Wednesday 20 December 2017

Karanta Kaji: Matsalolin Matar Bahaushe Da Dalilan Da Ya Sa Sauran Kabilu Suka Fi Ta Iya Zaman Aure

Tura Wannan Zuwa

Wannan fili zai bada dama ga masu bibiyarmu da
su aiko da sakon rubutu akan wata matsala da
ke addabar al’ummar Malam Bahaushe da nufin
kawo gyara, fadakarwa, tunatarwa da ilimantarwa
duk wai don mu taru mu gyara.

Wannan gudunmawa ce daga Alhaji Abdulyassar.

Muna fata za a karanta sakon nasa da idon
basira. kuma muna fata a samu wata mace ma
ta bayyana matsalolin maza a zamantakewar
aure da kuma dalilan da ya basa martaba mace
da ma auren kansa.

Daga nan kuma sai mu yi
nazari gaba daya akan yadda za a kawo karshen
matsalolin daga bangaren maza da mata
oqwoei.ru

A sha karatu lafiya:

Dalilai da yawa sun nuna mana cewa matan
sauran kabilu sun fi na Malam Bahaushe dadin
zama, hakan ta sa a yau, za mu tattauna akan
wasu dalilai da ke sa matar Bahaushe rashin
more dadin zaman aure kamar haka:

*1.Raini: Akwai tsabar raini ga matar malam
bahaushe,zaku zauna da mace shekara da
shekaru amma rana daya matsala ta samu za ka
ji maganganu na raini ka ji suna cewa mazajensu
kaddara ce ta sa suka aure su.

Sai ka ji suna
cewa ‘Idan ba kaddara ba, ba abunda zaisa na
aureka, Ai namiji ba dan goyo da zani ne ba,d
aman duk wacce ta dauki namiji uba za ta mutu
marainiya da dai sauran kalamai irin wadannan
In muka yi wa wadannan kalamai fassara na
tsanaki, za mu fahimci abinda matar Bahaushe
ke nufi da su.

Za mu gane manufarta ita ce kada
mace ta sake ta baiwa mijinta yadda dari bisa
dari, kada ta bashi soyayyarta duka. wanda kuma
daga nan ne matsalar auratayya ke farawa
Hakan tasa mazan hausawa da yawansu, suna
zaune da matan sune bisa lalura kawai, saboda
abin haushi da kularwa da matan ke nuna musu
wai da sunan kar su nunawa mazan soyayya da
yarda wai don hakan zai iya cutar da su.

KUMA
ABIN MAMAKI DA YAWAN MATAN HAUSAWA
SUNA DA WANNAN RA’AYIN, sabanin sauran
kabilu za ka samesu basa raina mazajensu

*2.Rashin yi wa miji hidima: A nan ma za ka ga
sauran matan kabilu suna yi wa mazajensu wanki
da guga da wanke takalmi da lura da kwalliyar
maigida da gyara masa ado, wasu har gona suke
zuwa, daukar nauyin karatun ‘ya’ya da sauransu..

amma matan bahaushe babu ruwansu, sai dai su
ci su kwanta, babu ruwansu da mijinsu, balantana
su yi masa wata hidima.

Hidimar kawai da za ta yi masa shi ne, ta dafa
masa abinci, ko ta kai masa ruwan wanka.

BA
WAI AN CE A ADDINANCE WAJIBI NE SAI TA YI
HIDIMA KAMAR BAIWA BA, A’A, AMMA TA FUSKAR
MALLAKE MIJI DA NUNA MASA KAUNA SAI KIN YI
MASA HIDIMA DAI DAI DA ARZIKINSA ,MISALI
GYARA MASA KWALLIYA, GOGE MASA TAKALMI DA
JAKA, DAURA MASA BELIT KO MADAURI WUYA,
GYARA MASA FUSKA DA KILIFA, GYARA MASA
HULA, RIKE MASA JAKA, IN ZAKI IYA YI MASA
WANKI MA TO BA LAIFI, AMMA BA TILAS.

Wadansu matan kabilun ma har yi wa mazansu
sutura suke yi tare da yi musu kyaututtukan
bazata.

Duk wannan yana kara soyayya da
shakuwa tsakanin ma’aurata
A nan ba ina nufin namiji ya kwanta kawai
matarsa ta rika yi masa hidima da baut aba
kamar yadda ake yi a wasu guraren kaga an
maida mata tamkar bayi suyi casa suyi surfe suyi
niqa,da shauran aikin wahala hakan bai dace ba
dan bautar da mata laifi ne a addininmu ..

AMMA
KODA MIJINKI MAI KUDI NE, TO YANA BUKATAR
HIDIMA KODA DA KYAUTATAWACE

3*Rashin godiya: Matar bahaushe tana da wata
al’ada ta rashin godewa kokarin da mazajensu
suke yi musu. Ba su nuna godiyar a aikace ko
kuma su furta da baka. Akwai matan da suke
cewa mazajensu mai suka taba yi musu tun da
na zo hanunka WANNAN KALMA CE MAI MUNI.

Daruruwan shekarun da suka gabata ANNABI
S.A.W ya suffanta mata masu irin wannan dabi’a,
amma abin mamakin shi ne yadda kasan da
matan Hausawa Annabi S.A.W ya ke don bincike
ya nuna sun fi sauran mata fadarta.

Akwai nau’o’i na nunawa miji godiya, kuma
WALLAHI DUK SADDA KI KA NUNAWA MIJI GODIYA
SAI YAJI YA KARA SONKI. KIN GA ASHE RIBARKI
CE MA..

Amma abin haushi ‘yan kalmomi kadan da za ta
furtawa mijinta hade da murmushi da
kyakkyawan kallo shikenan fa, kin farantawa
mijinki rai kin kara samun matsayi a zuciyarsa,
ga kuma hidimar da ya yi miki ga addu’ar da
mala’iku za su yi miki
Sau tari, in Kaga matar Malam bahaushe tana yi
wa mijinta godiya da fara’a to ta cuce shi ne ko
kuma tana shirin cutarsa

*4 boye soyayya ga miji: ita ma wata dabi’a ce ta
matan hausawa ,rashin nunawa miji soyayya sai
dai baya-baya, dan wasu matan sun dauka
nunawa miji soyayya nasa miji ya rainaki.

Wannan ma sai ya sa kaga ba a yi masa komai.

SU MATAN HAUSAWA ABINDA SUKA DAUKA NUNA
SOYAYYA GA MIJI ITA CE KAWAI KWANCIYAR
AURE, bayan haka ba wata soyayya da suke
nunawa mazajensu, sau tari za ka ji matan wasu
kabilun suna cewa “Wallahi da za su hada kishi
da bahaushiya sai sun kwace mijin, ba malamai
ba boka kawai tsantsar nunawa miji kulawa da
soyayya da hidima.

*5 Watsar da kwalliya bayan aure da rashin iya
tsara kwalliya:
Matar malam bahaushe da zarar ta yi aure bayan
ta gama cinye amarcinta hakanan za kaga
tawatsar da dabi’arta ta kwalliya ta koma daura
zani iya kirji, kwaskwarima, bare tafara tara
‘ya’ya, Subhanallah! Hakanan suke har wajen
tsarin sanya sutura, ba sa tsayawa su fahimci
wace iriyar sutura ke burge mazajensu don rike
irin wannan sutura a matsayin suturar da za su
sanya a kebantaccen lokacinsu tare da
mazajensu.

Wata sai kaga tana ta daura atamfa
alhali siket da ‘yar riga ke burge mijinta

*6:RASHIN IYA KISHI:
matar bahaushe ba ta iya kishi ba, KISHI ANA YIN
SA NE DON A MALLAKE MIJI TA HANYAR
KYAUTATA MASA, AMMA ITA MATAR BAHAUSHE
SAI DAI A BATAWA MIJI RAI.

Afuwa gareku matan Hausawa wannan bayani
badan ya yi muku zafi na yi shi ba, a’a, illa
kawai, don na tunatar da ku irin halayen mafiya
yawanku matanmu na Hausawa. An yi muku nisa
a fagen zamantakewa kamar yadda ku ka sani,
yau duniya ta ci gaba sosai a kowanne bangare,
wannan kuwa ya hada har da bangaren
zamantakewa.

A saboda haka ne ma na ke yin
kira a gareku da ku canja

Naku: Alhaji Abdulyasar

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin aiki Tukuru don jin dadin ku

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Mujallarmu

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: