Sunday 1 October 2017

Ba mu da komai Wannan ta sa aka mayar da mu tamkar al'ummar da aka ci ta da yaki-Kungiyar Igbo

Tura Wannan Zuwa

Kungiyar Ohaneze Ndigbo a Najeriya ta zargi
Shugaba Muhammadu Buhari da abin da ta kira
"bata lamari" ta hanyar watsar da al'ummar Igbo
a gwamnatinsa.

Yayin hira da BBC lokacin wata ziyara, shugaban
kungiyar, Cif John Nwodo ya ce batun mayar da
'yan kabilar Igbo saniyar ware, ba boyayyen abu
ba ne.

Hakan na faruwa ne, tun bayan jawabin da ya ce
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi
cewa zai bambanta tsakanin 'yan kasar bisa
la'akari da kuri'un zaben da suka ba shi.

A cewarsa: "Buhari ya fada wa duniya cewa zai
bambanta kulawar da zai yi wa mutanen da suka
kada masa kashi 97 cikin 100 na kuri'unsu da
wadanda suka kada masa kashi biyar na
kuri'unsu."

Jagoran Igbon ya ce ba a ba wa 'yan kabilarsa
gwargwadon hakkokin da suka cancanci samu.

John Nwodo ya buga misali da gwamnatin
jamhuriyar ta biyu. Inda ya ce kuri'ar da Shagari
ya samu a yankin Kudu Maso Gabas ba ta kai
wadda ya samu a yankin Middle belt ba, kuma ba
ta sa shi nuna wa Igbo bambanci ba.

"Ka ga! Ni tsohon dan jam'iyyar NPN ne, na rike
mukamin minista a gwamnatin Shagari, in ji shi."
Ya ce bai kamata Buhari ya yi fatali da 'yan
kabilar Igbo, don kawai ba su kada masa kuri'a
ba.

A cewarsa, shugaban kasa baban kowa ne, don
haka bai dace ya kori 'ya'yansa don kawai sun
bijire masa ba..

Ka duba hukumomin tsaro a Najeriya, babu ko da
daya da dan kabilar Igbo ke jagoranta..

"Mu, ba ga babban hafsan tsaro ba, mu ba ga
babban hafsan sojin kasa ko na ruwa ko sojin
sama ba. Ba a ba mu shugabancin hukumar kula
da shige da fice ba, ko ta leken asiri ko ta tsaron
farin kaya ko ta kiyaye hadurra ba."

"Ba mu da komai. Wannan ta sa aka mayar da
mu tamkar al'ummar da aka ci ta da yaki," a
cewarsa.
Ya yi ikirarin cewa an girke musu shingayen 'yan
sanda a duk manyan hanyoyin yankin Kudu Maso
Gabas babu gaira babu dalili.

John Nwodo ya ce kusan illahirin kwamishinonin
'yan sandan jihohin yankin Igbo, sun fito ne daga
arewacin Najeriya.

"Babban kwamandan da ke kula da runduna ta
82 da ke Enugu, dan arewa ne. Shin sun san
yankin ne?" Nwodo ya tambaya.
Cif John Nwodo ya ce yana alla-alla ya samu
ganawa da Buhari don zayyana masa wadannan
batutuwa da ke ci wa kabilar Igbo tuwo a
kwarya.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: