Tuesday 3 April 2018

GT BANK SUNA NEMAN MA'AIKATA RUWA A JALLO

Tura Wannan Zuwa Ga
Na ci karo da wannan tallar ne na ga ya kamata in yi sharing da yan uwa watakila wani yana da sha'awar aikin banki, sai dai kuma ka'idar gurbin da zasu cike na masu matakin karatun degree ne don haka idan kasan ba degree gare ka ba please kar ka bata
lokacin ka.

Na ga advert din ne kamar haka:

Yana daga kudurorin bankin guaranty trust (GTBANK) taimakon matasa akai-akai ta hanyar samar masu da damar samun ayyukan yi don su zama masu dogaro da kai su kuma zama masu amfani ga rayuwar al'ummar da suke rayuwa a cikin ta..

YADDA AKE APPLYING

Ka'idojin shiga ko kuma applying ana son mai neman aikin ya cika sharudda kamar haka:

1- Ya kammala makarantar sakandire da sakamakon WAEC ko NECO da karancin credits biyar ciki kuwa har da Mathematics da English kar kuma ya wuce zama biyu.

2- Dole ya zama ya kammala karatun degree da sakamako mafi karanci second class lower division daga kowace accredited University.

3- Dole ya zama ya kammala bautar kasa (NYSC) tare da shaidar kammalawa. (NYSC Certificate)

4- Dole ya zama dan shekara 26 ko kasa da haka
ka wadannan sharuddan da na lissafa a sama za'a gayyace shi don cigaba da application journey dinsa, wanda yake da matakai biyar.

Matakan sune kamar haka:

MATAKI NA FARKO

Kwarya-kwaryar jarabawa ta hanyar amfani da computer (Computer-Based Assessment) jarabawa ce da ta kunshi tarihi, current affairs, dabarun aiki, ilimin zamantakewa da sauran su.

MATAKI NA BIYU

Za'a gayyaci wadanda suka samu nasarar lashe jarabawar don tankade da raurayar takardun shaidar kammala makaranta da sauran su. Anan ana shawartar mai neman aikin ya tabbatar yazo da duk wata takarda ko sakamako da ya rubuta a cikin curriculum vitae din sa.

MATAKI NA UKU

Wadanda suka yi nasara a mataki na biyu su kadai ne zasu wuce mataki na uku a inda za'a yi karamar interview wadda zasu maka tambayoyi akan field of specialization naka da dai dan abinda ba'a rasa ba.

MATAKI NA HUDU

Wadanda suka yi nasara a mataki na uku su kadai zasu samu gayyata zuwa mataki na hudu wanda anan ne zaka yi interview babba wadda kowane bangare wanda zai iya amfanar su a yayin aikin ka za'a iya tambayar ka.

MATAKI NA BIYAR

Duk wanda yayi nasara a mataki na hudu to tamkar ya samu aikin ne saboda a mataki na biyar Entry Level Training Scheme ne za'a yi maku training na tsawon wata hudu akan yadda ake so ka rika gudanar da aikin ka tsakanin ka abokan kasuwanci ko abokan aiki ko shugabannin ka da ma wadanda ke karkashinka. tare da dokoki da hukuncin karya su.

Har zuwa lokacin kammala wannan rubutu basu yi specifying ranar kullewa ba, ga wanda yake sha'awa jaraba neman sa'a sai ya shiga nan kai tsaye.


Allah ya ba mai rabo sa'a.

Mai tambaya yayi ta email , mai sharing ko copying ma yayi amma
lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin
mu ne.

Source by ©Sirrin Wayar Android
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user