Friday 1 December 2017

NAJERIYA: Wani Ya Farma 'Yan Makarantar Firamare Da Sara

Tura Wannan Zuwa Ga

Da safiyar yau wani ya shiga makarantar
firamare a Jabi kusa da Maiduguri ya dinga sara
kan mai uwa da wabi kan daliban.

Wani da ba'a tantance ba ya shiga makarantar
firamaren Jabi kusa da Maiduguri, cikin jihar
Borno, inda ya fara saran daibai da adda.

Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar dalibai biyu nan
take da kuma rufe makarantar garin yadda
daliban suka fice a kidime yayinda wasu daga
ciki suka samu raunuka daga saran addar.

Sai dai rahotanni sun ce tuni ma'aikatan
makarantar suka yi kukan kura suka damke
mutumin wanda yake rike da addar, an bayya
cewa ya sari daya daga cikin malaman
makarantar.

Wani ganau da ya zanta da wakilin Muryar
Amurka, Haruna Dauda, ya ce mutumin ya fito ne
daga gefen garin ta kofar baya rike da adda.

Kafin a ankara ya shiga aji. Malamar dake
koyaswa da ta daga hannunta sai ya sareta.

Ba'a iya tantance ko yara nawa suka ji rauni ba
sanadiyar saran saboda yawancinsu sun arce
daga makarantar da rauni.

Mutumin da ya kai harin ba mazaunin wurin ba
ne sai dai tunda yana hannun jami'an tsaro za'a
san inda ya fito da kuma manufarsa.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com  hanya me sauki ko kuma daga kasan Website din akwai inda akasa

Name...
Email...
Message...

Sai Ku turo mana mun gode

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Voa-Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: