Sunday 24 September 2017

Igbo Mazauna Adamawa Na Goyon Bayan Najeriya a Matsayin Kasa Daya

Tura Wannan Zuwa

Shugabannin al'ummar Igbo dake zaune a jihar
Adamawa sun kira taron manema labarai a Yola
fadar gwamnati inda suka sake jaddada goyon
bayansu ga Najeriya a matsayin kasa daya

A l’ummar Igbo mazauna jihar Adamawa sun ce
ba zasu koma yankunan su ba kuma ba za a raba
kasar Najeriya ba duk da tada jijiyar wuya da
matasan kudanci da arewacin kasa ke yi kan
makomar ta kasa daya.

Wannan ita ce matsayar da al’ummar Igbo suka
dauka inji ta bakin shuigaban al’ummar Igbo na
jihar Adamawa Igwe Chief Godwin Omenaka da
yake wa manema labarai bayani a cibiyar ‘yan
jarida ta Najeriya reshen jihar Adamawa.

Igwe Godwin Omenaka ya ce don ya tabbatarwa
jama’arsa gamsuwarsa da matakan da
gwamnatin jihar Adamawa ta dauka na tsaron
lafiya da dukiyoyinsu shi ya sa ya maido da
matarsa Yola wadda ta je kasar su domin yi wa
‘yarsu wankana ego saboda ya takawa masu
neman maida iyalansu gida birki.

Wani dattijo dan sama da shekaru saba’in da
biyar Chief Francis Ogogo da ya share sama da
shekara arba’in a Yola fadar jihar Adamawa ya
ce ba bu inda zasu je kuma ba shi yiwuwa a raba
kasar Najeriya don haka ya ke kira ga al’ummar
Igbo su kauda fargaba.

A Jihar Taraba makwabciyar jihar Adamawa
shugaban kabilar Igbo Chief Joseph Uchedu
kuma mai baiwa gwamna shawara na
musamman ya ce sun gamsu da matakan da
gwamnatin jiha ta dauka na tabbatar da tsaron
lafiya da dukiyoyinsu shi ya sa ba su fargabar
komawa yankunansu. Sai dai ya tunatar da
gwamna bukatar ta kauda bambancin asali da
wariya na bangare da dan Najeriya ya fito
tsakanin jama’a.

Wata malamar makaranta Madam Peace Okeke
‘yar kabilar Igbo ta shaidawa Muryar Amurka
jihar Taraba gida ce a gareta, kuma yara da take
karantarwa sun dauke ta a matsayin uwa ita
kuma tamkar ‘ya’ya a gareta don haka inji ta
bata ga abinda zai mai da ita yankinsu ba.

A bangaren kungiyar Miyyetti Allah ta kasa
reshen jihar Taraba inji ta bakin shugabanta
Alhaji Jauro Sahabi suna yi wa matasansu
gargadi na kada su yarda a yi anfani da su wajen
tada fitina. Kan batun janye kafa da aka ce sun yi
na kai shanu kudancin Najeriya, y ace sun yi
haka don su yi nazarin yadda lamura ke tafiya a
yankin.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: