Sunday 1 October 2017

Kasar Nigeria na da matukar Muhimmanci a gare NI- Bill Gates

Tura Wannan Zuwa

Attajirin  da ya fi kowa arziki a duniya, Bill
Gates, ya ce Najeriya tana daya daga cikin
kasashen da yake sanya ido kansu sosai.

Bill Gates wanda ya bayyana haka a wata hira da
BBC, ya ce kasar tana da muhimmanci ne a
wurinsa saboda ita ce ta fi kowace kasa yawan
al'umma a nahiyar Afirka.

"Wannan ne ya sa gidauniyata ta Bill & Melinda
Gates Foundation take ci gaba da aikace-
aikacenta a can," kamar yadda ya ce.
Har ila yau, ya ce akwai babban kalubale a fannin
kiwon lafiya a yankin arewacin kasar.

"Akwai matsalar cutar maleriya da kuma batun
'yan gudun hijira. Muna aiki da wadansu daga
cikin gwamnatocin jihohi kamar na Kano da
Borno a kokarinmu na ganin mun magance
kalubalen kiwon lafiya a yankin," in ji shi.

Ya ce ayyukan gidauniyarsa suna taimakawa
wajen rage mutuwar mata masu juna biyu da
kuma kananan yara a fadin kasar.

Sai dai ya ce suna aiki ne tare da gwamnatin
kasar da kungiyoyi masu zaman kansa da kuma
attajirin nan da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka,
Alhaji Aliko Dangote - wanda dan kasar ne.
Kamar sauran kasashen Afirka, Najeriya na daya
daga cikin kasashen da aka fi yawan samun
mace-macen mata wajen haihuwa da kuma na
kananan yara.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: