Friday 1 December 2017

Gwamnatin Niger Za Ta Fitar Da Sabon Tsarin Gina Masallatai Da Yin Wa'azi-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

Ganin yadda ake fakewa da addini ana harzuka
jama'a har a kai ga tashin hankali ya sa
gwamnatin Niger ta gana da malaman addinin
Musulinci ta shaida masu sabon shirinta na gina
masallatai da yin wa'azi a duk fadin kasar.

Kokarin gujewa rikici ya sa gwamnatin Niger, ta
shirya taro da ilahirin shugabannin addinin Islama
domin nazarin hanyoyin rigakafi, inji ministan
cikin gida Bazoum Muhammaed.

Ministan ya ce yanzu kasar ba ta da wani tsari
akan yadda za'a bude masallaci da kuma yadda
za'a yi wa'azi, kowa ya ga dama sai ya bude
masallaci kuma ya yi wa'azi yadda ya ke so a
cewar Bazoum Muhammad. Haka ma mutane su
kan tashi su je fili su kama yin wa'azi ba tare da
tambayar kowace hukuma ba.

Har ma gidajen
rediyo da talibijin suke shiga su yi wa'azi ba tare
da wani izini ba, inji ministan.
Irin masu yin wa'azi yadda suka ga dama su kan
yi alfani da kalamun da basu dace ba su harzuka
mutane.

Shugaban wata kungiyar Islama Shaikh Nuhu
Abdulrahaman, ya yaba da yunkurin wanda ya
kira "babbar shawara ce suka kawo ga kasarmu".
Ya ce shawarar za ta tabbatar da kwanciyar
hankali a cikin kasar.

Shi ma Uztaz Muhammad Ashiru Muhammad
Tukur, na wata kungiya kuma reshen Maradi ya
gargadi gwamnati ta dauki matakan da zasu ba
da damar cin moriyar shirin. Ya yi kira ga
gwamnati kada ta bari harkokin addinin su lalace.
Kungiyarsa ta yi murna gwamnati za ta sa tsari
akan gina masallatai da yin wa'azi.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com  hanya me sauki ko kuma daga kasan Website din akwai inda akasa

Name...
Email...
Message...

Sai Ku turo mana mun gode

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Voa-Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: