Monday 12 February 2018

Karanta Ka Amfana: Babban Amfanin Zogale Ga Jikin Dan-Adam Guda 18

Tura Wannan Zuwa
1. Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha
kamar shayi domin maganin Olsa (Ulcer).

Amfanin Zogale

2. Ana shafa danyen ganyen zogala akan
goshi domin maganin ciwon kai.

3. Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani
karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen
ganyen zogale insha Allah jinin zai tsaya.

4. Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin
zogala da man zaitun ya shafa.

5. Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko
gembo domin saurin warkewa.

6. Sanya garin zogale a cikin abinci yana
maganin hawan jinni da kuma karama
mutum kuzari.

7. Ana dafa ganyen zogale tare da saka
kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon
shawara.

8. Ga mai fama da ciwon ido zai diga rowan
danyen zogala, haka ma mai fama da ciwon
kunne.

9. Macen da ke shayarwa ta dafa furen
zogale da zuma dan karin nono.

10. Wanda ke fama da yawan fitsari wato
cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale
da citta kamar shayi.

11. Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka shakamar shayi yana maganin sanyi.

12. Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsarciki ga yara.

13. Ana daka ganye zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon
hanta.

14. Ga mai fama da sanyin kashi ko wani
kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su
sannan a hada da man kwakwa (Mai-ja) sai
a shafa.

15. A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da
kuma kimba domin karin karfin da namiji
das aka masa kuzari, haka kuma yana
karawa mata nishadi.

16. A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki
(Apendis).

17. Haka kuma idan mutum yana fama da
ciwon Aids zogale kan iya rage masa
radadin shit a hanyar shan rowan dafaffen
zogale.

18. Haka kuma mai fama da Typhoid da
Malaria da kuma ciwon Basir ko Shawara,
zai iya yawaita shan ruwan dafaffen
zogalen domin samun sauki.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: Hausa Leadership
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user