Saturday 11 November 2017

Labari: Wanda ya fallasa dalolin da EFCC ta gano a Lagos ya 'zama miloniya'

Tura Wannan Zuwa

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin
arzikin Najeriya ta'annati ta ce mutumin da ya
fallasa kudin da aka gano a wani gida a unguwar
Ikoyi da ke jihar Legas "ya zama miloniya."

Shugaban riko na hukumar, Ibrahim Magu, ne ya
tabbatar da haka a wani taro a birnin Vienna na
kasar Australiya, in ji sanarwar da mai magana
da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya fitar.

Uwujaren ya tabbatar wa BBC cewa hukumar ta
bai wa wanda ya fallasa boye wadansu makudan
kudade a wannan gida, amman ya ki ya bayyana
nawa aka bai wa mutumin.

A shekarar da ta wuce ministar kudin Najeriya,
Kemi Adeosun, ta bayyana shirin gwamnatin
kasar na bayar da tukuicin kashi biyar cikin 100
ga duk wanda ya fallasa "haramtaccen kudin" da
ake zargin na sata ne.

Idan aka yi la'akari da cewa kudin da aka samu a
gidan na Legas a farkon shekarar nan ya kai
naira biliyan 13, za a iya cewa wanda ya
kwaramata bayanin kudaden zai samu kimanin
naira miliyan 650 (kashi 5 cikin 100 na kudin da
aka samu a cikin wani bene a Legas).

Bayan hukumar EFCC ta yi wawan kamun ne dai
aka gano cewa kudaden suna da alaka da tsohon
shugaban hukumar leken asirin Najeriya ta NIA,
Ayo Oke.

Wannan ya sa shugaban Najeriya, Muhammadu
Buhari, ya sa aka dakatar da Mista Oke daga
farko, kuma ya kore shi daga baya.

Source©Bbc

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: