Saturday 23 September 2017

Ma'aikatan Lafiya a Najeriya sun tafi yajin aikin sai baba ta gani

Tura Wannan Zuwa

Kungiyar Ma'aikatan Lafiya a Najeriya ta
bayyana tafiya yajin aikin sai baba ta gani
sakamakon yadda gwamnatin kasar ta gaza
cika alkawura da yarjeniyoyin da suka yi da
ita a baya.

Yajin aikin ya fara aiki daga ranar Alhamis
din nan, kuma an fara shi ne bayan karewar
wa'adin makwanni 2 da kungiyar ta bayar
na gargadi ga gwamnati.

Hadaddiyar
Kungiyar Ma'aikatan lafiya ta Najeriyan ta
bayar da gargadin a ranar 30 ga watan
Agustan da ya gabata.

Shugaban kungiyar Biobelemoye Josiah ya
ce, a tsawon makwanni 3 da suka bayar na
gargadin gwamnatin kasar ba ta saurare su,
ba ta kuma biya bukatun nasu ba.
jawabin da Josia ya yi ga manema labarai a
Ilorin babban birnin jihar Kwara ya bayyana
cewa, wannan halin rashin ko in kula da
gwamnati ke nuna wa ya kai matuka, kuma
sakamakon haka ya sanya suka yi kira ga
dukkan mambobinsu na Najeriya da su
tsunduma yajin aiki.

Ya ce, suna sake kira ga gwamnati da ta
girmama yarjeniyoyin da suka kulla tare da
aiwatar da su musamman ma umarnin kotu
da aka bayar. Haka zalika suna kira ga
dukkan mambobinsu da su aiki da umarnin
yajin aikin.

Ma'aikatan lafiyar dai na neman gwamnati
da ta kyautata yanayin aikinsu da
albashinsu.
An fara yajin aikin mako daya bayan da
kungiyar likitoci ta janye nata yajin aikin.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Trt Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: