Monday 25 September 2017

Sojojin Saman Najeriya Sun Yi Kwanaki Goma Suna Lugudan Wuta kan 'Yan Boko Haram

Tura Wannan Zuwa Ga

A cikin kwanaki goma da mayakan saman
Najeriya suka yi suna lugudan wuta kan sansanin
'yan Boko Haram a dajin Sambisa kwamandoji
'yan ta'addan da dama suka halaka.

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya
Air Marshall Abubakar Sadique ya ce dakarunsa
sun hango yadda wasu daga cikin jagororin
mayakan kungiyar Boko Haram ke kokarin sake
tattaruwa a cikin dajin Sambisa.
Ba tare da bata lokaci ba, inji hafsan hafsoshin,
dakarunsa suka afka masu inda suka kashe da
dama cikinsu.Yana mai cewa sunan wannan
farmakin shi ne lugudan ruwan wuta saboda sun
fahimci cewa akwai wani kokari da 'yan ta'addan
ke yi su sake kafa wani sansani cikin dajin
Sambisa.

Makasudin farmakin shi ne dakile duk wani
matakin da 'yan ta'addan suka dauka bai tabbata
ba. Dalili ke nan da sojojin saman suka kwashe
kwanaki goma suna lugudan wuta kan 'yan
ta'addan. Ta bakin Air Marshall Sadique sun
samu biyan bukata da gaske. Lokacin da suka
kare kai lugudan wutar babu alamar 'yan
ta'addan a wurin.

Duk da nasarorin da suka samu har yanzu suna
cigaba da shawagi a sararin samaniya, inji Air
Marshall Sadique.
Muhammad Inusa Barnawa masanin harkokin
yakin sama a Najeriya yana mai cewa koda an
tura sojojin kasa idan babu na sama babu abun
da zasu iya yi. Dole ne sojojin sama su fara hari
daga sama kafin na kasa su shiga. Muddin aka
karya lagwonsu daga sama a kasa kuma ba zasu
sami wani karfi ba.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: