Wednesday 4 October 2017

Labarin Siyasa 'Da ni INEC ne da sai na rushe jam'iyyar APC'

Tura Wannan Zuwa

Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki ta
Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya bayyana
damuwa kan yadda jam'iyyar ta gaza gudanar da
taron kwamitinta na amintattu kimanin shekara
uku bayan kafuwarta.

"APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba, tsarin
mulkinta ya tanadi cewa sai kwamitin amintattu
da kwamitin gudanarwa na kasa da kwamitin
wakilan tsara manufofin jam'iyyar na kasa sun yi
taro duk bayan wata uku.

Shin tun da aka kafa jam'iyyar nan, an yi taron
kwamitin amintattu?"
Bugu da kari a cewarsa tun da aka kafa APC,
jam'iyyar ba ta taba waiwayar kusoshin da suka
kafa ta don jin ra'ayinsu game da nasarori ko
akasin haka da ta samu ya zuwa yanzu ba.
Ya ce yana cikin mutum tara da suka sanya
hannu don kafa ta, bisa wasu hujjoji da wasu
sharudda, wadanda ya zuwa yau babu ko daya
daga cikinsu da ta iya cimmawa.

Buba Galadima ya ce ba zai yiwu 'yan Najeriya
su ci gaba da jiran jam'iyyar tsawon lokacin da
ba su san karewarsa ba kafin ta farga ta zo ta
jibanci lamarinsu.

Duk da rashin gamsuwa kan yadda jam'iyyar ke
tafiya a yanzu, Buba Galadima ya bayyana
kyakkyawan fatan cewa APC ko babu Shugaba
Muhammadu Buhari za ta ci gaba da kasancewa.

"Ba na so ka dangantaka wannan jam'iyya da
mutum daya, don kuwa jam'iyya ce tamu ta
dukkan al'ummar Najeriya."
Ya ce sha'anin siyasa wani batu ne na wannan
ya zo, wannan ya tafi, kuma duk wainar da aka
tona, ba shakka akwai masu ci.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: