan wasu.

Idan Allah ya so, su ne za su fara yi maka tafi watarana.

Yi aiki tuƙuru don ka cimma nasara.

Amma idan kuwa ka biye wa al'amarin mutane, daga ƙarshe, ba za ka iya taɓuka komai ba.

Yayinda su kuma za su dawo suna masu yi maka dariyar mugunta, har ma wasu daga cikinsu su rinƙa yi maka kallon wawan mutum wanda sam bai san ciwon kansa ba.

Yanzu haka, ba ka makara ba, don zaɓi yana hannun ka, inma ka yi abun da zai inganta rayuwar ka da ta iyalanka masu zuwa a nan gaba, ko kuma ka ɓata lokutan rayuwar ka a iska, ba tare da ka cimma komai ba. Yayin da su kuma al'umma da iyalanka da 'yan uwan ka, da abokan mu'amalar ka, ba lallai ba ne a iya samun wani daga cikinsu wanda zai iya yin alfahari da kai a ko'ina cikin faɗin duniya, muddin ka shirmantar da lokutan ka a iska. 

Musamman ma idan ya kasance ba ka cimma komai ba a iya tsawon rayuwarka gaba-ɗaya.


Allah Ya tabbatar mana da dukkan buƙatun mu na Alkhairi, Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 3 July 2020

Tsawon Lokaci

Tsawon Lokaci

Duk tsawon lokaci karka fidda rai na samun wata dama a rayuwa.

Samun Dama A Rayuwa


Marubuci:- M. Kabiru Muhammad

Kowa da ka gani yana da tasa Baiwar da Allah yayi masa.

Bar hassada da wanda Allah ya ba.

Kaima kana da abinda Shi bashi da shi.

Yi ƙoƙarin amfanar da al'umma da irin Baiwar da Allah Maɗaukakin Sarki yayi Maka

Allah Yasa Mudace Duniya da kuma Lahira Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: www.muryarhausa24.com.ng

Thursday, 7 May 2020

KYAWUN HALITTA KO KYAWUN DABI'A?

KYAWUN HALITTA KO KYAWUN DABI'A?

Mu ƙaddara inason Ka ne Saboda Kyawun Surar Ka,  watarana za a wayi gari babu wannan Kyawun halittar da nake so a tare da Kai, da sannu watarana idan waɗanda kuka dade baku haɗu da su ba , idan ku haɗu ba lallai bane su shaida ka a karon farko.

Rayuwa Tana Buƙatar Yin Nazari


Marubuci:- M. Kabiru Muhammad

Amma a baya Fa? Komai daɗewar da kuyi bakuga juna ba kuna haɗuwa zasu gane Ka.

Saboda a wancan lokacin halittar Ka bata sauya ba.

Kyawun Sura baya birge Ni Ko kaɗan (Saboda Kyau zai gushe amma banda kyawawan ɗabi'u).

Amma kyawawan halaye suna matuƙar birge Ni musamman idan an gina su a hanya managarciya (Don Allah, badon neman yardar mutane ba).

Koba mutuwa akwai tsufa, mai canza kamannin zahiri zuwa waɗanda idanuwa ko Zuciya bata taɓa hasashen su ba.

Komai zai iya canzawa na ɗan Adam amma banda halaye matuƙar halayensa nagari Ne.

Kuma Ya riƙe su gam, bai bi ruɗin Duniya ba.

Allah Yasa Mudace Duniya da Lahira Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Friday, 1 May 2020

RAYUWAR DUNIYA

RAYUWAR DUNIYA

Kana burin gina al'umma wani yana nan yana burin ganin baka cimma burin Ka ba, idan ma ka cimma burin Ka yana nan yana bin duk wasu hanyoyi don ganin baka Kai labari ba.

Rayuwa Kenan...


Marubuci:- M. Kabiru Muhammad

Daga ƙarshe, ka yi amfani da dukkan irin damar da ka samu a rayuwa, kafin ta kuɓuce maka.

Allah Ya Shiga Tsakanin Nagari da Mugu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.