Friday 17 November 2017

Labarin Wasanni: Man United ta samu fam miliyan 141

Tura Wannan Zuwa Ga

Manchester United ta sanar da samun kudin
shiga da ya kai fam miliyan 141 a wata ukun
farko, amma albashin da take biyan 'yan wasa
ya karu sakamakon buga gasar Zakarun Turai da
take yi.

A watan Janairu ne United ta zama ta daya a
duniya wajen arziki a tsakanin kungiyoyin
tamaula a karon farko a kididdigar da Deloitee ta
fitar, rabon da ta taka wannan matsayin tun
2005.

A rahoton kudin da United ta sanar ta samu a
ranar Alhamis a farkon wata uku zuwa karshen
watan Satumbar 2017, ta samu karin fam miliyan
120.2 daidai da yadda ta samu a bara.

United ta kashe kusan fam miliyan 145 a farkon
kakar bana wajen sayo sabbin 'yan wasa da suka
hada da Romelu Lukaku daga Everton da
Nemanja Matic daga Chelsea da kuma Victor
Lindelof daga Benfica.

Haka kuma bashin da ake bin kungiyar ya kai fam
miliyan 268 zuwa karshen Satumbar 2017, sai dai
kuma ya ragu kenan zuwa fam miliyan 69.6.

United ta ci wasa hudu da ta yi a gasar cin kofin
Zakarun Turai sannan ta kai daf da na kusa da
karshe a kofin Carabao, sannan tana ta biyu a
gasar cin kofin Premier.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: