Saturday 23 September 2017

An kori jami'an Kwastam 'kan shigo da makamai'

Tura Wannan Zuwa

Masana harkokin tsaro sun fara tofa albarkar
baki musammam game da jami'an hukumar
kwastam 28 da ake zargi, da hannu wajen kawar
da kai ga makaman da ake satar shiga da su
Najeriya.

Babban kwanturolan hukumar, Kanal Hamid Ali
ya ce bayan kammala bincike da hukumar tasa
ke da alhakin yi kan lamarin, ta mika makaman
da wadanda ake tuhuma ga hukumar tsaro ta
farin kaya ta kasar, kuma tuni an mika su ga
kotu don a yi musu hukuncin da ya dace.

"Mu kuma namu jami'an da muka kama su da
hannu a ciki tuni muka kore su daga aiki."

A baya-bayan nan dai hukumar kwastam ta
Nigeria ta kama bindigogi 470 a tashar jiragen
ruwan Tincan Island a Lagos, wadanda aka shigo
da su daga kasar Turkiyya, makonni kadan da
shigo da kama wasu fiye da 1,000 da suma aka
shigo dasu daga Turkiyyan.

Gwamnatin kasar ta ce dole ta hau teburin
tattaunawa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke
kasar.

Malam Kabir Adamu, wani mai sharhi ne kan
harkokin tsaro, ya kuma shaida wa BBC cewa
duk da yake babu cikakkiyar shaida mai alakanta
irin wannan sakaci na jami'an kwastam, da
shigar irin wadannan makamai hannun kungiyoyi
irinsu Boko Haram, da masu satar mutane da
kuma sauran masu gwagwarmaya da makamai,
ana iya cewa al'amarin ba karamar barazana ba
ce ga Najeriya.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: